Burina in taimaka wa mata da yara – Hajiya Rakiya Jibrin

Hajiya Rakiya Jibrin ita ce Shugabar kungiyar Matan Musulmi ta kasa (FOMWAN) reshen Jihar Nasarawa kuma Babbar Darakta ce a Ma’aikatar Manyan Makarantun Jihar Nasarawa.  A tattaunawarta da wakilinmu ta shawarci mata game da muhimmancin ilimi da sauransu.  Ga yadda hirar ta kasance: Tarihin rayuwata:Sunana Hajiya Rakiya Jibrin Ali, kodayake ni daga nan Jihar Nasarawa […]

Burina in taimaka wa mata da yara – Hajiya Rakiya Jibrin
Burina in taimaka wa mata da yara – Hajiya Rakiya Jibrin

Hajiya Rakiya Jibrin ita ce Shugabar kungiyar Matan Musulmi ta kasa (FOMWAN) reshen Jihar Nasarawa kuma Babbar Darakta ce a Ma’aikatar Manyan Makarantun Jihar Nasarawa.  A tattaunawarta da wakilinmu ta shawarci mata game da muhimmancin ilimi da sauransu.  Ga yadda hirar ta kasance:

Tarihin rayuwata:
Sunana Hajiya Rakiya Jibrin Ali, kodayake ni daga nan Jihar Nasarawa ne amma an haife ni ne a wani gari da ake kira Riruwai a Jihar Kano a shekarar 1960. Ina da aure da ‘ya’ya 2 wato A’ishatu Jibrin da Usman Jibrin. Na yi karatun firamare dina a Shekara Girls Boarding Primary School a Kano. Daga nan na cigaba a Kwalejin ilimi na mata  a Kano. Daga nan na cigaba da karatuna a Gumel Adbanced Teachers College Kano. Na kuma cigaba a Jami’ar Bayero da ke Kano a shekarar 1990 inda na samu digiri dina a fannin karatun Islama.

AIKI NA:
Bayan wannan kafin da kuma lokacin da na fara aiki na kuma samu horo a wasu cibiyoyi da dama da suka hada da ANCOPSS National Conference daga shekarar 1997 zuwa 2008 da Mandatory ANCOPSS Zonal Workshop for Principals da Joint Consultatibe Committee on Education reference and Plenary meetings da National Council on Education Meeting da dai sauransu. Na fara aiki ne a matsayin shugabar makarantar sakandaren gwamnati da ke Maina a garin Lafiya. Daganan sai aka koma dani makarantan sakandaren gwamnati dake Akurba a matsayin shugaban makarantan inda na ke daga shekarar 1997 zuwa 2000. Daga nan aka sake komawa da ni makarantar sakandaren gwamnati da ke Nasarawa Eggon inda bayan wasu lokuta aka sake turo ni zuwa makarantar sakandaren gwamnati dake Bukan-sidi a Lafiya. Sai kuma sakandaren gwamnati dake Doma. Daga nan sai aka koma da ni ofishin ma’aikatar ilimi dake Assakio inda na yi aiki a matsayin mai kula da harkokin ilimi a yankin (chief inspectorate officer) kenan a Turance. Daga nan bayan wasu lokuta sai aka kawo ni ma’aikatar manyan makarantu dake karkashin ma’aikatar ilimi na jihar nan inda nake rike da mukamin babban daraktan ma’aikatar. Ka ji wasu daga cikin mukamai da na rike  a bangaren aiki kuma kamar yadda na bayyana maka galibinsu a bangaren ilimi ne.

kUNGIYOYI DA NAKE CIKI:
Ina cikin kungiyoyi da dama musamman na mata kuma wanda nake alfahari da shi sosai shi ne namu na matan Musulmi da aka fi sani da  FOMWAN. Ni asalin memban kungiyar ce ta kasa. A nan Jihar Nasarawa kuma bayan na kasance memban kungiyar na lokaci mai tsawo na kuma rike mukamin mataimakin shugabar kungiyar na wasu shekaru kafin daga bisani aka gudanar da zabe na tsaya takara na samu nasara inda na zama shugabar kungiyar a jihar nan. Matsayin da nake rike da shi kenan har yanzu. Ita dai wannan kungiya kamar yadda ka sani daga cikin ayyuka da muke yi sun hada da tabbatar da cewa matan Musulmi sun samu ilimin addinin Musulunci da na zamani don rayuwarsu ya inganta. Kuma ka san sai da ilimi mace za ta iya shawo kan kalubalen dake gabanta a matsayinta na uwa da kuma matar aure. Muna kuma taimakawa mata da yara har ma da wadanda ba musulmi ba musamman ta hanyan tuttubar gwamnati dangane da bukatar a rika taimaka musu musamman marasa galihu da nakassassu cikinsu. Muna kuma shirya wa’azi a lokuta-lokuta inda muke wa matan musulmi wa’azi da sauransu don karfafa imaninsu. Ka ji kadan daga cikin ayyukanmu a wannan kungiyar FOMWAN a jihar nan da nake shugabancinta a halin yanzu.

Halayen da na koya a wajen iyayena:
A gaskiya iyayena sai dai in cigaba da yi musu addu’a Allah Ya saka musu da alheri musamman mahaifina Alhaji Abdullahi Zakari. Ya kasance malami ne kuma akoyaushe yakan shawarce ni  in kasance mai wadatar zuci wato kada in rika sa ido a kayan wani.   In rika neman na kaina, in kuma rika godewa Allah akan duk abinda ya faru da ni a rayuwa. Ya kuma taimaka sosai wajen tabbatar na samu ingantaccen ilimi da zan iya cewa yau na zama abinda na zama sakomakon gudumawarsa ne. A takaice dai na koyi kyakkyawan tarbiyya da halaye

masu kyau a lokacin da nake tare da iyayena musamman daga wurin mahaifina.

Abin da nake so a tuna da ni:
Ni dai zan so a tuna da ni a matsayin wanda ta taimakawa jama’a musamman mata wajen magance kalubalen rayuwa. Don burina na kenan kullum in ga ina taimakawa mata da yara wajen tabbatar sun magance matsalolin rayuwa. Saboda haka idan da wani abu da zan so a tuna da ni shi ne wacce ta taimakawa mata da yara wajen cimma burin rayuwarsu.

Shawarata ga mata:
Shawarata ga mata ‘yan uwana sh ine a nemi ilimin addini da na zamani musamman na addini don sai kin samu ilimin addini kafin ki san mahimmancin samun na zamani. Idan mace tana da ilimi ba shakka za ta taimakawa maigidanta a hanyoyi da dama. Kuma ita kamar malama ce ga ‘ya’yanta saboda haka dole ne ta nemi ilimi kafin ta iya koyawa yaranta kyawawan tarbiyya. Kadan daga cikin shawarwari da nake da shi ga mata ‘yan uwana kenan. Nagode.