Burina in gyara tarbiyyar matasa masu bangar siyasa – Dokta Hajara Ibrahim Salim

Hajiya Dokta Hajara Ibrahim Salim, gogaggiyar ma’aikaciyar gwamnati ce wacce ita ce mace ta farko da ta fara zama Akawun Majalisar Tsara Dokoki na Jihar Gombe (Clerk) tun kafin kafuwar majalisar bayan an bai wa Gombe jiha daga jihar Bauchi a tsakanin shekarun 1996 zuwa 2000.  Ta taba zama Kantomar riko ta karamar Hukumar Gombe […]

Burina in gyara tarbiyyar matasa masu bangar siyasa – Dokta Hajara Ibrahim Salim

ibrahim salim

Hajiya Dokta Hajara Ibrahim Salim, gogaggiyar ma’aikaciyar gwamnati ce wacce ita ce mace ta farko da ta fara zama Akawun Majalisar Tsara Dokoki na Jihar Gombe (Clerk) tun kafin kafuwar majalisar bayan an bai wa Gombe jiha daga jihar Bauchi a tsakanin shekarun 1996 zuwa 2000.  Ta taba zama Kantomar riko ta karamar Hukumar Gombe a 1998 zuwa 1999 sannan kuma fitacciyar ’yar siyasa ce a Gombe wacce ake ji da ita a yankin Gombe ta tsakiya da ma Jihar Gombe baki daya kuma ta yi takarar Sanata a shekarar 2016. A tattaunarwata da Aminiya ta tabo tarihin rayuwarta da sauran batutuwa kamar haka:

Tarihin rayuwata:

Sunana Dokta Hajara Ibrahim Salim, ni  ’yar asalin garin Kumo ce  a karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe.  An haife ni a ranar 13 ga watan Maris shekara ta 1956 tun ana Northern Nigeria jihohi 19 na arewa, ni ce babba a cikin ’ya’ya takwas da mahaifin mu ya haifa.   Na girma a bukuru da ke Jos a Jihar Filato  sannan sai aka sa ni a firamaren Kwana ta ’yan mata ta Kabo Girls Boarding da ke Kano a shekarar 1962 zuwa 1968 bayan na gama sai na tafi Makarantar Mission a garin billiri a shekarar 1969 zuwa 1973 mu ne daliban farko mata da muka fara gamawa kuma makarantar maza ce mu hudu ne kadai mata a wancan lokacin idan mutum ya gama sakandare aiki jiransa yake yi ba shi ne yake jiran aikin ba.

Aiki:

Na fara aiki ne da babbar kotu a garin Maiduguri a matsayin mai yin fassara a kotu a shekarar 1975 inda na yi watanin biyar.   Lokacin albashina Fam 19 ne daidai da Naira 38.   A waccan shekarar ce aka canja Naira a lokacin kudin jirgi da na je Landan a lokacin zuwa da dawowa Naira 48 ne lokacin Naira tana da daraja idan kaje kasar waje har bin ka turawa suke yi ko ka je da Naira ka canjar musu. Aikin watanni biyar kadai na yi sai na tafi Cibiyar samun horo ta Ma’aikata da ke garin Potiskum a matsayin sakatariya wato Stenographer daga 1975 zuwa 1977 sai na koma NTTC (National Technical Teachers Collage) wacce yanzu ita ce  FCE (T) lokacin su biyu ne kawai a Najeriya daya a Yaba Legas sai daya a Gombe.   A 1980 sai na yi hidimar kasa NYSC a Commercial Collage Zariya da ma a ka’ida idan ka gama ta a lokacin za ka yi hidimar kasa na shekara daya, bayan gama NYSC di na sai na yi koyarwa a Azare a 1981 zuwa 1989 daga nan sai na tafi Ingila na yi digiri sannan digiri na biyu wato Masters a Jami’ar Jos a 1990 sai na tafi Jami’ar St. Clements a Landan na yi digiri na uku (Dokta) a 2006.

kalubalen da na fuskanta:

Ka yi aiki da maza a rayuwa akwai kalubale domin idan kuna aiki namiji ya ga mace ta fi shi kokari sai ka ga yana ta bin duk wata hanya da zai bi don ganin ya take ta ba ta kai ko’ina ba, saboda wasu ba sa so su ga mace ta ci gaba suna wajen domin a wancan lokacin ina cikin  mata na farko da suka fara yin fice a yankin Arewa Maso Gabas.

