Burina in yi waka a fina-finan Indiya- Mawakiya Taylor
Shahararriyar mawakiyar Amurka, wanda ta zama gwarzuwar mawakiyar Grammy Award sau hudu, Taylor Swift ta ce babban burinta bai wuce ta yi waka a fina-finan Indiya ba.Mawakiyar ta ce ta dade tana sha’awar kade-kaden kasar Indiya, inda ta ce ta fi son wakokin mawaki A R Rahman. “Na dade ina sauraron wakokin A R Rahman, […]
Shahararriyar mawakiyar Amurka, wanda ta zama gwarzuwar mawakiyar Grammy Award sau hudu, Taylor Swift ta ce babban burinta bai wuce ta yi waka a fina-finan Indiya ba.
Mawakiyar ta ce ta dade tana sha’awar kade-kaden kasar Indiya, inda ta ce ta fi son wakokin mawaki A R Rahman.
“Na dade ina sauraron wakokin A R Rahman, ya iya wakoki masu kayatarwa da kuma nishadantarwa. Wakokinsa suna motsa ruhi da zuciya, ina kwadayin in ga yana barje gumi a bikin kalankuwa ko gala.” Inji mawakiyar.
Mawakiyar ’yar shekara 24 ta ce tana yunkurin shirya kalankuwa a Indiya, saboda son kasar da take yi, sannan ta ce tana kudurin yin hadaka da mawakan Indiya a nan gaba.
Ta ce hakan ya sanya a yanzu take koyon yaren Hindi don idan ta ziyarci Indiya al’amarin ya zo mata da sauki.
“Koyon yaren Hindi zai taimaka mini wajen magana da ’yan kallo. A halin yanzu ban iya yaren ba, amma burina in yi waka a fina-finan Indiya.” Inji ta.
Mawakiyar ta ce za ta ziyarci Indiya, sannan za ta ci dukkan nau’ikan abincin kasar.
“Ina jin ana ambatar garuruwa da suka hada da Taj Mahal da Kashmir da Delhi da kuma South India. Ina son abubuwan tarihi. Don haka idan na kawo ziyara Indiya zan ziyarci wadannan garuruwan, don in kashe kwarkwatar idanuna.” Ta ce daga karshe.