Burina in kawo canjin da zai amfani jama’ata – Tijjani Aliyu

dan takarar kujerar Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar APC daga mazabar Azare da Madangala a karamar Hukumar Katagum Alhaji Tijjani Muhammad Aliyu ya ce babban burinsa na son zama wakilin jama’arsa a majalisar shi ne don ya kawo canjin da za su amfana. Alhaji Tijjani Aliyu wanda yake tsayawa takarar kujerar a […]

Burina in kawo canjin da zai amfani jama’ata – Tijjani Aliyu
Burina in kawo canjin da zai amfani jama’ata – Tijjani Aliyu

dan takarar kujerar Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar APC daga mazabar Azare da Madangala a karamar Hukumar Katagum Alhaji Tijjani Muhammad Aliyu ya ce babban burinsa na son zama wakilin jama’arsa a majalisar shi ne don ya kawo canjin da za su amfana.

Alhaji Tijjani Aliyu wanda yake tsayawa takarar kujerar a karo na uku ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a Azare, inda ya ce da don kashin kansa yake
tsayawa takara da ya hakura domin ya nemi wannan matsayi a shekarar 2007 da 2011 bai yi
nasara ba, amma da yake yana yi ne don al’ummarsa su amfana, ya sa ya sake dawowa don fafatawa.
Alhaji Tijjani Aliyu ya ce, ya kamata a wayar da kan mutane game da aikin ’yan majalisa inda ya ce hatta su kansu ’yan majalisar da dama ba su san aikinsu ba, ko kuma sun sani suna yin abin da suka ga dama, maimakon tsayawa wajen yin dokokin da za su inganta rayuwar jama’arsu da tabbatar ana sarrafa dukiyar gwamnati ta hanyar da ta dace a samu a inganta rayuwar jama’a.
Sai ya yi kira ga al’ummar mazabar da ta jihar da kuma ta Najeriy su guji siyasar gaba da juna kuma su gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali, kuma ya shawarci magoya bayan Jam’iyyar APC su fito su yi zabe tare da tsayawa don kare kuri’unsu har sai sun raka sun kuma jira sakamako.