Nasarori:

Gaskiya nasarorin da na samu ba za su misaltu ba domin duk wani rufin asiri da na samu yanzu a rayuwa da nake cikin sa nasarar aiki ne kuma na yi gwagwarmaya har na kai matsayin babbar Darakta a gwamnatin tarayya kafin na yi ritaya sannan kuma har yanzu a wasu lokutan ana neman mu don bada shawara a wasu bangarorin aikin gwamnati.

Kwasa-kwasan da na je:

Na je kwas a Jami’ar Harbard da ke Amurka kan mata da mulki a shekarar 2012 sannan na je Landan kan samun horo da gudanar da mulki a 2010 na sake zuwa Landan kwas na manyan ma’aikata  a 2010, na je Johannesburg a Afirka ta kudu kan mata da mulki a 2009 sannan na je Malaysiya a 2009 na kuma sake zuwa Australiya  da sauran su.

Mukaman da na rike:

Na rike mukamin sakatariya na (Logistics) bangare kula da kayayyaki na taron tsarin mulkin kasa a Abuja 1994 zuwa 1996 sannan na rike mukamin Shugabar karamar hukumar Gombe ta riko daga 1998 zuwa1999.   Na zama akawun majalisar dokokin jihar (Clerk) ta farko daga shekarar 1996 zuwa shekarar 2000 na kuma rike shugabar kwamitin akawun  majalisar dokokin jihar Bauchi na riko a 1990 zuwa1993 sannan na zama Malama a cibiyar ci gaban Malamai ta Azare da ke Jihar Bauchi a 1980 zuwa 1989  daga nan sai na rike Darakta kuma shugabar sashi a majalisar wakilai ta Najeriya (National Assembly) a1993 zuwa 2014.

Hutu:

A lokacin da nake aiki har zuwa yanzu idan lokacin yin hutu na ya yi babu inda ba na zuwa hutu daga nan gida Najeriya har zuwa kasashen ketare musamman kasashen Afirka.

Lambobin yabo da na samu:

Na samu lambar yabo daga daliban Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, sun ba ni lambar yabo na iya jagoranci a mulki. Na samu lambar yabo daga Matan Shiyyar Arewa (Northern Nigerian Women), na samu lambar yabo daga daliban Kudu maso Kudu na Najeriya, na samu lambar yabo na wacce ta kware wajen rubutun shorthand daga NTTS Gombe, na samu lambar yabo daga wata jarida ta Treasury na wacce take da kishin ci gaban al’ummar karkara, na kuma samu lambar yabo na macen da ta sadaukar da kanta wajen yi wa al’umma hidima daga kungiyar daliban aikin Akanta na Kwalejojin Kimiyya da Fasaha (Polytechnics, NAPAS).

Tufafi:

Kasancewa ta ’yar asalin Arewa na fi sha’awar sanya tufafin da zai rufe mini jiki gaba daya musammam ma doguwar riga na sanya gyale duk wanda ya ganni ya san cewa ni ’yar Arewa ce.

Burina a rayuwa:

Burin da na nake da shi a rayuwa shi ne in gina gidan marayu mai suna Al-gidan Umma Hajara, (AL-GUH)  don kula da marayu da marasa gata don ina son duk wanda ya shigo gidan ya zama yana karkashin kulawa ta. Ina son in zama uwar marayu ne kafin karshen rayuwa ta.

Dalilin shiga ta siyasa:

Na shiga siyasa ne don  na kawo karshen ta’addancin da ’yan siyasa suke sa matasa a ciki na lalata musu tarbiyya da tunani kuma in Allah ya yarda na dauki damara sai na kawo karshen hakan a Gombe.

Sarautar gargajiya:

Ina da sarautar Hagalare ta gargajiya wacce Galadiman Akko ya ba ni tun a shekarar 1999 ta Jakadiyar Akko.

Yawan Iyali:

Ina da aure da ’ya’ya da jikoki

Shawarata ga iyaye:

Ina mai bai wa iyaye shawarar su sanya ‘ya’yansu su yi karatun zamani da na addini domin duk macen da ba ta yi ilimi ba ta zama ballagaza saboda babu a inda za ta yi daraja, kuma iyaye su sani kamar ni da na kai wani matsayi da yawa a kasar nan ilimi ne ya kai ni da ban yi ilimi ba da ban kai wannan matsayin ba, don haka iyaye su gane ilimi a wurin mace abun nema ne.   Sannan ba na goyon bayan dorawa ’ya’ya mata talla saboda talla na lalata tarbiyyar yara.