Burina in rika tallafa wa marayu – Hajiya Baheejah Mahmood
Hajiya Baheejah Mahmood mace ce da ta yi fice a Jihar Bauchi a kokarin da take yi na tallafa wa marayu da marasa galihu. Ta taba rike mukamin Babbar Darakta a Hukumar Kula da Marayu da Yara Marasa Galihu a jihar kuma yanzu haka ita ce’yar takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar ACD. Wakilinmu […]
Hajiya Baheejah Mahmood mace ce da ta yi fice a Jihar Bauchi a kokarin da take yi na tallafa wa marayu da marasa galihu. Ta taba rike mukamin Babbar Darakta a Hukumar Kula da Marayu da Yara Marasa Galihu a jihar kuma yanzu haka ita ce’yar takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar ACD. Wakilinmu ya tattauna da ita inda suka tabo batutuwa da dama da suka shafi rayuwarta kamar haka:
Tarihina
Iyayena marigayi Malam Abdullahi Mahmood da Hajiya Khadija Mahmood sun haife ni ne a garin Azare a Karamar Hukumar Katagum a Jihar Bauci. Na yi makarantar boko da na addinin Musulunci a garin Azare, sannan na yi karatu a garuruwan Zariya da Gamawa da Gombe da kuma Bauchi. Yanzu haka ina da aure da ’ya’ya. Ni ’yar kasuwa ce kuma ina yin noma, na rani da na damina. Ina da ’yan uwa maza da mata, yayye da kanne.
Lokacin da nake karama
Alhamdulillah, ni da ’yan uwana mun samu rayuwa mai inganci lokacin da muke yara. Mahaifinmu alkali ne kuma ya tabbatar da cewa dukanmu (maza da mata) mun samu ilimin boko da na Musulunci daidai gwargwado. Na tashi tsakanin maza biyar inda duk gwagwarmaya a cikinsu na yi. Saboda duk wata gwagwarmaya da maza ke yi, da ni suke yin ta, har ta kai na kware. Hakan ya ba ni damar kula da yara musamman maza ba tare da na sha wahala ba.
Darussan da na koya a rayuwa
Darussan rayuwa da na koya suna da yawa, kuma har yanzu ina kan koyansu. Amma ina son mutunta mutane, rikon amana da son tallafa wa marayu da marasa galihu.
Abin da na so zama ina karama
Na so in zama mai ilimin sarrafa abubuwa kamar gine-gine da kuma tallafe tallafe, kuma ina son lura da yara. A gidanmu duk bakuwar da ta zo da yara, nakan hutasshe ta kulawa da su, saboda zan dauki yaro, in yi masa wanka, in ba shi abinci, in goye shi har sai ya yi barci. Hakan ya sa ’yan uwanmu sukan aiko da yara gidanmu idan ina nan, saboda in zauna da su. Alhamdulillah har yanzu babu abin da na fi so kamar kula da yara da ba su tarbiyya da gina dan Adam.
Dalilin da na yi suna wajen kula da yara da marayu
Kamar yadda na zayyana a baya, hakan ya samo asali ne tun ina karama, kuma Allah Ya taimake ni, lokacin da nake aiki, ya zamo gwamnatin lokacin ta ba ni damar kirkiro Hukumar Kula da Marayu da Marasa Galihu ta Jihar Bauchi. Samun wannan dama ke da wuya, sai na yi ta kirkiro hanyoyi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar marayu da marasa galihu, musamman ganin cewa marayu da marasa galihu kullum kara yawa suke yi kuma babu mai tunawa da su. Wannan ya sa na mai da hankalina a kansu, domin inganta rayuwarsu, kuma alhamdullahi an kafa wannan hukuma mun samu nasarori da dama kuma dukan al’ummar Jihar Bauchi sun rungumi wannan hukuma har ma wadansu daga cikin jama’a musamman ma’aikata suna ba da kashi daya na albashinsu don gudanar da wannan hukuma. Ka ga yarda da nasarorin da muka samu da aminci da amana kan ayyukan da muke yi ya sa aka samu haka.
Hada hidimar siyasa da ayyukan gida
A matsayina na uwa, ya zamo mini dole in kula da yanayin da gidana yake a kowane lokaci. Saboda haka duk abin da nake ciki nakan tuna da sha’anin iyalina kuma in tabbatar da komai na tafiya daidai bisa tsari na mussamman don gudanar da abubuwa daban-daban a kusan lokaci guda insha Allah.
