Burina in kera keke mai taya hudu—Shamsuddeen

Shamsuddeen Adam, mai sana’ar walda ne a Jos da ke Jihar Filato, ya kware wajen kera gadaje da kujerun karfe. A hirarsa da Aminiya ya bayyana matsalolin da yake fuskanta, nasarorin da ya cimma dalilin sana’ar da kuma burinsa a nan gaba. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Aminiya: Za mu fara da gabatar da kankaShamsuddeen: […]

Burina in kera keke mai taya hudu—Shamsuddeen
Burina in kera keke mai taya hudu—Shamsuddeen

Shamsuddeen Adam, mai sana’ar walda ne a Jos da ke Jihar Filato, ya kware wajen kera gadaje da kujerun karfe. A hirarsa da Aminiya ya bayyana matsalolin da yake fuskanta, nasarorin da ya cimma dalilin sana’ar da kuma burinsa a nan gaba. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Za mu fara da gabatar da kanka
Shamsuddeen: Assalamu alaikum, sunana Shamsudden Adam. Na yi makarantar Firamare a unguwar Rogo da ke Jos, Jihar Filato, daga nan na fara makarantar karamar sakandare a Kwanar Shagari, bayan mun yi jarrabawar 6334, sai na koma Jihar Zamfara, inda na ci gaba da karatu.
Aminiya: Yaushe ka fara sana’ar walda?
Shamsuddeen: Na fara a shekarar 2009, a lokacin ina karamar sakandare a Kwanar Shagari cikin garin Jos ke nan, a lokacin idan na je makaranta bayan an tashi sai in wuce wurin koyon aiki. A nan Kwanar Shagari na koyi yadda ake kera gadaje da kofofi da tagogi da kujerun karfe, a nan na koyi yadda ake sarrafa karafa.
Bayan mun yi jarrabawar 6334, sai kanen mahaifina da ke Jihar Zamfara ya bukaci in koma wajensa da zama don kuma in ci gaba da karatu. Hakan ya sa na koma can, inda a Zamfara ma na ci gaba da zuwa wajen aikin walda. A nan samu kwarewa sosai.
Aminiya: Me ya dawo da kai Jos?
Shamsuddeen: Bayan na kammala karatun sakandare, na kuma samu jari sai na yanke shawarar in dawo nan Jos, don in kafa nawa. Shi ne ka gan ni a nan yanzu.
Aminiya: Bayan ka dawo Jos me ka fi mayar da hankali wajen kerawa?
Shamsuddeen: Na mayar da hankali wajen kera gadajen karfe, inda ko yanzu ma da ka same ni gadon nake kerawa. Sannan ina kera kofofin karfe, nakan yi kera kujerun karfe daban-daban.
Aminiya: Kana samun ciniki bayan yanzu an fi mayar da hankali kan gadaje da kujeru na zamani maimakon na karfe?
Shamsuddeen: Ba wai gadajen karfe ba ne kawai, a’a, nakan kera su yadda za su tafi da zamani, akwai salo-salo masu daukar hankali, idan ka gan su sai ka yi sha’awarsu, don haka jama’a suna sonsu. Bayan mun kera su za mu yi musu fenti mai sheki, za ka rika ganin irin kujerun a wuraren shakatawa. Nakan sayar gado mai fadin kafa shida da shida a kan Naira dubu 25 zuwa sama.
Aminiya: Wadanne matsaloli ka fuskanta a sana’ar walda?
Shamsuddeen: A yanzu dai zan iya cewa ina fama da karancin jari, domin akwai abubuwa masu yawa da nake so in kera wadanda rashin isasshen jari ya kawo mini tarnaki. Idan har da ina da jari akwai nau’in keken hawa da nake so in rika kerawa, wannan nau’in keke ya bambanta da wanda aka saba gani, zan yi shi mai taya hudu ne, wanda zai rage hadari.
Aminiya: Wadanne nasarori ka samu dalilin sana’ar walda?
Shamsuddeen: A har kullum na tuna cewa ina daya daga cikin wadanda suka sanya kofofi 150 a Jami’ar Dutsin-Ma da ke Jihar Katsina nakan ji farin ciki ya kama ni, domin ina alfahari da hakan, musamman ma cewa na bada gudunmuwa a fannin ilimi, ka ga wannan nasara ce. Na biyu dalilin wannan sana’ar nake ci da sha da taimakon ’yan uwa da abokan arziki, sannan akwai yaran da nake koyawa.
Aminiya: Yanzu wane buri kake so ka cimma?
Shamsuddeen: Burina in kera keke mai taya hudu, da hakan zai zama keke na farko mai taya hudu a Najeriya.
Aminiya: Da yaya kake yunkurin cimma wannan burin?
Shamsuddeen: Idan na samu isasshen jari magana ta kare.
Aminiya: A yanzu wane kira kake da shi ga gwamnati?
Shamsuddeen: Ina kira ga gwamnati ta tallafa wa masu sana’ar walda, masu sana’a irin tamu suna da fasaha da idan sun samu tallafin gwamnati- ta hanyar ba su jari ko samar musu da kayayyakin da suke bukata, to za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki, domin za su rika kera kayayyakin da za a rika saya a Najeriya ba sai an fita zuwa waje ba. Sannan ina rokon masu sana’ar hannu su tsare gaskiya, su kuma rika cika alkawari, domin yawancin masu sana’ar hannu suna da wadannan matsalolin.