Burina in bude kamfanin sassakar turmi na zamani -Sama’ila Maiturmi

Duk wanda aka ce masa akwai masu sana’ar sassakar turmi a tsakiyar birnin Makka da ke kasar Saudiyya zai yi mamaki. Aminiya ta gano wani wuri a da ake kira ’Yan Turmi a unguwar Yabalash da ke yankin Shara-Mansur a birnin Makka, inda Hausawan Najeriya da Nijar suke sassakar turmi iri-iri. Alhaji Sama’ila Isa Gombe, […]

Burina in bude kamfanin sassakar turmi na zamani -Sama’ila Maiturmi
Burina in bude kamfanin sassakar turmi na zamani -Sama’ila Maiturmi

Duk wanda aka ce masa akwai masu sana’ar sassakar turmi a tsakiyar birnin Makka da ke kasar Saudiyya zai yi mamaki. Aminiya ta gano wani wuri a da ake kira ’Yan Turmi a unguwar Yabalash da ke yankin Shara-Mansur a birnin Makka, inda Hausawan Najeriya da Nijar suke sassakar turmi iri-iri. Alhaji Sama’ila Isa Gombe, dan Najeriya ne da ya yi shekaru masu yawa yana sassaka turmi a wurin. Ya bayyana dalilin da ya sa yake sassaka turmi a Saudiyya da nasarori da kuma matsalolin da yake fuskanta. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Za mu fara da gabatar da kanka?

Sunana Alhaji Sama’ila Isa Gombe. Ni dan asalin Jihar Gombe ne, amma ta Maiduguri na taho Saudiyya. Shekarata 44 a duniya. Matana uku da ’ya’ya da yawa. Na shekara 15 ina sana’ar sassaka turmi, wato tun daga Najeriya har zuwa nan Saudiyya. Sana’ar sassaka turmi gadon gidanmu ne, saboda mahaifina ita yake yi, kuma daga wurinsa na koya, sannan da na zo Saudiyya sai na ga masu sana’ar, sai kawai na shiga cikinsu na ci gaba da yi ba tare da wani ya koya mini ba.
Me kake sassakawa bayan turmi?
Ina sassaka turmi da akushi da kota da muciya da kujera da abin kama zuma da tabarya da kota da duk wani abin gargajiya da ake yi da itace. Babu abin da ba na iya sassakawa na gargajiya da hannuna. Kuma Larabawa da mutanenmu na Afirka suna sayan kayanmu.
Nawa kake sayar da kayan da ka sassaka?
Ina sayar da babban turmi fam takwas zuwa fam goma, dubu hudu zuwa dubu biyar ke nan a kudinmu na Najeriya. karamin turmi fam shida zuwa fam bakwai. karamin Akushi kuwa ina sayarwa fam hudu, babban Akushi fam biyar. karama da babbar kujera su ma daga fam biyar zuwa fam bakwai. Haka abin kama zuma, shi ma akwai babba da karami, ya danganta da wanda mutum yake bukata.
A ina kake samun itacen da kake sassaka turmin?
Ai bishiyar Maina ce ko kuma Darbejiya. Ana samunta a nan Saudiyya, saboda haka idan kana bukata za ka samu daga wurin dillalan da suke sayarwa. Su kuma suna saya ne daga masu yanko ta a daji. Mu ma kanmu muna zuwa mu yanko da kanmu a daji. Amma yawancin lokuta a kan zo a dauke mu idan za a yi ginin gida ko idan za a rushe gida, kuma ana so a sare bishiyoyin da ke gidan, mukan je mu sare mu kawo nan, mu sassaka turmi da su. Idan wurin da za a yi ginin gida ne ko za a rushe gida ba saya muke ba. Hasalima su ne suke biyanmu mu sare musu itacen. Ka ga riba goma-da-goma ke nan.
Mene ne bambancin sana’ar sassaka turmi a Najeriya da Saudiyya?
Gaskiya akwai bambanci da yawa. Bambancin shi ne ta gida ta fi wahala saboda komai da hannu za ka yi. Sare bishiyar da hannu za ka yi sassaka ma da hannu za ka yi, amma a nan Saudiyya komai da inji muke yi. Sare bishiyar da inji muke yi sassakar ma da inji muke yi. Cikin mintina kadan za ka gama turame masu yawa, amma idan a Najeriya ne sai ka yi awowi sannan za ka gama turmi daya. Kuma an fi samun kudi a nan Saudiyya. Ga babu wahala sosai, ga samun kudi da yawa a Saudiyya. A Najeriya kuwa ga wahala ga ba samun kudi.
Wadanne nasarori za ka iya bayyanawa ka samu a sana’ar?
Na samu nasarori da yawa. Ka ga na yi aure har mata uku da ita na biya musu kudin aikin hajji da ita nake ciyar da su da ’ya’yana. Na yi abubuwa da yawa wadanda ba za su lissafu ba. Kuma duk wata matsala da ta taso mini kai tsaye nake tunkarar ta ba tare da wata matsala ba.
Wace matsala kake fuskanta a nan Saudiyya?
Babbar matsalar da nake fuskanta ita ce, yadda hukuma take takura mana da kame. Duk takardar da kake da ita idan suka kama ka sai kawai su daure ka a gidan yari. Amma ba don kame ba da mun ji dadi sosai a nan kasar Saudiyya. Ba ni da matsalar karancin kayan aiki, amma ka ga a Najeriya akwai matsalar kayan aiki da kasuwa.
Mene ne burinka a nan gaba?
Burina shi ne, in ci gaba da wannan sana’a har na samu kudin da zan koma gida Najeriya in ci gaba da sana’ar nan. Ina da burin in samu jari in sayi kayan aiki na zamani, in koma in bude katafaren kamfanin sassaka turmi na zamani, ta yadda Larabawa da sauran mutane za su rika zuwa Najeriya suna saya ba tare da wata matsala ba.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya