Burina in zama farfesa – Wada Mai Hidimar kasa
Wani wada mai suna Shamsudden Abdullahi, wanda aka fi sani da Saiful Islam Diniya mai shekara 25 da ke zaune a Unguwar kwarbai, Zariya a Jihar Kaduna kuma yanzu ke hidimar kasa a Hukumar Kula da Harshen Larabci da Ilimin Addinin Musulunci ta kasa (NBAIS) da ke Kaduna, ya ce nakasar da yake tare da […]

Wani wada mai suna Shamsudden Abdullahi, wanda aka fi sani da Saiful Islam Diniya mai shekara 25 da ke zaune a Unguwar kwarbai, Zariya a Jihar Kaduna kuma yanzu ke hidimar kasa a Hukumar Kula da Harshen Larabci da Ilimin Addinin Musulunci ta kasa (NBAIS) da ke Kaduna, ya ce nakasar da yake tare da ita ba ta hana shi neman ilimi ba.
A tattaunawarsa da Aminiya, Shamsuddeen Abdullahi ya yi wa Allah godiya bisa damar da ya ba shi don yin karatu tare da tallafawar al’umma.
Shamsu ya ce ya hadu da kalubale da dama amma hakan bai hana shi yin karatu ba. “Na faro daga makarantar firamare har zuwa sakandare, amma a lokacin da na shiga Kwalejin Kimiya da kere-kere ta Nuhu Bamalli da ke Zariya, nan na samu Babbar Diploma ta kasa kuma ga shi yanzu ina hidimar kasa.
“Wato fannin da na karanta yana da wuya ga mai nakasa irin tawa, amma bai hana ni yin sa ba saboda ba da kafa ake yi ba, kuma ba wai sai da tsawo ake yi ba, a’a, tunda Allah Ya yi mini kwakwalwa sai na ga zan iya; domin a cikin abokaina suna ganin kamar ba zan iya ba to, don haka sai na kara mai da hankali wajen ganin na yi duk abin da suke ganin ba zan iya ba. Domin shi karatun da na dauka yana da wuya saboda gwaje-gwaje ne ya fi yawa amma tunda dai ba karfi ba ne, don haka na tsaya sosai don ganin na yi.”
Ya kara da cewa, “Yanzu bukatata ita ce inda zan samu damar haduwa da Matar Mataimakin Shugaban kasa, Dopulafor Osibanjo a kan alkawarin da ta yi mini lokacin da ta kawo ziyara a sansanin yi wa kasa hidima da ke Kubwa,Abuja. Ta yi mini alkawarin samar mini aiki idan har na gama hidimar kasa, lokacin da ta hango ni cikin mu kusan dubu uku da wani abu, saboda mamakin ga ni nakasashe kuma ina sanye da kayan yi wa kasa hidima. Sai ta sa aka kira ni, tana mamakin cewa duk da yadda Allah Ya yi ni amma na tsaya na yi karatu. Ta tambaye ni, ni kuma na fada mata cewa duk da na fito a gidan da ba masu hali sosai ba, burina shi ne in gwada wa ’yan uwana masu nakasa cewa kada su yi wasa da harkar neman ilimi kuma na gaya mata cewa abin da nake bukata a rayuwata shi ne ba wai in samu kudi ba, a’a, ni dai su ba ni aikin yi ta bangaren karatun da na yi, domin in dogara da kaina, kuma jama’a su ci amfanin karatuna; wato gwamnati ta ba ni aikin yi.
To, ta amsa mini, sai dai kuma yanzu ban san yadda zan yi in kara ganinta ba, ka san irin wadannan mutanen aiki ya yi musu yawa. Kafin ta tuna da ni sai dai idan rabona ya ratsa. Kuma burina na gaba shi ne, a wannan karatu in ga na kai har matasayin Farfesa. Yanzu haka idan na sa wannan kaya na hidimar kasa, ina bin ’yan uwana nakasassu masu tsayawa a gidajen mai da kokon bara, ina wayar musu da kai cewa kada su tsaya suna wulakantar da kai wurin barace-barace, su yi kokari su yi karatu, domin su taimaki kansu kuma na fara samu nasara a kan haka. Domin idan na yi musu bayani suna gamsuwa. Don haka nan gaba idan na samu aiki, zan karfafa wannan da’awa tawa ta wayar da kan nakasassu a kan su daina bara. Wannan shi ne burina a rayuwa,” inji shi.