Burina in inganta rayuwar mata – Dokta Badiyya Hassan Mashi
Dokta Badiyya Hassan Mashi kwararriyar malamar Nazarin Kananan Halittu (Microbiology) kuma tsohuwar malama ce a Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Hassan Usman Katsina wato Hassan Usman Katsina inda ta koyar a fannin na tsawo shekara 25. Har ila yau malama ce da take ziyartar Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa kafin ta zama Kwamishinar Harkokin Mata ta […]
Dokta Badiyya Hassan Mashi kwararriyar malamar Nazarin Kananan Halittu (Microbiology) kuma tsohuwar malama ce a Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Hassan Usman Katsina wato Hassan Usman Katsina inda ta koyar a fannin na tsawo shekara 25. Har ila yau malama ce da take ziyartar Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa kafin ta zama Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Katsina a shekarar 2016. A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana tarihin rayuwarta da ma sauran wasu batutuwa kamar haka:
Rabilu Abubakar a Katsina
Tarihin rayuwata:
Sunana Dokta Badiyya Hassan Mashi, Kwamishinar Harkokin Mata. Ni ’yar Karamar Hukumar Mashi ce a Jihar Katsina amma a gidan Durbin Katsina Hakimin Mani, Kakana na wajen mahaifiya aka haife ni a bisa al’adarmu ta Hausawa (kasancewata ’yar fari). Da na girma na kai shiga firamare sai aka sa ni firamare ta Gidado da ke garin Katsina. Bayan na kammala sai na tafi GGSS Malumfashi inda na kammala karatun sakandare. Bayan na gama a 1986 sai na samu tafiya Jami’ar Bayero ta Kano inda na yi digiri na farko a bangaren Nazarin Kananan Halittu na fita da takarda mai daraja ta biyu (2nd Class Upper) daga nan sai na sake komawa Jami’ar Bayero na yi digiri na biyu, sai na sake yin digiri na uku (Phd) a bangaren Enbironmental Microbiology. Na yi karatu a bangaren Kimiyyar Sabunta Makamashi (Renewable Energy Technology). Na zama mamba a Jami’ar Greenwich Unibersity da ke Landan. Na yi bincike da nazari a wannan bangaren. Na kuma yi rubuce-rubuce na mukala da mujallu a cikin gida da kasashen waje.
Aiki:
Na fara aiki ne a 1992 a matsayin malama a Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Hassan Usman Katsina, har na tsawon shekara 25 sannan ina ziyarar koyarwa a Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa daga bisani a shekarar 2016, Gwamna Aminu Bello Masari ya ba ni Kwamishinar Harkokin Mata har zuwa yanzu.
Nasara:
A matsayina ta malamar Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere na taimaka wa yara da dama wajen harkokin kimiyya saboda a kasar nan an bar yankin Arewa a baya wajen yin bincike da sauran abubuwan da suka shafi sha’anin kimiyya don mu zama abin koyi nan gaba. Kamar ni, na taso ne a babban gida inda kowa ya yi karatu hakan ta sa ba na so in ga an bar wadansu a baya. A wajena wannan taimako da na bayar shi ma nasara ce gare ni, sannan a matsayina ta Kwamishina, ma’aikatarmu ta aiwatar da ayyuka masu dimbin yawa na ci gaban mata a fannonin kiwon lafiya, ilmi, kasuwanci, aikin gona, addini, zamantakewa da sauransu.
Mun samu nasarori musamman ta fuskar bunkasa tattalin arzikin mata ta hanyar ba su jari ko tallafi musamman mata masu karamin karfi a kungiyance ko a daidaikunsu, la’akari da burin Gwamna Aminu Bello Masari na bunkasa rayuwar matan Jihar Katsina da kuma kokarin cika musu irin alkawurran da ya yi musu.
Mun samu nasarar yin gangami da kuma kaddamar da yaki da shan miyagun kwayoyi, yaki da cutar tamowa wato yunwa da yara kanana suke fama da ita a Jihar Katsina ta fuskar wayar wa iyaye mata kai da samar musu abinci mai gina jiki da fadakarwa a kan muhinmmacin allurar rigakafin cututtukan kananan yara da muhimmancin zuwa awo da kuma haihuwa a asibiti da kulawa da horar da mata masu yoyon fitsari da gyara da gabatarwa a gaban Majalisar Dokokin Jiha daftarin dokar kare hakkin kananan yara da kafa wuraren ci gaban mata da koyon sana’a a kauyuka da kananan hukumomi da tallafa wa mata marasa lafiya musamman masu cutar daji da tallafa wa marayu da matasa ta bangaren kungiyoyin sa-kai a fannoni daban-daban da tallafa wa nakasassu ta hanyar ba su jari da ababen inganta rayuwarsu da sauransu.
Kalubale:
Kalubalen shi ne a kullum muna neman ’ya’yanmu su shiryu amma sai ga wadansu iyaye mata sun fada harkar shaye-shaye, duk da ma’aikatarmu tana koya musu sana’oi ta hanyar horar da su yadda za su dogara da kansu amma lamarin a wani lokaci yana son fin karfinmu. Wannan shi ne babban kalubalena.
Burina a rayuwa:
Burina a rayuwa shi ne a yanzu da nake Kwamishina ina son in ga na yi aiki tukuru don inganta rayuwar matan Jihar Katsina da na sauran sassan kasar nan. Da fatan Allah Mai girma da daukaka Ya kara mini jagoranci.
Hutu:
Tun ina malamar makaranta ba na samun isasshen hutu saboda yawan bincike da nazari balle kuma yanzu da nake rike da mukamin siyasa na kula da harkokin mata, kullum muna cikin aiki. Kasashen da na je :
Na je aikin ibada kasar Saudiyya sannan na je Dubai da Masar da Indiya da Ingila da Faransa da Turkiyya da Nijar da sauransu.
Kungiyoyi:
Ni mamba ce a kungiyoyi da yawa kuma shugabar kungiyoyi masu zaman kansu daban-daban saboda, kasancewata Kwamishinar Harkokin Mata, ma’aikatarmu tana tafiya da kungiyoyi daban-daban.
Tufafi:
Kasancewata ’yar Arewa, Bahaushiyya, Musulma, na fi son in daura zane da riga sannan in sanya hijabi wanda zai rufe mini jiki, duk wanda ya gan ni ya san ’ya ga mace mai mutunci da kamala.
Yawan iyali:
Alhamdulillah, Allah Ya azurta ni da ’ya’ya biyar, uku maza, biyu mata. Ukun sun gama jami’a biyun suna kai.
Shawara ga iyaye:
Shawarata ga iyaye shi ne su sa ’ya’yansu a makaranta musamman mata saboda karatun ’ya mace yana da muhimmanci domin ko ni mu hudu muka taso kanmu daya, mahaifinmu yana shirya mana gasa duk wanda ya yi kwazo ya kan yi masa kyauta ta musamman, ta haka ya rika zaburar da mu har muka gama karatu.
Ka ga ashe karatun ma idan ’ya’ya suna samun kulawar iyaye suna kara kokari.
Sannan ina kira ga iyaye su rika kara wa ’ya’yansu kwarin guiwa, wannan yana taimaka musu wajen yin karatu.
Har ila yau dora wa yara talla yana lalata tarbiyyarsu don haka iyaye su gane cewa karatu shi ne mafita ga rayuwar ’ya mace ba talla ba.