Burina in zama Farfesa – Hajiya Hadiza Zakari Hadeja
Cikakken sunana: Sunana Hajiya Hadiza Zakari Hadeja, malama a Kwalejin Aikin Gona ta Bilyaminu Usman da ke Hadeja a Jihar Jigawa. Tarihina: An haife ni a Hadeja a 1968. Da yake mahaifina yana aiki a Zariya lokacin da nake karama an tafi da ni Zariya kasancewar mahaifina shi ne Sarkin Fulanin Hadeja wato Alhaji Dauda […]
Cikakken sunana:
Sunana Hajiya Hadiza Zakari Hadeja, malama a Kwalejin Aikin Gona ta Bilyaminu Usman da ke Hadeja a Jihar Jigawa.
Tarihina:
An haife ni a Hadeja a 1968. Da yake mahaifina yana aiki a Zariya lokacin da nake karama an tafi da ni Zariya kasancewar mahaifina shi ne Sarkin Fulanin Hadeja wato Alhaji Dauda Sale. Na yi makarantar firamare a garin Zariya a Tudun Wada a Makarantar Nurul Huda amma ban kammala ba sai mahaifina ya mayar da ni garin Hadeja kuma aka sanya ni a Makarantar Firamare ta Sambo inda na kammala a 1981. Ina daya daga cikin daliban da suka fara karatu a tsarin karatu na 6-3-3-4 kuma daga kanmu ne aka soke karatun aji bakwai a matakin firamare.
Mahaifina ya koma da ni Hadeja ne saboda haka ya yi wa duk ’yan uwana, saboda yana son mu saba da ’yan uwa domin kowa ya san mu saboda mutum ne mai son zumunci. Da na kammala firamare sai na wuce Kwalejin ’Yan Mata da ke Kura a Jihar Kano inda na kammala a 1985. Daga nan na samu nasarar shiga Makarantar Share Fagen Shiga Jami’a (CAS) da ke Kano inda na yi karatu a bangaren Kimiyya da nazarin halittu (Biology). Kafin na gama karatun ne mahaifina ya yi mini aure don yana cikin tsarin gidanmu ana yi mana aure ne da wuri, ba sai mun yi girma sosai ba.
Bayan na kammala ne sai samu damar shiga Jami’ar Bayero da ke Kano inda na yi kammala Digiri a kan Kiwon Lafiya da Kimiyya a 1992. A lokacin ina da aure kuma na samu ciki don haka ban je hidimar kasa ba sai a 1993. Kafin na kammala hidimar kasa ne aka dauke ni aiki a matsayin malama a Kwalejin ’Yan mata da ke Jahun a Jihar Jigawa. Na rike mukamin Shugabar Sashen Kimiyya da Fasaha (HoD) a 1994 a lokacin ana saura watanni biyu na kammala hidimar kasa.
Na yi aiki ne a kwalejin a tsakanin 1994 zuwa 2000 daga nan ne aka mayar da ni sabuwar Kwalejin ’Yan mata ta Kimiyya da Fasaha da ke garin Guri a matsayin Shugabar Makarantar (Principal) inda na yi aiki na tsawon shekara biyu. Daga nan ne na koma wata kwaleji da ake kira Model a matsayin Mataimakiyar Shugabar Makaranta. A lokacin wadansu baki ne suke rike da kwalejin a lokacin suna kokarin komawa kasarsu. Nan ma na yi aiki har na tsawon shekara biyu.
Bayan na kammala wa’adin shekara biyu a can sai aka mayar da ni Hukumar Kula da Makarantu ta Jihar Jigawa. Daga nan ne na samu damar komawa karo karatu na yi karatun PGD a kan kasuwanci da mulki, a Jami ar Bayaro da ke Kano. Kusan zan iya cewa duk karance-karancen da na yi, na yi su ne a Jami’ar Bayero ta Kano. Bayan na gama a shekarar 2006 sai na koma Kwalejin ’Yan mata ta Taura da ke Jihar Jigawa inda bayan shekara biyu kuma sai aka sake mayar da ni Kwalejin ’Yan mata da ke Jahun duk a matsayin Shugaba (Principal).
Daga nan na koma karatun digiri na biyu a fannin kasuwanci da mulki. Daga nan aka sake yi mini sauyin wurin aiki zuwa Kwalejin Koyon Sana’a ta Gwamnati ta maza zalla wato Gobernment Technical School da ke Hadeja. Daga nan na koma makaranta domin karo ilimi inda na yi nazari a bangaran ilimin tsirrai da halittu (Botny of Science).
Bayan an fara daukar ma’aikata a Kwalejin Aikin Gona ta Jihar Jigawa sai na koma can na ci gaba da aiki a matsayin Babbar Malama (Senior Lecturer), kuma yanzu haka ina yin karatun digiri na uku (PhD) a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. A takaice dai ina da shaidar ta digirin farko da na biyu kuma yanzu ina kan yin karatu a matakin digiri na uku wato PhD.
kalubalen da na fuskanta a rayuwa:
Lokacin da aka ba ni matsayin Shugabar Makarantar ’Yan mata ta Guri na fuskanci matsaloli masu yawa saboda a lokacin a gindin bishiya muke dauklar darasi. Al’amarin ya ba ni takaici saboda a lokacin ne ake ginin makarantar sai idan za a yi gini mu matsa wata kusurwa, da haka har aka kammmala. Duk zafin da nake da shi a kan yara sai da na yi sanyi domin yaran da suke makaranta kanana ne sai na koma ina rainonsu tamkar ’ya’yan cikina. Hakan ta sa na ba su tarbiyya don al’umma ta more su idan sun kammala karatu.
