Burina in mallaki awaki dubu – Barista Tamatuwa
Wani lauya mai zaman kansa da ke Gombe, Barista Abdullahi Muhammad Inuwa Tamatuwa, da ya kware wajen kiwon awaki ya ce yana fata ya mallaki awaki dubu don cikar burinsa a rayuwa. Barista Abdullahi Tamatuwa ya ce zamansa a wajen Bappansa a tsohuwar Jihar Bauchi, lokacin yana ma’aikaci a Ma’aikatar Gona kuma yana kiwo ne […]
Wani lauya mai zaman kansa da ke Gombe, Barista Abdullahi Muhammad Inuwa Tamatuwa, da ya kware wajen kiwon awaki ya ce yana fata ya mallaki awaki dubu don cikar burinsa a rayuwa.
Barista Abdullahi Tamatuwa ya ce zamansa a wajen Bappansa a tsohuwar Jihar Bauchi, lokacin yana ma’aikaci a Ma’aikatar Gona kuma yana kiwo ne ya sa shi ma ya koyi kiwon awaki inda a yanzu yake da fiye da awaki 100 na gida da na waje.
Barista Tamatuwa ya ce ya fara kiwo ne da guda 10, suna hayayyafa yana sayo wasu; har suka kai 127. Amma saboda rashin kula na makiyaya a daji wadansu sun mutu wadansu kuma an sace su. Ya ce awakin iri-iri ne; akwai ’yan kasa masu matsakaicin tsawo akwai ’yan Arewa, akwai jajaye ’yan Sakkwato har da wani da ake kiransa BOAR dan kasar Afirka ta Kudu. A cewarsa BOAR din a garin Hadeja a Jihar Jigawa ya sayo shi kan Naira dubu 40, kuma ya yada iri kafin cuta ta kama shi ya mutu. “Akwai ma irin awakin Somaliya wadanda sha’awar kiwon ya sa nake nemo su in kawo su cikin awakina; amma saboda rashin lokaci sannan masu yi min kiwo ba sa kula da su yadda ya kamata ya sa wasu suke mutuwa wasu ake sace su a daji,” inji shi.
Ya ce burinsa a kiwon awaki shi ne su kai dubu daya; sannan ya nemi babbar gona mallakinsa da zai shuka musu abinci da magarya yana killace su a gonar, kuma likitoci suna kula da su a wajen.
A bangaren magani da abincinsu, ganin kiwon su bai da wahala kamar na raguna; Barista Tamatuwa, ya ce yana kashe abin da bai gaza Naira dubu 50 ba duk shekara da yake a daji suke suna samun abinci ko’ina, kuma kiwon da yake yi ba gasa yake yi da wani ba yana yi ne domin ra’ayin kansa. Ya ce a baya yana hadawa da kiwon talo-talo da agwagi da kaji da shanu; amma rashin kulawa ya sa ya hakura ya tsaya iya awakin.
Barista Tamatuwa ya ce kiwon akwai riba sosai musamman idan aka samu kulawar da ta dace a cikin kankanen lokaci mutum zai samu riba; amma rashin kulawar da ta kamata ce take sawa ake samun ’yan matsaloli a kiwon.