Burina in mayar da noman lambu da kiwon kaji sana’a idan na bar aiki – Salamatu Dahiru Biri

Hajiya Salamatu Jijji Gadam da aka fi sani da Salamatu Dahiru Buba Biri, ita ce Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Ilimi Mai zurfi ta Jihar Gombe, tsohuwar malamar makaranta kuma da ta fara koyarwa tun 1990 ta yi ayyuka a wurare daban-daban har ta zama Babbar Sakatariya. A zantawarta da shafin Zinariya ta bayyana tarihin rayuwarta […]

Burina in mayar da noman lambu da kiwon kaji sana’a idan na bar aiki – Salamatu Dahiru Biri

Hajiya Salamatu Dahiru Biri

Hajiya Salamatu Jijji Gadam da aka fi sani da Salamatu Dahiru Buba Biri, ita ce Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Ilimi Mai zurfi ta Jihar Gombe, tsohuwar malamar makaranta kuma da ta fara koyarwa tun 1990 ta yi ayyuka a wurare daban-daban har ta zama Babbar Sakatariya. A zantawarta da shafin Zinariya ta bayyana tarihin rayuwarta da wasu bangarori kamar haka:

Tarihin rayuwata

Sunana Hajiya Salamatu Jijji Gadam, da na yi aure da maigidana Alhaji Dahiru Buba Biri, sai na canja suna zuwa Salamatu Dahiru Buba Biri. Ni ’yar kabilar Bolawa ce ta garin Gadam a Karamar Hukumar Kwami a Jihar Gombe. Mijina ma Babolin Biri ne a Karamar Hukumar Nafada a Jihar Gombe. An haife ni a 1961 a garin Gombe, a nan na girma aka sa ni a makarantar firamare ta Central wacce yanzu aka mayar da ita Hassan Central Model Primary, a 1968 zuwa 1974, bayan na gama sai na tafi Sakandaren Gwamnati (GSS) ta Gombe daga 1974 zuwa 1979, daga nan sai na tafi kwalejin Adbance Teachers College, Azare wacce yanzu ita ce Kwalejin Ilimi (COE) da ke Azare, daga 1979 zuwa 1982 inda na samu takardar shaidar Malanta ta Kasa (NCE) da na gama sai na je hidimar kasa (NYSC) domin a wancan lokaci idan mutum ya yi NCE zai yi hidimar kasa kamar mai digiri. Ina NCE 1 a lokacin aka yi min aure da na gama ban ci gaba da karatu ko aiki a lokacin ba saboda mijina yana aiki ne a Gwamnatin Tarayya sai muka koma Jos daga nan sai aka mayar da shi Sakkwato, a 1986  muka bar Sakkwato muka dawo Adamawa ya koma aiki a Kamfanin Sukari na Sabannah a wancan lokaci ne na koma karatu a Jami’ar Maiduguri, a lokacin ina da ’ya’ya 3 kuma ba wata jami’a a kusa sai Jami’ar Maiduguri da Jos da kuma ABU, na gama digirina na farko a 1989 a bangaren (Ilimi) Ingilishi da Nazarin Addinin Musulunci. A shekarar 2000 sai na sake komawa Jami’ar Maiduguri na yi digiri na biyu (Ilimi) Harkokin Mulki na gama a shekarar2006.

Aiki

Na fara aiki a tsohuwar Jihar Bauchi a matsayin malamar makaranta a garin Cham lokacin Cham don ba a kirkiro Jihar Gombe ba. Lokacin kuma muna Adamawa da maigidana yana aiki, a shekara ta 2006 din lokacin na bar mijina a Sabannah na dawo Gombe sai aka sake tura ni makaranta Sakandaren Gwamnati ta Gandu a fadar jiha ban wuce wata biyu a wajen ba don ko aji ban shiga ba lokacin suna hutu sai aka sake dauke ni aka mayar da ni Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Gombe (Muslim Pilgrim Welfare Board) a matsayin jami’a mai kula da harkar mulki, a wajen na zama Mataimakiyar Sakatariya na kuma zama Sakatariya inda na kai shekara goma sha uku ina aiki, kafin a shekarar 2013 a  canja min tsarin aiki daga harkar malanta zuwa sashin mulki inda na zama Mataimakiyar Darakta. Ina nan sai aka sake canja min wajen aiki zuwa Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta Jihar Gombe (GOSIEC )ina kula da ofishin Daraktan Kudi da Mulki (DAF) a wannan lokacin aka tabbatar min da mukamin Darakta sai aka mayar da ni Ma’aikatar Ayyuka a shekarar 2015 na yi shekara biyu, a watan Satumban shekarar 2017 na zama Babbar Sakatariya aka rantsar da ni sai aka tura ni Ma’aikatar Ilimi Mai zurfi ta Jihar Gombe inda nake har yanzu.

