Burina in shahara sosai a harkar fim – Nafi’u Gwammaja

Bashir Rijau ya kasance mai shiryawa da ba da umurni a fina-finan Hausa. A kwanakin baya ya fitar da wani kayataccen fim dinsa mai suna Sarki Jatau. Ya tsamo labarin fim din ne daga shahararren littafin nan na Magana Jari Ce na marigayi Dokta Abubakar Imam. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya bayyana yadda fim din […]

Burina in shahara sosai a harkar fim – Nafi’u Gwammaja
Burina in shahara sosai a harkar fim – Nafi’u Gwammaja

Bashir Rijau ya kasance mai shiryawa da ba da umurni a fina-finan Hausa. A kwanakin baya ya fitar da wani kayataccen fim dinsa mai suna Sarki Jatau. Ya tsamo labarin fim din ne daga shahararren littafin nan na Magana Jari Ce na marigayi Dokta Abubakar Imam. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya bayyana yadda fim din ya dauki hankalin al’umma, musamman yadda fim din ya fitar da al’adun gargajiyar Malam Bahaushe. Ga yadda ganawar ta kasance:

Za mu fara da takaitaccen tarihinka.

Sunana Nafi’u Shua’ibu Ibrahim Gwammaja, wanda a baya ake kirana da Magambo, amma saboda ina girma sai na hana wannan sunan saboda an sa mini shi ne tun ina firamare wato a 1990. Na yi firamare a Gwammaja, na yi karamar sakandare a Gwammaja, sannan na kammala a Technical da ke Nasarawa, a Jihar Kano a shekarar 1999.
Yaushe ka fara harkar fim, kuma me ya ja hankalinka ka shiga wannan harkar?
Na shiga harkar fim tun a 1997, abin da ya sa na shiga harkar fim shi ne, daga farko ina yin wata harka ce daban, sai harkar ta karye, daga nan ne na ga wadansu ’yan unguwarmu a harkar, sai na shiga, inda na fara aiki a wani fim mai suna ‘Kainuwa’ fim din kamfanin Sarauniya Film Production ne, kamfanin ne ya yi fim din ‘Allura Da Zare.’ Fim din da aka fara sa ni shi ne ‘Kainuwa’ sai ‘Rintsi,’ na yi ‘Zarge’ da ‘Sangaya’ da ‘Nagari’ da ‘Sartse’ da Garwashi’ da sauransu. Daga nan na koma Usmaniyya Film Production, kamfanin Misbahu M. Ahmad ke nan, muka yi ‘Kansakali’ da sauransu. Daga baya Aminu Saira ya ja ni a jikinsa, muka koma Saira Mobies, inda muka fara da ‘Musnadi’ da ‘Jamila Da Jamilu’ da ‘Garinmu Da Zafi’ da duk fina-finan da Saira ya yi tare da ni ya yi su.
A cikin wadannan fina-finan da ka ambata wanne ne ya fi burge ka?
Ai ban ambaci fim din da ya fi burge ni duk a cikin wadanda na ambata ba, fim din da aka ba ni gurbin da ba a taba ba ni ba shi ne ‘Uwar Gulma.’ Na fito a dan daba, mai shaye-shaye da bangar siyasa, an ba ni gurbin da nake so.
Me ya sa aka sanya maka lakabin Magambo?
An sama mini lakabin Magambo ne saboda wata rana muna firamare, idan an bugi ’yan ajinmu sai in je in rama musu, to wata rana an bugi wani yaro sai na je na rama masa. A yayin dukan sai na yanke shi da kusa, sai aka zo gaban asambili, sai malamin yake duka na, sai ya ce ‘kai ga Magambo, idan an bugi ’yan ajinku sai ka je ka rama musu ko?’ Hakan kuma ya faru ne lokacin da fim din Magambo mai suna ‘Mr India’ ya fito. Malamin ya yi mini bulala, bayan an tashi asambili shi ke nan dalibai suka fara ihu suna cewa Magambo, Magambo. Tun ba na so, ina duka, wani lokaci in kai kara, har ya zama babu yadda zan yi, aka ci gaba da kirana Magambo. Ka san idan ka girma ka yi aure da kuma ’ya’ya, ya kamata a ce ka hana duk wani lakabi marar amfani, shi ne na hana.
Ba ka gani gurbin dan daba da aka ba ka a fim din ‘Uwar Gulma’ ba zai sake dawo maka da lakabin ba?
