Burina in zama fitaccen mawaki a zamanina – Umar Katanga Mawakin Gwandara
Matashin mawaki Dan kabilar Gwandara, wanda kuma yake da fasahar rera wakoki cikin harshensa na gado, Umar S. Katanga, ya bayyana cewa yana alfahari da sana’arsa ta waka, inda kuma ya jaddada cewa babban burinsa shi ne ya ga cewa ya samu Daukaka, ya shahara a fannin waka a zamaninsa.A yayin ziyararsa ga Aminiya, mawakin […]
Matashin mawaki Dan kabilar Gwandara, wanda kuma yake da fasahar rera wakoki cikin harshensa na gado, Umar S. Katanga, ya bayyana cewa yana alfahari da sana’arsa ta waka, inda kuma ya jaddada cewa babban burinsa shi ne ya ga cewa ya samu Daukaka, ya shahara a fannin waka a zamaninsa.
A yayin ziyararsa ga Aminiya, mawakin ya bayyana cewa shi Dan asalin kabilar Gwandara ne da aka haifa shekaru 25 da suka gabata a kauyen Shereti-Kabusa da ke yankin Abuja, amma daga bisani iyayensa suka yi kaura zuwa Suleja, Jihar Neja, inda yake zaune a halin yanzu. Ya ce bai yi karatu mai zurfi ba, saboda matsalolin rayuwa gami da rashi. “Na yi karatun firamare a Shereti, inda daga bisani na samu tafiya makarantar sakandare ta Garki-Abuja, amma ban samu damar kammalawa ba, saboda matsalar rayuwa da rashi, amma ina da bukatar in ci gaba da neman ilimi.” Inji shi.
Mawakin, wanda ya ce ya fara sana’ar waka shekaru biyar da suka gabata, ya bayyana cewa yana yin waka da yarensa na Gwandara da kuma Hausa. Ya zuwa yanzu ya fitar da faifan waka guda Daya a shekarar 2014, wanda ya sanya wa suna Wawarawaye (Kowa da ranarsa). “Wannan faifan yana Dauke da wakoki huDu ne, wato ita wakar Wawarawaye da wakar Tarihin Kano da wakar Gaisuwa ga al’ummar Gwamdara da kuma wakar Olale (hanya ta rabu). Abin da ya sanya na yi wakar Tarihin Kano shi ne, saboda ka san mu Gwandara, asalinmu daga Kano ne, su Kanawa yaran gidanmu ne.” Inji matashin mawakin na Gwandara.
Ko ta yaya yake samun fasahar tsara wakoki? Tambayar da Aminiya ta yi masa ke nan, inda shi kuma ya amsa da cewa: “Ni dai kam Allah Ya ba ni baiwa ce kawai, ba na rubuta waka, domin da zarar na bukaci in rera waka, takan zo mani ne kawai sai in kama rerawa.”
Ya zuwa yanzu dai ya ce yana nan yana tsara fitar da faifansa na biyu kasuwa, amma a halin yanzu yana yin wakoki a wuraren bubukuwa da suna na Gwandara da sauran wuraren da aka gayyace shi. Ya kuma yaba da yadda al’umma, waDanda ba ma na Gwandara ba suka yi na’am da wakokinsa. Ya ce faifansa na farko ya samu amsuwa daga Yarabawa da Hausawa da Gwandara da sauran kabilu daban-daban.