Burina in ci kwallo 30 a gasar Premier ta bana- Shu’aibu Ibrahim
dan kwallon gaba a kulob din Giwa da ke garin Jos a Jihar Filato Shu’aibu Ibrahim ya bayyana cewa burinsa a kakar wasa ta bana shi ne ya ci kwallaye 30, sannan ya lashe kofin gasar Premier ta Najeriya ta bana. Shu’aibu dan kimanin shekara 20 ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa […]
dan kwallon gaba a kulob din Giwa da ke garin Jos a Jihar Filato Shu’aibu Ibrahim ya bayyana cewa burinsa a kakar wasa ta bana shi ne ya ci kwallaye 30, sannan ya lashe kofin gasar Premier ta Najeriya ta bana.
Shu’aibu dan kimanin shekara 20 ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Jos a lokacin da suke atisaye a ranar Lahadin don fuskantar wasan da za su yi da kulob din Kwara United a ranar 2 ga Agusta.
Shu’aibu wanda ya ci kwallaye 5 a wasanni 9 na farkon gasar a bana sai da ya yi wasanni biyar ba tare da ya ci kwallo ba, daga baya ya samo bakin zaren ta hanyar ci wa kulob dinsa kwallo ta 3 ta hanyar bugun tazara (free kick) a lokacin da suka kara da kulob din Elkanemi a Kaduna.
dan wasan wanda yana daya daga cikin ’yan wasan da tsohon kocin Najeriya Stephen Keshi ya gayyata a lokacin da Najeriya ta buga wasa neman gurbin gasar cin kofin Nahiyar Afirka mai zuwa da kasar Chadi a Kaduna a kwanakin baya, ya jaddada kwarin gwiwarsa na cimma kudurinsa na cin kwallaye 30 da kuma lashe gasar premier ta bana, inda ya yi alwashin zai kara zage damtse don cimma kudurin nasa.
“Kamar yadda ka ga nake ta atisaye ba ji ba gani, ina sane da kudurin da nake so in cimma, don haka zan zage damtse sosai a lokacin wasanni, ba zan rika barin damar da na samu ta rika kufce mini ba. Burina in ci kwallaye 30 a bana, sannan mu lashe kofin gasar na bana. Idan Allah Ya yarda burina zai cika. A yanzu dai dan wasan ya jefa kwallo 10 a wasanni 19, inda sauran kwallo 20 ya cika burinsa na cin kwallaye 30.