Burina in yi fina-fanai a Kannywood da Nollywood- Amina Adam
Wata matashiyar jaruma mai suna Amina Adam da ke zaune a Jihar Legas ta ce burinta a harkar fim ta yi fina-finai a Kannywood da kuma Nollywood.Amina wacce aka fi sani da Samira ’yar kimanin shekara 27 ta ce hakan ne a wata tattaunawa da Aminiya ta yi da ita, inda ta ce a shirye […]

Wata matashiyar jaruma mai suna Amina Adam da ke zaune a Jihar Legas ta ce burinta a harkar fim ta yi fina-finai a Kannywood da kuma Nollywood.
Amina wacce aka fi sani da Samira ’yar kimanin shekara 27 ta ce hakan ne a wata tattaunawa da Aminiya ta yi da ita, inda ta ce a shirye take ta amsa kiran kujigiyar fina-finan Hausa ta Kannywood ta da Nollywood a duk lokacin da suka neme ta.
Ta ce: “Gaskiya ina da sha’awar harkar fim kuma ina da burin da nake so na cim ma a harkar, babban abin da nake so na cim ma shi ne na samu daukaka, duniya ta san ni.”
Ta ci gaba da cewa “Shi ya sa a yanzu a shirye nake na amsa kiran duk wata kungiya ko wani kamfani na shirya fina-finai. Zan yi duk abin da zan iya wajen nuna kwarewata da kokarina da kuma fasahar da Allah Ya ba ni. Domin ina jin Turanci da Yarabanci da Hausa daidai gwargwado.”
Ta bayyana cewa babban abin da ya fi damun ta shi ne irin yadda mutane ke yi wa ’yan fim sharri suna bata musu suna. Saboda haka sai ta yi kira ga jama’a su nisanci yin kazafi da yada jita-jita a kan ’yan fim.
“Gaskiya irin yadda jama’a suke yada jita-jita don su bata wa ’yan fim suna shi ne yake damuna. Yau ka ji an ce wane ya yi kaza, gobe a ce wance ta yi kaza alhalin karya ne, shaci-fadi ne kawai. Mutum sai ya zauna a dakinsa ya karkiro karya ya dangana wa ’yan fim ai bai dace ba. Ya kamata mutane su daina yin haka. Su sani cewa ’yan fim mutane ne irin su za su iya yin kuskure. Kamata ya yi mutane su rika yi musu addu’ar fatan alheri a maimakon su rika bata su.” Inji ta.
Jarumar wacce ta taba fitowa a wani fim mai suna ‘Inkiya’ da aka shirya a Jihar Legas ta yaba da yadda aka tsara fim din da kuma darasin da yake koyarwa.
Ta bayyana cewa ta koyi darasi da dama ta kuma samu ilimi mai yawa a harkar fim tare da haduwa da jama’a iri-iri.
Sai dai ta nuna bakin cikinta ga irin yadda harkar fim din Hausa ke samun koma-baya a Kudancin Najeriya.