Burina in gina gidauniya don taimaka wa marayu – Garkuwar Muri

Garkuwar Muri Malama Salamatu Dauda Aliyu da aka fi sani da Salma Garkuwar Muri ta bayyana niyyarta ta kafa gidauniyar kula da marayu. Salma Garkuwa ta bayyana haka ne lokacin da take tattaunawa da Aminiya, inda ta ce ganin yawaitar marayu a unguwanni ne ya sa ta samar da gidauniyar don taimaka wa marayun da […]

Burina in gina gidauniya don taimaka wa marayu – Garkuwar Muri

Malama Salma Garkuwar Muri

Garkuwar Muri Malama Salamatu Dauda Aliyu da aka fi sani da Salma Garkuwar Muri ta bayyana niyyarta ta kafa gidauniyar kula da marayu. Salma Garkuwa ta bayyana haka ne lokacin da take tattaunawa da Aminiya, inda ta ce ganin yawaitar marayu a unguwanni ne ya sa ta samar da gidauniyar don taimaka wa marayun da dan abin da take samu a rayuwa.

Salma Garkuwar Muri, ta  ce burinta a rayuwa kafin ta koma ga mahaliccinta shi ne ta ga ta yi sanadiyar samar da wata hanya da za ta iya daukar nauyin wadansu marayu ko kadan ne don rage wa ’yan uwansu dawainiyar yau da kullum.

Ta ce, yanzu haka tana da marayu na ’yan uwa kuma tana ganin yadda wadanda aka aka bar su da  marayu suke fama da su, ganin yadda rayuwa ta yi tsada.

A cewarta Annabi Muhammad (SAW) ya ce duk wanda ya taimaki maraya za su tashi tare da shi a Aljanna don haka take kiran jama’a su bullo da hanyoyin ganin sun dauki nauyin maraya daya ko biyu ko uku da ke tsakanin al’umma.

Salam Garkuwar Muri, ta ce ba sai ta gina gida ta tara su waje daya kamar gidan marayu ba, gidauniyar kawai za ta samar da za ta rika gudanar da komai bisa tsari.

Ta ce marayun da ke gidajen marayu a suna dagata domin gwamnati da sauran masu hannu da shuni suna kai musu gudunmawa amma wadanda suke tsakanin ’yan uwa a unguwanni ba a cika kula da su ba, don haka ta wannan hanya ta wani ya dauki nauyin daya ko biyu ba ne za su samu kula.

Ta ce, tana son ta fara da samar musu da sutura da tallafin abinci da kudaden makaranta daidai gwargwado  inda za ta fara daga matakin firamare.

Sai ta yi kira ga masu hali su dubi halin da marayun ke shiga a lokutan Sallah da kowane mai iyaye ke walwala amma maraya na tagumi.

Sai ta shawarci jama’a su taimaka wa marayu domin duk yaron da ya tashi ya ga bai da uba zai ji rayuwa ta yi masa kunci amma idan yana samun tallafi ba zai dauka shi maraya ba ne.