Ba zai dawo mini da shi ba, duk da cewa ina son gurbin da zan yi rashin mutunci, saboda na riga na hana sunan, don haka ko an zo rubuta sunayen jarumai ko ma’aikata a fim ba a sa sunana da inkiyar Magambo, sai dai a sa Nafi’u Gwammaja. Duk wanda ya kira ni da Magambo to ya san ni tun a shekarun baya.
Ga shi ka dade a harkar fim amma me ya hana har yanzu ba ka taba fitowa a matsayin babban jarumi ba?
A lokacin da na shiga harkar ba na shiga ba ne da burin in zama jarumi, ba ni da sha’awar zama jarumi sai dai idan za a yi wata fitowa babu kowa sai in shiga. Misali, kamar gurbin dan sanda ko likita ko kuma a ce babu wanda zai yi maigadi, sai in fito. Amma ban taba jin ina sha’awar fitowa babban jarumi ba, sai lokacin da Halima Atete da Darakta Alolo suka ce zan iya taka gurbin dan daba. Bayan an ba ni gurbin a fim din ‘Uwar Gulma’ ne na ji dadinsa, sai na fara sha’awar in zama jarumi.
Wadanne matsaloli ka fuskanta a harkar?
Farkon shigowa ta harkar ne na fuskanci matsala, Hauwa Ali Dodo, Allah Ya ji kanta, ita ce ta share mini fage na shiga harkar fim. ’Yan unguwarmu kin dauka ta suka yi, sai bayan Hauwa Ali Dodo ta ce ni kaninta ne kafin aka karbe ni. Bayan nan ban fuskanci wata matsala ba. Yin fim yana sa ni nishadi da jin dadi.
Wadanne nasarori ka samu a harkar fim?
Harkar fim ta yi mini komai, a cikin fim na yi aure, na haifi ’ya’ya biyu, nake daukar nauyinsu. Da fim nake taimaka wa iyayena da ’yan uwana. Ta dalilin fim na yi mota. Zan iya cewa duk wani muhimmin abu da na samu a rayuwa, na same shi ta dalilin harkar fim ne.
Wane buri kake da shi a cikin wannan harka?
Burina in yi suna fiye da Ali Nuhu. Ina sha’awar harkar, zan iya cewa yanzu na fara, don haka ina so in shahara fiye da Ali Nuhu. Na je neman biza zuwa Amurka har yanzu da nake magana da kai ba a ba ni ba, amma na tabbata da na yi suna kamar Ali Nuhu da yanzu an ba ni,
Ka tabbata Ali Nuhu ba ya fuskantar matsala wajen neman biza?
Ba ya fuskantar wata matsala, duk lokacin da zai fita waje, idan aka duba sunansa a intanet, za a ga babban jarumi ne a duniyar fina-finan Najeriya da Afirka, don haka ba zai yi asarar fuskarsa ba, fuskarsa ba za ta bari idan ya je wata kasa ya aikata abin assha ba, don haka ba za su yi dari-dari da shi ba, sai ka ga sun ba shi biza.
Yaya kake ganin harkar fim a nan gaba?
Harkar fim a nan gaba za ta samu daukakar da ba a taba tsammani ba saboda kullum kyakkyawan canji ake samu a harkar, akwai wani fim mai suna ‘Salma’ an yi amfani da kayan aikin daukar fim da ba a taba amfani da shi a harkar ba. Wata kyamara za a harba sama, inda za ta rika dauko fitowar da ake yi daga sama, wannan abin ai ka ga ci gaba ne, da babu shi. A da da karamar kyamara ake daukar fim, aka dawo bHS, aka dawo Betacam, aka dawo amfani da Z7, yanzu kuma da Canoon, an ci gaba sosai. A da daukar fim ake ba tare da bambance sauti ba, amma yanzu daban yake, daga kan fim din ‘Jamila Da Jamilu’ aka fara kawo sauti daban. Da na yi harkar tufafi, haya muke zuwa mu karbo ko aro, amma yanzu kasafi za ka yi don tufafi, sannan ta bangaren abinci, idan ana lokeshin zuwa ake a sayo, amma yanzu kudi na musamman ake warewa don a dafa. Idan ka dauki bangaren biyan mutane ba kamar da ba ne, lokacin da na yi fim din ‘Allura Da Zare, Naira 900 aka ba ni. Don haka ci gaba za a rika samu.