Burina in taimaki al’umma –Farfesa Fatima Sawa
Farfesa Fatima Sawa, tsohuwar Malamar Jami’a ce kuma kwararriya akan ilimin tsirrai (botany). Sannan tana daya daga cikin matan da suka yi fice a tsakanin matan shiyyar Arewa maso Gabas da ta yi fadi- tashi a harkar karatun boko har ta zama Farfesa. Yanzu haka ita ce Shugabar Kwalejin ilimin Koyar da Harkar Noman Lambu […]
Farfesa Fatima Sawa, tsohuwar Malamar Jami’a ce kuma kwararriya akan ilimin tsirrai (botany). Sannan tana daya daga cikin matan da suka yi fice a tsakanin matan shiyyar Arewa maso Gabas da ta yi fadi- tashi a harkar karatun boko har ta zama Farfesa. Yanzu haka ita ce Shugabar Kwalejin ilimin Koyar da Harkar Noman Lambu ta Dadin-Kowa Federal College of Horticulture da ke Gombe. A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana irin kalubalen da ta fuskanta a rayuwa da kuma irin nasarorin da ta samu kamar haka:
Tarihin Rayuwata:
Sunana Fatima Sawa. Ni ’yar asalin kabilar Tera ce (Bateriya) a garin Zambuk dake yankin karamar hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe. A garin Zambuk aka haife ni a shekarar 1963. Na shiga firamare ta Zambuk a shekarar 1969 zuwa 1975. Bayan na gama sai na tafi Sakandaren ’Yan Mata ta GGSS Bauchi a shekarar 1975 zuwa 1980. A shekarar 1981 na tafi Kwalejin BACAS (Bauchi Collage of Art and Science) inda na yi karatun share fagen shiga Jami’a watau IJMB inda na shekara biyu daga 1981 zuwa 1983. Bayan na gama sai na wuce Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria (ABU) a shekarar 1983 na gama a 1986 inda na karanci Ilimin Tsirrai wato botany a Digirin Farko sai na yi bautar kasa watau NYSC dina a 1986 zuwa 1987. Da na gama sai na samu aikin koyarwa a Jami’ar Abubakar Tafawa balewa dake garin Bauchi (ATBU) daga shekarar 1987 zuwa shekara ta 2007 a lokacin na zama Farfesa bayan shekara 20 ina koyarwa. A shekara ta 2015 kuma na zama Shugabar Kwalejin koyar da Ilimin Noman Lambu dake garin Dadin-kowa a Jihar Gombe (Federal Collage of Horticulture, Gombe State).
Aiki:
Bayan na kammala Jami’a na fara aiki ne a Jami’ar Abubakar Tafawa balewa dake garin Bauchi ATBU daga shekarar 1987 har zuwa 2007. Ayyukan na yi su ne a matsayin malamar Jami’a (Lecturer) tun daga karamar malama har na zama Farfesa a Jami’ar ATBU watau a tsakanin shekara 20 kafin daga bisa na zama Shugabar Kwalejin Ilimi ta koyar da Noman Lambu, Federal Collage of Horticulture dake garin dadin-Kowa a 2015 zuwa yanzu.
kalubalen da na fuskanta:
A gaskiya a duk tsawon lokacin da na yi ina koyarwa har zuwa yanzu ban fuskanci wani kalubale ba domin ni na ma fi jin dadin aiki da maza saboda ina samun kulawa ta musammam daga wajensu saboda koda lokacin da muka yi karatu mun samu tallafin karo karatu na Scholarship wanda koda iyayenka talakawa ne za ka yi karatu ba kamar yanzu da lokaci ya canja ba wanda idan iyayenka ba su da karfi ba zai yiwu mutum ya iya karatu ba.
