Burina in taimaki al’umma –Dokta Larai Aliyu

Dokta Larai Aliyu Likita ce da ta yi suna a Jihar Sakkwato wajen taimakon al’umma musamman mata don ana kallonta ne a matsayin mace likita da ta fi sanin ciwon mata da hanyoyin magance su har ana yi mata hasashen da wuya ta bayar da magani ba a samu sauki ba.  Aminiya ta samu tattaunawa […]

Burina in taimaki al’umma –Dokta Larai Aliyu
Burina in taimaki al’umma –Dokta Larai Aliyu

Dokta Larai Aliyu Likita ce da ta yi suna a Jihar Sakkwato wajen taimakon al’umma musamman mata don ana kallonta ne a matsayin mace likita da ta fi sanin ciwon mata da hanyoyin magance su har ana yi mata hasashen da wuya ta bayar da magani ba a samu sauki ba.  Aminiya ta samu tattaunawa da ita kuma sun tabo batutuwa da dama.  Ga yadda hirar ta kasance:

Tarihinta:
Assalamu Alaikum. Sunana  Dakta Larai Aliyu Tambuwal.   An haife ni a garin Tambuwal a shekara ta 1971.   Na yi karatun fiiramare a karamar makaranta ta cikin garin Tambuwal bayan na kare a 1983 sai na koma Sakkwato inda mahaifiyata take zaune tana aiki inda na yi sakandare a Kwalejin ’yan mata ta Nana.   Ina aji na biyu ne aka kirkiro karatun ilmin kimiyya karkashin hukumar kula da ilmin kimiya ta jiha sai aka zabe mu, mu biyar daga wannan makarantar da wasu daga Bodinga da Rabah da Tambuwal inda muka kai 36 amma kuma mu biyar kawai muka ci jarabawar yin karatun kimiyya a makarantar.   Haka aka yi har na kammala sakandare  amma saboda na fadi darasi daya da ya shafi karatun kimiyya ban samu tafiya katratun Jami’a kai tsaye ba.   A lokacin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU) na so na je don in yi karatun kimiyya amma saboda na fadi a darasin kimiyya ta sa tilas na tafi Jami’ar Usmanu danfodiyo don in gyara jarrabawata. Zariya nake son in yi karatu shi ya hana ni farawa don danfodiyo suna bayar da damar a gyara jarrabawar  kan haka sai tafi can na yi gyara, bayan na samu amincewar iyayena da kyar don wasu na ganin bai dace na bar nan ba don yin karatu. A hakan na fara karatun gyaran jarabawa bayan na samu nasara ne na rubuta takardar neman gurbin karatu kuma na samu aka dauke ni  amman  ban samu takardar shedar an dauke ni ba sai sauran sati biyu a rufe biyan kudin makaranta sai na koma gida saboda ba zan iya bhiyan kudin a wannan lokaci ba.   Ana bukatar na biya Naira 900 don sai na biya ne zan fara karatun. A lokacin iyayena talakawa ne ba su da kudin.  Albashin da mahaifiyata ke karba bai wuce Naira 500 ba yayin da ni kuma nake karbar alawus din Naira 370  a aikin wucin gadin da nake yi a ma’aikatar kiwon lafiya da takardar sakandare. Hakan ya sa na yi ta tunanin yadda zan bullowa lamarin  can sai na tuna ina bin gwamnatin Sakkwato bashin kimanin Naira dubu 1200 na kyautar da aka ce za a ba ni  a matsayin daliba mafi hazaka.   Duk an fada a kafafen yada labarai cewa ni na lashe wannan kyauta amma abin bai zo hannuna ba, kawai sai na je na yi bayani aka dauko rekod  aka duba sai aka biyani, da su ne na biya kudin makaranta a Zariya.
Bayan wata shida da fara karatuna  na dawo gida hutu sai na tarar gwamnati na sanarwar cewa duk dan asalin jiha mai son zuwa karatun lafiya a kasashen waje to ya kawo takardunsa. Nan da nan na aika nawa takardun inda na samun nasarar kasancewa mutane 20 daga cikin wadanda suka samu wannan tallafi aka tura mu zuwa Bulgariya.  Mata uku maza 17 amma biyu daga cikin matan ba su je ba wai in sun tafi lalacewa za su yi. Ni kam na tafi inda na share kimanin shekara bakwai zuwa takwas na kammala na  dawo na fara aiki da asibitin Maryam Abacha dake Sakkwato. Bayan na koma asibitin koyarwa na Usman danfodiyo na yi  digirina na biyu kan lafiyar al’umma kuma gwamnati ta dauki nauyina na yi wasu kwasa-kwasai da  dama kan lafiyar mata da al’umma da sauran cututtuka daban- daban.   Yanzu haka akwai wanda nake yi ban kammala ba amma ina shekarar karshe ce. Yanzu kuma ina aiki  da hukumar lafiya ta duniya inda ake tura ni garuruwa don  kula da lafiyar jama’a  kuma ana ba ni kananan hukumomi biyu inda nake yin wata shida ina kula da su.
