Burina in taimaka wa mata da matasa – Salamatu Wambai
Salamatu Wambai Aliyu Zambuk (Mama Salamatu) Alkyabbar Kwadom, Gimbiyar Progress FM Gombe, Sarauniyar Amana Rediyo, bwararriyar ’yar jarida ce da ta zama ’yar siyasa. Ta yi aiki da gidajen rediyo hudu a Jihar Gombe, yanzu kuma ’yar takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Gombe ce a barbashin Jam’iyyar PDM daga mazabar Yamaltu ta Yamma a Baramar […]
Salamatu Wambai Aliyu Zambuk (Mama Salamatu) Alkyabbar Kwadom, Gimbiyar Progress FM Gombe, Sarauniyar Amana Rediyo, bwararriyar ’yar jarida ce da ta zama ’yar siyasa. Ta yi aiki da gidajen rediyo hudu a Jihar Gombe, yanzu kuma ’yar takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Gombe ce a barbashin Jam’iyyar PDM daga mazabar Yamaltu ta Yamma a Baramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe. A zantawar ta da Aminiya ta bayyana tarihin rayuwarta da gwagwarmayar da ta sha kawo yanzu:
Tarihin rayuwa:
Sunana Salamatu Wambai Aliyu Zambuk da aka fi sani da Mama Salamatu. Ni ce Alkyabbar Kwadom. An haife ni a Birin Fulani da ke Baramar Hukumar Funakaye a Jihar Gombe a ranar 21 ga Mayun,1977. Na girma a garin Bajoga. A can na yi firamare ta Central da ke Bajoga. Daga nan na tafi Sakandaren ’Yan mata ta Gwamnati (GGSS), Bagoja na gama a 1995 sai aka yi mini aure a 1996. Bayan wasu shekaru da yin aure wato a 2009 sai na tafi Kwalejin Koyon Aikin Shari’a ta Misau a Jihar Bauchi (Collage of Legal and Islamic Studies) inda na yi Difloma a bangaren aikin jarida wato Mass Communcation na gama a 2011, sai na sake yin Satifiket a bangaren kwamfuta.
Ayyuka:
Na fara aiki ne da gidan Rediyon Jihar Gombe a shekarar 2005 a matsayin mai gabatar da shirye-shirye har zuwa shekara ta 2015, sai na bar su na koma Ray Power FM na yi shekara daya da wata biyar, su ma na bar su na koma Progress FM tashar ’yanci da ci gaban al’umma su ma na yi shekara daya da wata biyu na bar su na sake komawa Amana Rediyo FM har zuwa yanzu. Daga nan na ajiye aiki don yin takarar kujerar Majalisar Dokokin Jiha a barbashin Jam’iyyar PDM a mazabar Yamaltu ta Yamma daga Baramar Hukumar Yamaltu Deba.
Nasarori:
Nasara kan akwai domin na sanu sosai a Gombe saboda aikin rediyo da na yi kowa ya san Mama Salamatu kuma duk wajen da na yi aiki ni nake ajiyewa da kaina in canja waje ba kora ta ake yi ba kuma ana rabuwa ne cikin mutunci. Sannan na hadu da manyan mutane wadanda idan ba don aikin jarida ba ban isa in yi hulda da wadansu ba saboda matsayinsu, wannan sanayyar ce ma ta sa na ajiye aiki na kama harkar siyasa.
Balubale:
Kowane abu yana tattare da irin nasa balubalen, sai dai ni ban dauke shi a matsayin balubale ba saboda idan mutum ba ya fuskantar balubale a kowane irin abu to ba kasafai yake samun ci gaba ba. Don komai ne zai riba zuwa a bagas ba, ba tare da an sha wahala ba.
Burina a rayuwa:
Burina shi ne in ga ina taimaka wa mata da matasa wanda hakan ne ma ya sa na shiga harkar siyasa don idan na samu nasarar kasancewa ’yar majalisar jiha to hakan zai ba ni damar taimaka wa al’umma musamman mata da matasa.
Tufafi:
Na fi sha’awar atamfa in dinka zane da riga da gyale saboda shi ne shiga irin ta kamala ta ’yan Arewa kuma duk wanda ya gan ki ba zai ce ba ki yi shigar mutunci ba.
Bungiyoyi:
Ina cikin bungiyoyi na mata dadan-daban. Na taba zama sakatariya a Amada Women Famers wato bungiyar mata manoma ta Amada. Sannan mamba a bungiyar Fadama II, mamba a bungiyar Food Security sannan na ribe mubamai da dama.
Basashen da na ziyarta:
Ban taba zuwa wata basa a duniya ba, amma a jihohi 36 na Najeriya kadan ne jihohin da ban leba ba.
Lambar yabo:
Na taba samun lambar yabo da wata bungiyar dalibai ta sakandaren al’umma ta Shehu Abubakar da ke Bolari a fadar jihar ta Hausa Fasaha ta ba ni.
Yawan iyali:
Alhamdulillahi na haifi ’ya’ya shida, uku maza, uku mata amma daya ya rasu saura biyar.
Shawara ga iyaye:
Ina mai ba iyaye shawara su kula da tarbiyyar ’ya’yansu musamman wajen ba su ilimin addini da na zamani da za su taimaka musu wajen gudanar da rayuwarsu. Domin rashin ilimi a wajen ’ya mace ba baramar illa ba ne. Sannan ina bara shawartar iyaye su guji dora wa ’ya’yansu musamman mata talla domin talla na lalata tarbiyyar yara. Wadansu iyayen na fifita ilimi ’ya’ya maza a kan na mata wanda kuma matan su suka fi tausayi da taimaka wa iyaye. Don haka a matsayina na mace ina cewa ilimin mace abin nema ne, idan aka ilimantar da mace tamkar an ilimantar da al’umma ce, amma namiji tamkar mutum daya aka ilimantar.