Nasara:
Na samu nasara sosai domin a lokacin da nake aiki na samu tallafi daga wata kungiya ta Turawan Burtaniya (British Council) inda na samu horo (training) a can Birtaniya. Sannan na sake samun tallafin karatu daga Bankin Duniya da ya ba ni dama na samu Digiri na uku wato Phd a United Kindom, inda na yi shekara daya. A lokacin karatun ban samu matsala ba shi ya sa na gama akan lokaci har rubutana a can na yi sai da na komo Nijeriya ne na mika. Bayan nan kuma na sake samun dama na je horo a United Kindom inda a wajen aka koya mana hanyoyin dabarun noma a wata tsangaya ta International Agricultural Research Institute. Da na dawo Nijeriya na rike mukamai daban-daban a Jami’ar Abubakar Tafawa balewa har na zama Farfesa kafin a ba ni wannan matsayi na Shugabar Kwalejin Ilimin koyar da harkar Noman Lambu.
Abin da na so in zama a rayuwa:
Lokacin da nake karama na so in zama Likita ce amma bisa ga yanayin karatu sai na canja hanya domin har na samu damar tafiya Bulgeriya a shekara ta 1981 daga cikin mu 11 da aka zaba daga Jihar Bauchi ni kadai ce mace, sai iyayena suka ce babu yadda za a yi tafiya da maza goma sha daya ni kadai ce mace. Shi ya sa ban tafi Bulgeriya ba sai na tafi Jami’a na karanta fannin ilimin tsirrai amma ban yi da-na-sanin rashin samun tafiya Bulgeriya don na karanta fannin Likita ba.
Burina a rayuwa:
Burina a rayuwa bai wuce in taimaki al’umma ta ba kafin na mutu domin na riga na zama Farfesa wanda shi ne burin duk wani malamin Jami’a. Ina fata idan na gama wa’adi na a matsayin Shugabar Kwaleji zan koma jami’a in ci gaba da koyarwa.
Abin da ya fi burge ni a rayuwa:
Abunda ya fi burgeni a rayuwa shi ne in ga iyaye suna sa ’ya’yansu mata a makaranta don su samu ilimin zamani wanda zai ba su dama su dogara da kansu koda a gidan miji ne.
Abin da nake so a rika tunawa da ni a kai:
Ina so ko bayan ba ni da rai
a rika tunawa da ni a matsayin mace ta-gari mai taimakon al’umma musammam al’ummar karkarar mu saboda b ani da keta akan komai, ina son in ga mutane suna taimakon na kasa d asu.
Yawan iyali:
Maigidana ya rasu yanzu ba ni da aure amma ina da ’ya’ya uku, biyu mata daya namiji.
Hutu:
Idan ina hutu ba na zuwa ko’ina da ya wuce garin mu in zauna tare da al’umma ta a kauye, saboda na shaku da su amma wani lokaci na kan je kasashen waje don na dan huta a can.
Shawarata ga mata:
Mata iyayen mu ina mai baku shawara da komai runtsi a bar ‘ya mace ta shiga makarantar boko, ta samu ilimin zamani domin shi ne gishirin rayuwa. Idan mace ba ta yi ilimi ba, ko gidan aure za ta iya samun matsala saboda babu yadda za ta yi al’amuranta su tafi daidai da wacce ta yi karatu. Wasu na ganin ilimi shi ke sa mace yin tsafta da tarbiyya. Idan mace ta yi karatu tana iya amfanar duk zuriyarta da ribar wannan karatun. Sannan za ka ga tana tausayin iyaye fiye da da namiji. Don haka iyaye a bar mata su yi ilimin zamani. A kiyaye wajen dora musu talla saboda yana gurbata tarbiyya kwarai da gaske, domin a wurin talla ne ake saurin lalata tarbiyyar ‘ya mace a lokacin da take cudanya da kowanne irin da namiji, nagari da na banza. Saboda haka iyaye a kula domin wasu iyayen ma idan suka dorawa ‘yarsu talla sukan ba ta lasisi ne na lalacewa domin cewa suke yi kar ta yarda ta dawo musu da kwashe. Allah ya sauwake.