kalubalen da ta fuskanta:
Ina shekara ta uku cikin karatuna na dawo gida Nijeriya na yi aure.  Bayan na koma duk shekara sai na dawo Sakkwato na kwana 30 na koma, na yi fama da juna biyu a can ga shi ba na kusa da gid.  Maigidana ya same ni a Bulgariya lokacin da na haihu.   Bayan an yi suna ne sai ya dawo na cigaba da kulawa da ita.  Hankalina ya rabu biyui, ga karatun da nake yi sannan ga kula da jaririya. Bayan wata tara ne na kammala karatuna  na dawo gida.
Yawan iyali:
Ina da ‘ya’ya biyar, maza biyu mata uku.
kasashen da ta ziyarta:
Kamar yadda na fada maka na ziyarci  kusan dukkan jihohin da ke kasar nan.  A waje kuwa na ziyarci kasashen da suka hada da Bulgariya da Turkiyya da Romaniya da Ingila da Tailand da Bankok inda a can ne ma na gabatar da takarda a  kan ciwon daji.
Macen da take koyi da ita:
Baya ga mahaifiyta da ta yi kokari wajen ba ni tarbiyya da kula da ni wajen samun ilimi, akwai shugabar makaranta ta J T Usman,’ yar Zuru ce inda ta kasance jagorata.   Ta so ni inda ta kula da ni a makarata ita da mataimakiyarta.   Wadannan matan su suka azani akan tubalin da na gina rayuwata.  Sannan Hajiya Fatima Bunza ita ce mace ta farko da na sani a matsayin likita, ina ganin yadda take karatu da tafiyar da rayuwarta cikin tsari ina koyi da ita.
Abin da ba za ta manta da shi ba:
Gwagwarmayar da na sha kafin na kawo wannan matsayi, gaskiya ba zan manta da shi ba.  
Sha’awa a rayuwa:
Karatun littafai da kula da ’ya’ya inda wasu ke mamakin yadda na kasance likita kuma ina da yara biyar.   To ina son yara sosai, mu yi hira da hulda don na koyar da su dabi’una kuma ina son tafiye-tafiye in shiga mutane a yi da ni.
Da mi kike son a tuna dake a rayuwa:
Ina son a tuna da ni a matsayin mace hazika mai son taimakawa al’ummarta kuma mai tsoron Allah dake kwatantawa a rayuwa  da tausayi.   Mai son ci gaban kanta da jama’a musamman ’ya’yanmu ’yan asalin Sakkwato su samu ilmi.   Ina takaicin koma bayan da muke samu na ilmi duk da tallafin da ake samu mun kasa yin gogayya da wasu jihohi.
Kin gamsu da yawan matan da ke karatun likita a yanzu?
Gaskiya wannan matsala ce babba a Jihar Sakkwato.  Hasalima yanzu haka babu matan da suka karanta likita kimanin 20  a dukkan asibitocinmu.   Ni kaina da nake likita mace ban so idan  na je asibiti wani namiji ya duba ni ba sai dai mace ‘yar uwata.   Lokacin da nake Bulgariya namiji bai taba duba ni ba, sai in ya zama dole. Abin akwai nauyi a ce mace ta je wajen namiji likita tana bayyana mata sirrinta.  Gaskiya likitoci mata da jami’ an kiwon lafiya ba su ishe mu ba muna da karanci kan haka nake kalubantar yara mata su jajirce don kawar da wannan matsala duk da za su fuskanci kalubale kafin kai wa ga nasara da taimakon Allah da iyaye. Akwai masu tunanin ’ya’yansu ba za su yi karatun likita ba don dadewa kafin a kare karatun to su sani fa dole ne su kawo matan su ko ’ya’yansu a duba su a asibiti, kenan in babu mata, maza ne za su duba su, ko kuna so ko ba kwa so.   Ka ga a nan zabi ya rage gareku, ko dai ku bar ’ya’yanku mata su yi karatun likita inda za a karu da su, ko kuma ta kasance maza su cigaba da duba su.  
Shawara ga mata:
Ana yi mana kallon ba mu iyawa to ni na san mace tana iyawa ga duk abin da ta sanya gaba.   Iyaye musamman mata ku taimaka wa yaranku mata wajen yin ayyukan gwamnati nan ma za a samu cigaba.  Sannan ina kira ga mata su yi ilimin addini da na zamani sannan ku koyi sana’o’in hannu.
Abin da take yi lokacin hutu:
Kula da yara da ba su ilmi da zantawa da su don sanin matsalolinsu da farin cikinsu. Wani lokacin nakan kalli fim din Hausa ko na turawa ko wakoki ko karatun Kur’ani.
Sutura:
 Na fi son wando da atamfa da shadda da irin kayan Mali.