Burina in rubuta ingantaccen littafi a rayuwata – Kareena Kapoor
Kareena Kapoor, kanwa ga ’yar fim kuma marubuciya, Karishma Kapoor ta bayyana cewa tana son nan gaba a rayuwarta ta rubuta littafi mai ma’ana kuma mai inganci.’Yar fim din, wacce a kwanan nan aka lura cewa ta maida hankali sosai ga karance-karance, tana son ne ta zama kamar yayarta Karishma, wacce ta dade da wallafa […]

Kareena Kapoor, kanwa ga ’yar fim kuma marubuciya, Karishma Kapoor ta bayyana cewa tana son nan gaba a rayuwarta ta rubuta littafi mai ma’ana kuma mai inganci.
’Yar fim din, wacce a kwanan nan aka lura cewa ta maida hankali sosai ga karance-karance, tana son ne ta zama kamar yayarta Karishma, wacce ta dade da wallafa littafi, baya ga sana’ar fim da take gudanarwa.
Kareena ta bayyana kudurinta na son zama marubuciya a yayin bikin kaddamar da littafin Don’t Lose Out, Work Out, wanda Rujuta Diwekar ya rubuta.
Da aka tambaye ta cewa ko tana son rubuta littafi ko labarin fim a rayuwarta, sai ta amsa da cewa: “Ban sani ba ko zan rubuta labarin fim amma dai ina da burin rubuta littafi a wata rana nan gaba a rayuwata. Ban yi wani tunani game da rubuta labarin fim ba, amma dai batun rubuta littafi, wannan al’amari ne mai kyau da ke sanya farin ciki.”
’Yar fim din wacce a bana ta cika shekara 33 a duniya, ta kara da cewa: “Na fara karance-karancen littattafai da yawa, domin fadada tunanina fiye da fitowa cikin fim. Bisa ga haka, wata rana zan iya rubuta littafi, sai dai ban san a wane maudu’i zan rubuta ba. Na taba rubuta gabatarwa ga littafin Rujuta, wanda haka ke nuna cewa lallai ina da sha’awar rubuta littafi.”