Kalubale 

Akwai kalubale a aiki musamman ma a ce mace tana da aure kuma tana haihuwa ga aikin ofis inda za ta rika barin yara a hannun masu raino tana tafiya aiki duk da ma dai rayuwar wancan lokacin da yanzu akwai bambanci amma dai kalubale ne, kuma a hakan na bai wa ’ya’yana tarbiyya har suka girma ga shi dukkansu suna da digiri uku daga cikinsu kuma suna da digiri na biyu, kuma a lokacin ma dole miji ya rika hakuri da ke saboda dole ya jure wasu abubuwa ga kuma tallafin da ya bayar na kudin karatu da shawarwari. Kamar lokacin da nake Adamawa ina koyarwa a Cham kullum nakan tashi zuwa aiki daga Sabannah zuwa Cham wannan hadari ne sosai na yadda nake yawo a hanya da mota kullum kuma a lokacin albashi ko kudin mai ba zai ishe ka ba a wata.

Nasara

Nasarar da na samu a aikin gwamnati ba karama ba ce, domin daga malamar makaranta na fara ga shi yanzu ina matsayin Babbar Sakatariya wanda duk cikin wadanda muka yi karatu da su mu biyu ne da Hajiya Zainab I. Haruna kawai muka kai matsayin manyan sakatarori a gwamnati sai kuma Gwamnan Gombe na yanzu Alhaji Muhammad Inuwa Yahya, shi tun firamare ma ajinmu daya da shi a Central.

Burina

Burina a rayuwa shi ne idan na gama aiki na yi ritaya in koma gidan gona, domin yanzu hakaina da lambu orchat a garin Kwadom wanda har na fara cin moriyarsa wajen sayar da mangworori abin kuma yana ba ni sha’awa sannan zan hada da gidan kaji domin kajin gidan gona suna bukatar lokaci sosai.

Hajiya Salamatu Dahiru Buba Biri da iyalanta
Hajiya Salamatu Dahiru Buba Biri da iyalanta

 Abin da na fi so a tuna ni da shi

Ina son ko bayan raina a rika tunawa da  ni a matsayin mai taimaka wa mutane. Ka bar batun malamta da kowa ya san yadda malami ke taimakon dalibai a lokacin da nake Hukumar Jin Dadin Alhazai na taimaka wa mutane sosai a bangaren tafiya aikin Hajji.

Tufafi

Suturar da na fi sha’awa ita ce zane da riga da babban hijabi wanda zai rufe min jiki sosai, domin duk wanda ya gan ni ya ga na yi shiga ta kamala da dattaku irin wadda Musulunci ya koyar.

Yawan iyali

Alhamdulillah ina da ’ya’ya 7 maza 5 da mata 2 kuma dukkansu suna da digiri, uku daga cikinsu sun yi digiri na biyu kuma suna aiki, karamar cikinsu ce wato ’yar autana ta gama digiri na farko ba da dadewa ba a Jami’ar American Unibersity da ke  Yola.

Kasashe

Saudiyya na je ba adadi domin da nake aiki a Hukumar Jin Dadin Alhazai a shekara nakan je sau biyu saboda shirye-shirye aikin Hajji, sannan na yi aikin Hajji din na je Dubai na je Ingila da sauransu.

Kungiyoyi 

Ba na cikin wasu kungiyoyi amma dai ni mamba ce a Kungiyar Mata Musulmi ta Kasa (FOMWAN) a lokacin da nake Adamawa na zama Amira ma.

Shawara ga mata

Shawarata ga mata ita ce su rika bai wa ’ya’ya mata dama ta yin karatun boko, ni a gidanmu ba ni ce mace ta farko da ta fara karatun boko ba akwai yayyena sun yi, abin da ya kara daga sunan gidan Jijji Gadam shi ne saboda mahaifinmu ya san darajar ilimin ’ya mace. Akwai gidajen masu kudi da yawa da ko sunansu ba a ji saboda ba su yi karatu ba, don haka kada iyaye su bambanta ilimin ’ya’ya maza da na mata don idan aka ilimantar da ’ya mace an ilimantar da al’umma ce, shi kuwa namiji shi kadai ne. Sannan batun talla ba alheri ba ne ga yara mata domin a wajen talla yara suke lalacewa kuma tallar kanta ba ta da wani amfani sai zubar da kima da darajar iyayen. Kuma a tuna ilmin addini shi ne kan gaba domin idan yara suka ilimantu da boko da addininsu ko zaman gidan aure sai sun zama daban da wadanda ba su da ilimin.