Burina in samar da zama lafiya da ci gaba a Jihar Bauchi –Gwamna Abubakar
A tatttaunawa da manema labarai a karshen mako Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ya fayyace ayyukan da gwamnatinsa ke yi da kuma rikice-rikicen da Jam’iyyar APC ke ciki a jihar. Wane mataki za ka dauka domin ganin ka samu nasara a zaben 2019? Kamar yadda a shekarar 2015 Allah Ya yi ikonSa Ya ba […]
Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar
A tatttaunawa da manema labarai a karshen mako Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar ya fayyace ayyukan da gwamnatinsa ke yi da kuma rikice-rikicen da Jam’iyyar APC ke ciki a jihar.
Wane mataki za ka dauka domin ganin ka samu nasara a zaben 2019?
Kamar yadda a shekarar 2015 Allah Ya yi ikonSa Ya ba ni mulkin Jihar Bauchi, haka yanzu ma muke kyautata zato wajen Allah. Shi zai ba mu mulki Ya kuma bai wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari mulkin Najeriya a 2019 tare da goyon bayan jama’ar Bauchi da kuma al’ummar Najeriya,
Ya kamata mutane su fahimci yadda al’amura suke da yadda suke gudana, ta haka ne za su fahimci cewa muna yin abubuwan da suka kamata ko ba ma yi. Misali ka dauki batun tsarin albashin ma’aikata na Jihar Bauchi, muna da ma’aikata dubu 105, da suke aikin gwamnati a jihar kuma ake biyan su albashi, sannan kudin da ake biya a matsayin albashi kowane wata ya kai Naira biliyan biyar da miliyan 700. Mafi yawan kudaden nan daga Abuja ake samo su. A watannin baya, idan muka tafi Abuja, ba ma samun kudaden da za mu iya biyan albashi, to amma Allah Yana taimakonmu muna biyan albashi kowane wata a jihar. Wannan matsala ta sa na gagara tabo wasu daga cikin ayyukan da muka kudiri niyyar yi don ciyar da al’ummar Jihar Bauchi gaba.
A cikin shekara uku da Jam’iyyar APC ta yi tana jan ragamar mulki a jihar irin nasarorin da muka samu sun fi nasarorin da gwamnatin PDP ta samu a shekara 16 da ta yi muhimmanci ga al’umma. Duk wanda yake zaune a jihar nan zai tabbatar maka da wannan magana da na yi. Na kuma gode wa Allah da Ya sa muke zaune lafiya a Jihar Bauchi. Ina kuma zaune da sarakunan gargajiya lafiya, kuma cikin ikon Allah mun yi ayyuka daidai gwargwado don kyautata rayuwar al’umma, a bangaren ilimi da lafiya da tattalin arziki da gina kasa da gina al’umma. Ina gina hanyoyi da yawa a Bauchi. Ku tafi garin Jama’are da Itas/Gadau da Giyade da Toro da Dass da Ganjuwa da Bauchi, za su fada muku haka.
Ba ka tunanin rikice-rikicen cikin gida da na waje za su iya kawo muku matsala?
Kwata-kwata wannan ba shi ne abin da yake cikin zuciyata ba, ina so in gaya muku cewa, cece-ku-ce wani suna ne na biyu da ake ambaton siyasa da shi. Ai dama ita siyasa cike take da rashin jituwa da kuma sulhuntawa. To sai dai kuma rashin jituwa ko kuma akasin haka ba shi ne ba, abin da zai sa ka kai ga nasara wajen kyautata wa jama’a shi ne abin dubawa. Ina ganin cewa matakin da na dauka shi ne yi wa Jihar Bauchi aiki tukuru, muna kan hanya, kuma ba ma shakka. Ka ga lokacin da na lashe zaben fid-da gwani na Jam’iyyar APC abin da ya zo cikin zuciyata shi ne godiya ga Allah, saboda ni mutum ne wanda ya yi imani da Allah, domin kuwa Shi ne Yake tafiyar da lamurana. Yaya za ka magance matsalar cikin gida a Jam’iyyar APC ta Bauchi?