Yadda nake yin hutu
Nakan yi kokarin hutawa, sai dai ba kamar yadda nake so ba, saboda wani lokaci, ina cikin hutawa za a bugo waya a ba ni labarin wani abin da yake bukatar taimakona, dole in tashi in je domin warware matsalar.
Kasashen da na ziyarta don yin hutu
Maganar hutu a wata kasa ba na yi, kuma ba ni da sha’awar hakan domin na fi jin dadin kasata fiye da kowace kasa a duniya. Amma Idan da hali nakan je wasu kasashe domin ziyarar ’yan uwana da suke can. Nakan je Saudiyya domin yin aikin Haji, ko wasu kasashen domin kasuwanci.
Abubuwan da na fi bukata
Na fi son koyaushe a ce ina da wani abin yi da zai amfane ni ko iyalina, ko al’umma baki daya. Ba na son zaman banza.
Nasarorin da na samu a rayuwa
Alhamdulillah, na samu nasarori a rayuwa. Ina da koshin lafiya, Allah Ya ba ni iyali da ke kaunata, kuma na kirkiro Hukumar Kula da Marayu da Marasa Galihu, wanda har yanzu ake morar tsare-tsaren da hukumar ke gudanarwa. Kuma ga shi ina takarar Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar ACD.
Yadda na hadu da mijina
Mun hadu ne a wurin aikinsa a banki a garin Bauchi
Abincin da na fi so
A gaskiya ba ni da wani zabi amma ina sha’awar tuwon samobita da miyar taushe.
Gudunmawar da mata za su iya bayarwa a siyasa
A Najeriya a yanzu, mata su ne karfin siyasa. Na farko dai, mata a matsayinsu na iyaye, Allah Ya ba su taushin zuciya a wajen mu’amala da mutane saboda haka suna da rawar ganin da za su taka. Tun a 1999 da mulkin dimokuradiyya ya dawo a Najeriya mata suna taka rawar gani wajen fita kada kuri’a, amma mazan da suke zaba a kullum sun gaza wajen aiwatar da ayyuka domin ci gaban al’umma. Saboda haka, yanzu lokaci ya yi da mata za su fito domin tsayawa takara a matakai daban-daban kuma mata ’yan uwansu su fito kwansu da kwarkwata su tsaya domin mara musu baya don samun nasara wajen ceton al’umma baki daya daga halin kuncin da ake ciki a yanzu.
Abin da ya sa na fito takarar Gwamnan Jihar Bauchi
Tun da siyasa ta dawo Najeriya a 1999 zuwa yanzu, maza ne ke mulki a mukaman tarayya da kuma jihohi, kuma babu wani ci gaban rayuwa da al’umma ta samu, wanda za a ce wannan ci gaba ya kawar da talauci da fatara da yunwa a cikin al’umma, kuma ya kawo bunkasar tattalin arziki da walwala yadda ya kamata. Saboda haka shi ya sa kungiyoyin mata suka nemi na fito domin na ceto su. Kuma yadda na ga dimbin maza da mata sun maraba da fitowata ya ba ni kwarin gwiwar yin gogaggaya inda na zama kallabi a tsakanin rawuna.
Burin da nake da shi idan na samu nasara
Tunda ake siyasa a Jihar Bauci, ka taba jin an yi Gwamna mace? Ka taba jin an yi Gwamna uwar ’ya’ya? Komai iyawar namiji, ba zai iya yin wani abin da mace za ta yi ba. Aikin da na fi kwarewa a kai shi ne inganta rayuwar dan Adam, saboda haka na san dabarun da zan bi domin inganta rayuwar al’ummar Jihar Bauchi musamman maza da mata da yara da matasa. Dukan gwamnatocin da suka shude har da mai ci a yanzu sun fi mai da hankalinsu ne a kan ayyukan kyale-kyale, mu kuwa za mu mai da hankalinmu ne a kan fito da tsare-tsare masu gina dan Adam da jihar, domin amfanin jama’a daya.
Shawara ga matasa
Matasa su ne ginshikin kowace al’umma. Kasar da ba ta da matasa masu kwazo, ta rasa zuriyar da za ta ciyar da ita gaba. Gaskiya, zuwa yanzu, wadansu ’yan siyasa da sauran marasa kishin kasa sun mayar da matasanmu abubuwan cimma burinsu. Ina kira ga matasanmu su yi kokarin samun ilimin boko da na addini saboda yin hakan shi zai fitar da su daga kangin rashi da bauta wa masu dukiya. Idan muka kafa gwamnati ko shakka babu za mu karfafa wa matasa gwiwa a bangaren sana’o’i da gina su a fannoni da dama don su ci moriyar rayuwa.
amma ina sha’awar tuwon samobita da miyar taushe.