Burina in yi fina-finan da za su gyara rayuwar jama’a – Rukayya El-Bashir
Aminiya ta samu tattaunawa da wata fitacciyar jaruma a harkar fina-finan Hausa a Jihar Legas mai suna Rukayya El-Bashir wacce ake yi wa lakabi da Ruka inda ta yi karin haske dangane da dalilan da suka sa ta shiga harkar fim da kalubalen da take fuskanta da kuma nasarorin da ta samu.Za mu so ki […]

Aminiya ta samu tattaunawa da wata fitacciyar jaruma a harkar fina-finan Hausa a Jihar Legas mai suna Rukayya El-Bashir wacce ake yi wa lakabi da Ruka inda ta yi karin haske dangane da dalilan da suka sa ta shiga harkar fim da kalubalen da take fuskanta da kuma nasarorin da ta samu.
Za mu so ki gabatar da kanki?
Assalamu alaikum, da farko dai sunana Rukayya El-Bashir amma an fi sani na da Ruka. Shekarata 23 a duniya. An haife ni a unguwar Mu’azu da ke Jihar Kaduna. A Kaduna na yi makarantar firamare da sakandire. Mahaifina dan jihar Ogun ne amma mahaifiyata mutuniyar Birnin Zazzau a jihar Kaduna ce. Bayan da iyayena suka dawo Legas ni kuma a lokacin na kammala karatuna na sakandire sai na koma Legas.
Yaya aka yi kika shiga harkar fim?
Na shiga harkar fim tun shekarar 2007. Na fara da kamfanin Kurmi Entertaiment da kuma kamfanin Bege Entertaiment. Na fara gwaji ne da kamfanin Hafizun Bege. A lokacin da muka fara sai abin ya zama kamar a yi kamar ba za a yi ba. Daga baya sai muka hade da Alhaji Sabi’u Na Allah shi ya fara fitar da fim din da na yi na farko.
Me ya sa kika shiga harkar fim?
A gaskiya da farko dai ba don sha’awa ko neman kudi na shiga ba takura mini aka yi. A lokacin wadansu ne za su yi fim a Legas sai suka gayyace ni. Da na je na shiga sai na fara sha’awar abin. Daga baya sai na yanke shawarar tsunduma cikin harkar saboda ina so duniya ta san da ni kuma ya zamanto ina koyar da darasi ga jama’a.
A lokacin da kika fara fim wane matasayi aka ba ki?
Na fito ne a jaruma sauran kuma na fito a kawar jaruma. Na fito a fim din ‘Inkiya’ da ‘Zainaba’ da ‘Azabar Zuciya’ da sauran su. Na yi fina-finai da yawa. A cikin fina-finan da na yi na fi son fim din ‘Azabar Zuciya’. Saboda a cikinsa na fuskanci kalubale da yawa. A fim din akwai inda ake nuna yadda auren mai kudi yake da kuma rayuwa a gidan miji mai kudi, amma babu kwanciyar hankali. Akwai abubuwa da yawa a cikin fim din. Fim din ‘Inkiya’ shi ne ya fi ba ni sauki kuma ban fuskanci kalubale da yawa a cikinsa ba, saboda na fito ne a kawar jaruma. Fim din da ya fi ba ni wahala shi ne wanda na yi da tashar tauraro ta DSTb. Fim din a kan masu cutar sikila aka shirya shi.
A cikin ’yan fim wace ce ta fi burge ki?
Na fi son Zainab Indomi saboda duk abin da za ta yi a fim tana yinsa da gaske. Tana sha’awar abin da take yi ba kamar ana tilasta ta ba. Sai kuma a cikin jarumai, na fi son Adam A. Zango. Saboda yana da saukin kai da kwarjini a wurin mutane. Sannan kuma ya na saurin fito da mutanen da suke karkashinsa wato ba shi da bakin cikin ko kyashi.
Wane buri kike so ki cim ma a harkar fim?
Ina son na cim ma burika da yawa amma ni a ganina harkar fim ta Hausa ba ta yi karfi ba a nan kuduncin Najeriya. Saboda muna da karancin furodusoshi da jarumai. Ina rokon idan Allah ya ba ni dama in rika yin fim dina na kaina da kudina ta hanyar yin amfani da fasahar da Allah Ya ba wa matasanmu. Idan ka duba a yanzu za ka ga mutanenmu Hausawa ba su mayar da hankali a kan harkar ba. Ina so in zama furodusa amma irin furodusan da zai rika taimaka wa wadanda ba su da karfi.
A ganin ki mece ce matsalar fina-finan Hausa a nan Kudu?
Matsalar fim a Legas ita ce Hausawa ba su fiye son fina-finanmu ba sai na baki da suke a wasu wurare. Hankalin mutanenmu ya raja’a ga ’yan fim na Arewa a maimakon mu da muke tare da su. Akwai mutane da suke da kudi a Legas amma sun ki taimaka mana. Wannan abu yana karya mana gwiwa mu da muke yin fim a Legas. Ina kira ga mutanenmu su rika taimaka mana.
Wadanne nasarori kika samu a harkar fim?
Kodayake ba wani nisa na yi sosai ba a harkar, amma na samu alaka da masu tallace-tallace wadanda suke kirana na yi musu talla. Ka ga wannan ba karamar nasara ba ce. Ina da alaka da fitaccen jarumin barkwanci mai suna Sa’id Funky Malam.
Shin bayan kin yi aure za ki ci gaba da harkar fim?
Gaskiya idan na yi aure zan zauna a gidan mijina amma kuma zan rika yin fim a matsayin furodusa. Domin ni harkar fim ta zama jinin jikina saboda na san alfanunta.