A lokacin da na lashe zaben fid-da-gwani a shekarar 2015, na ziyarci dukan ’yan takara a gidajensu domin neman goyon bayansu a lokacin babban zabe, wadansu sun amince wadansu suka ki amincewa. Dokta Ibrahim Yakubu Lame yana daya daga cikinsu, na ziyarce shi sau biyu, ziyara ta farko ya ce mini zai duba bukatata, daga bisani ya gayyace ni domin in gana da tawagar yakin neman zabensa, na kuma gana da su inda muka kulla yarjejeniya wadda a yau shugaban riko na Karamar Hukumar Giyade, wanda Daraktan yakin neman zaben Ibrahim Yakubu Lame shi ne Kwamishinan Watsa Labarai a halin yanzu, haka kuma jakadan Najeriya a kasar Switzerland shi ma ni na ba da sunansa. Haka kuma wani daraktan yakin neman zabe ta fuskar fadakarwa da tsare-tsare na Ibrahim Lame, Kwamared Sabo Mohammed shi ne mai tallafa min na musamman a bangaren ilimi da wayar da kan al’umma, Sai wani daraktan kuma, Chindo Abdu shi ne Shugaban riko na Karamar Hukumar Bauchi a halin yanzu. Na kuma nuna kyakkyawan halin dattako da girmamawa da sanin ya kamata ga dukan wadanda Allah Ya hada mu tafiya tare, kuma shi ne abin da zan yi a wannan karo ma. Wani batun shi ne an dauki tsawon lokaci wadansu na ganin kamar ana zaman rashin fahimta da ’yan Majalisar Tarayya da ni, mutane da dama suna ta yayata labarai marasa dadi a kaina, a yayin da muka fara mulki, a cikin ’yan Majalisar Tarayya, uku ne kacal daga cikinsu suke tare da ni, amma kuma a yau guda tara daga cikinsu suke tare da ni, don haka ina ganin ai wannan wata gagarumar nasara ce wadda ta samo asali sakamakon gagarumin mataki da muka dauka.
Wace rawa kake ganin ’yan jarida za su taka a gwamnatinka?
Ya kamata kafofin watsa labarai su rika tafiyar da ayyukansu yadda ya kamata, kuma ban ce wani ya rika mara mini baya ba, haka nan idan wani ya ce babu abin da ake yi a Jihar Bauchi, a matsayinku na ’yan jarida ba na tsammani za ku soki lamirin wannan mutum. Abin da nake so ku yi shi ne ku zagaya, ku kuma bincika shin aiki yana tafiya ko a’a, haka kuma hakkinku ne ku rubuta labarai a kan abubuwan da kuka gani da idonku.
Ana zargin cewa an yi amfani da shaidar zama dan jam’iyya na bogi wajen zaben fid-da-gwani, me za ka ce game da haka?
Ban san komai ba dangane da wannan magana. Da farko dai ba ni ne na gudanar da wannan zabe ba, makukar kana bibiyar lamarin, za ka fahimci cewa lokacin da kwamitin shirya zabe na jiha ya yi taro, ina kasar China tare da Shugaban Kasa. Sun dauki mataki ne wanda tsarin Uwar Jam’iyyar ya gindaya, inda suka nuna cewa suna so a gudanar da zabe ta amfani da wakilai, sai kuma aka gudanar da zaben ’yar tinke, amma suna kokawa. Haka kuma hedkwatar jam’iyya ta turo wani kwamiti mai karfi wanda ya kunshi farfesoshi guda biyu a matsayin shugaba da sakatare da kuma manyan mutane a matsayin mambobi, sun kuma gabatar da dukan tambayoyinsu, an kuma ba su amsoshin da suke bukata game da korafe-korafe da suke yi, sun kuma amince tare da gamsuwa da shirye-shiryen kwamitin.