Burina:
Ba ni da wani buri a rayuwa da ya wuce in zama Farfesa domin tun ina karama nake da burin na zama masaniya a bangaren bayar da magunguna amma Allah bai nufa ba sai na tsinci kaina a halin yanzu a bangaren aikin gona. Yanzu haka ina karatun digiri na uku (PhD) ne a kan aikin gona, daga nan zan dora har in zama Farfesa insha Allah.
Gudunmawar da na bayar da ba za a taba mantawa ba:
Hakika na taimaka wajen samar wa wata mace aiki a lokacin da nake Guri a lokacin da aka yi wata annobar ciwon hanta wacce ta hallaka mutane da yawan gaske amma cikin ikon Allah cutar ba ta shiga makarantarmu ba, da ta shiga makarantar Allah kadai Ya san irin barnar da za ta yi.
Ita waccan matar a lokacin mijinta ya rasu, babban danta ya rasu, matar danta ta rasu. Ta zama ba ta da wani gata ta koma tamkar marar hankali. Da taimakon Allah sannan da taimakona na sa aka dauke ta aiki. Yanzu haka ta warware, ta zama mace ba ta da wata matsala. A lokacin da mijinta ya rasu ya bar ta da kananan yara, rayuwa ta yi mata tsanani.
Yanzu haka ita ce shugabar mata masu dafa abinci a Kwalejin ’Yan mata ta Kimiyya da Fasaha da ke Guri kuma tana nan tana aikinta. Kafin a dauke ta babu irin korafin da ba a yi ba amma na dage sai da na ga an dauke ta aiki. A gaskiya ina alfahari da wannan.
Abin da ba zan taba mantawa da shi ba
Mutuwar mahaifina ita cee abar da ta fi tsaya min a rai saboda mun shaku da juna don ya nuna mini gata. Duk da yake ya yi karatun boko mai zurfi ba ya daukar kansa a matsayin wani, yana gudanar da rayuwa ne irin ta kowane talaka. Bayan ya sanya mu a makaranta mun girma, ba ya da abokan shawarar da suka wuce mu. Sai dai na yi addu’ar Allah Ya jikansa da rahama.
Tarbiyyar ’ya’ya mata a yanzu da kuma a da:
A gaskiya akwai bambanci a tsakanin tarbiyyar ’ya’ya mata a yanzu da kuma a da. Domin a da iyaye ne ke zabar wa ’ya’yansu mazan aure amma yanzu ’ya’ya ne ke zabar wa kansu mazan aure kuma mafi yawa kyale-kyalen abin duniya ne yake rudarsu shi ya sa da an yi auren sai ka ji an rabu.
Yawan mutuwar aure:
Babban dalilin da ya sa ake yawan samun mutuwar aure shi ne rashin bin tafarkin shari’a. Sannan da yawa iyaye ba sa koya wa ’ya’yansu mata girki a gida, sai bayan an yi aure sai ka ga an koma ana ta kame-kame. Babu mijin da zai jure fita yana cin abinci a shagunan sayar da abinci a rayuwarsa alhali yana da mace a gida. Wadannan na daga cikin dalilan da ke janyo mutuwar aure a yanzu.
Neman ilimi ga ’ya’ya mata:
Akwai gyara domin ita rayuwar mace tana da takaitaccen lokaci saboda ita rayuwar mace gajeriya ce kamata ya yi idan ta samu lokaci a rika aurar da su a kan lokaci maimakon su ce za su ci gaba da yin karatu kafin su yi aure. Don haka mace za ta iya neman ilimi idan ta kasance a dakin mijinta. Haka ma ya fi mutunci. Bayan yarda sai mace ta balaga a gida tana karatu kafin ta yi aure ba. Duk karatun da na yi, na yi ne a dakin mijina, don haka aure ba ya hana ilimi, kamar yadda ilimi bai hana a yi aure.
Abin da ya fi ba ni tausayi:
Yadda wadansu iyaye ke tura yara kanana karatun allo a garuruwan da ba nasu ba. Ka ga yaro ya shiga wata irin rayuwa tun yana karami. Gaskiya wannan abin tausayi ne.
Batun iyali:
Ina tare da mijina wato Alhaji Mahmood Muhammad, wanda shi ne Mataimakin Magatakarda a kwalejin da nake aiki a halin yanzu. Muna da ’ya’ya shida, uku maza, uku mata da jikoki biyar. Daga cikin ’ya’ana akwai Sadik Mohammed shi ma malami ne a kwalejin da nake aiki sai Shu’aibu Muhammed wanda shi kuma likita ne a Babban Asibitin Birniwa, sai kanwarsu da take kataru a Jami ar Ahmadu Bello da ke Zariya tana nazarin aikin shari’a tana ajin karshe.
kasashen da na ziyarta:
Na ziyarci kasashen Saudiyya da Masar.
Abin da ya fi bata min rai:
Ba na son karya da yaudara don ina da saurin amincewa da mutum. Sannan ba na son cin amana.
Abincin da na fi so:
Wake da doya, don ina sarrafa su ta hanyoyi da dama.
Tufafin da na fi so:
Na fi son leshi duk da yake yana da nauyi, amma ban gajiya da shi.
Abin hawa:
Ni fi son mota kirar Honda da kuma Fijo domin Fito ta fi kowace mota kwari da juriya, don haka nake son ta.