Burina in zama injiniya –Yarinya mai gyaran manyan babura
Maryam Muhammad Bawada yarinya ce da ke aji biyu a karamar Makarantar Sakandare ta Gwamnati ta Mpape (Pape) da ke hanyar Katampe a yankin Birnin Tarayya, Abuja. Sai dai kokarin da take yi wajen koyon gyaran manyan baburan nan da ake kira motor bike a Ingilishi na daya daga cikin abubuwan da suke jawo hankalin […]

Maryam Muhammad Bawada yarinya ce da ke aji biyu a karamar Makarantar Sakandare ta Gwamnati ta Mpape (Pape) da ke hanyar Katampe a yankin Birnin Tarayya, Abuja. Sai dai kokarin da take yi wajen koyon gyaran manyan baburan nan da ake kira motor bike a Ingilishi na daya daga cikin abubuwan da suke jawo hankalin jama’a game da ita. Aminiya ta tattauna da ita a wurin gyaran manyan baburan na mahaifinta, Malam Muhammad Bawada wanda ma’aikacin Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa ne (FRSC) da ke Abuja. Maryam ta shaida wa wakilinmu cewa baya ga gadon mahaifinta ne gyaran, burinta ta zama injiniya:
Aminiya: Mene ne sunanki, kuma ke mutuniyar ina ce?
Maryam Bawada: Sunana Maryam Muhammad Bawada, kuma ni mutumiyar Kano ce, amma a nan Abuja aka haife ni nan na yi firamare a LEA, Mpape. Iyayena mutanen Zango ne da ke karamar Hukumar Birnin Kano.
Aminiya: Me ya ba ki sha’awa kika shiga gyaran wadannan manyan babura?
Maryam Bawada: Ganin yadda mahaifina yake gyara wadannan manyan babura ne ya ba ni sha’awa. Na tashi ne na iske kaina ina taimakon babana, saboda ina ganin yana yi, ya sa na fara sha’awa daga nan na fara koya.
Aminiya: Za ki kai kamar shekara nawa a duniya?
Maryam Bawada: A yanzu ina da shekara 16 a duniya.
Aminiya: Ke nan kina makaranta, kuma a ina?
Maryam Bawada: Ina makaranta a karamar Sakandaren Mpape da ke Katampe a nan Abuja, yanzu ina aji biyu na karamar sakandare (JSS2).
Aminiya: Kina da burin ci gaba da wannan sana’a bayan kin kammala karatu?
Maryam Bawad: Eh, ina da burin ci gaba da gyaran ko kuma sayar da kayan gyarar manyan baburan.
Aminiya: A yanzu da me da me kika iya game da gyaran?
Maryam Bawada: Na iya cire taya da sabis din babur din da legi da su kamar fulug-gaf da sauke inji da gyara shi, wani lokaci kuma ina koyon gyaran mota, kamar yadda na iske mahaifina yana yi.
Aminiya: Misali idan aka kawo gyaran ga babanki, yakan bar ki ne ya zuba miki ki gyara ko yaya?
Maryam Bawada: Yana bar ni in yi ne, inda ya lura na yi kuskure sai ya nuna min yadda zan yi.
Aminiya: Yanzu kin kai kamar shekara nawa kina koyon wannan sana’a?
Maryam Bawada: Na kai shekara biyu.
Aminiya: Cikin shekara biyun kina jin kin gyara babura kamar guda nawa?
Maryam Bawada: Ba zan iya sanin adadinsu ba, saboda kawowa ake mu gyara su tafi, ba a nan suke ajiye ba. Sai dai ina jin za su kai goma sha. Kuma wannan babur da ka dauke ni a kansa nakan kwance shi daidai in hada shi.
Aminiya: An taba kawo irin wadannan manyan babura kika gyara mahaifinki ba ya nan?
Maryam Bawada: Ba a kawo gyaran sai yana nan, sai dai in an kawo kamar sabis din taya da sabis din babur din ko ba ya nan muna yi.
Aminiya: Kin fara fita kina aiki a biya ki ko har yanzu a nan wurin mahaifinki ke ki aikin?
Maryam Bawada: Wani lokacin ina fita amma tare da mahaifina muke fita ba na fita ni kadai.
Aminiya: Kin iya baburan da kike gyarawa ne?
Maryam Bawada: Eh, na iya wasu amma ba dukkansu ba. Ina hawa Yamaha da Kawasaki, amma ba mafiya girmansu ba, kananansu.
Aminiya: Kasancewar kina gyaran wadannan babura, yaya kawayenki suke kallonki?
Maryam Bawada: Suna jin dadi, amma suna ganin kamar in bari wannan ba aikin mata ba ne, na maza ne. Kuma nakan ce musu ba dominsu nake yi ba, don kaina nake yi.
Aminiya: Cikin kawayenki ba wadda ta taba cewa ita ma bari ta zo ta koyi wannan gyara?
Maryam Bawada: Eh, akwai kawayena da suke sha’awa amma ba ta koyon gyaran wadannan babura ba, su suna sha’awar yadda nake hawa babur din ne.
Aminiya: Idan Allah Ya hada ki da mai sha’awar wannan sana’a koda bayan aurenki kina jin za ki ci gaba?
Maryam Bawada: Eh, zan ci gaba.
Aminiya: Ba wanda ya taba nuna miki hawa wadannann manyan babura hadari ne musamman ganin ke yarinya ce?
Maryam Bawada: Akwai su da yawa ba ma kawayena kawai ba, har da sauran mutane.
Aminiya: Ku nawa ne a cikin ’ya’yan mahaifinku kuke koyon gyaran manyan baburan?
Maryam Bawada: A cikin ’ya’yan mahaifinmu takwas, mu biyu ne muke koyon gyaran manyan baburan a yanzu.
Aminiya: A bangaren karatu me kike son zama?
Maryam Bawada: Burina in zama injiniya, musamman a bangaren da ya shafi harkokin injuna.
Aminiya: Yanzu me kike karantawa?
Maryam Bawada: Yanzu ina karamar sakandare ce, kuma darussan da na fi dagewa a kai, su ne na ilimin farko kan kere-kere (basic technology). Wanda yake da alaka da aikin da nake yi a yanzu.
Aminiya: Kina da sako ga yara mata wadanda su ne ake watsi da ilimi ko sana’arsu?
Maryam Bawada: Kirana ga yara mata, su mayar da hankali su koyi sana’a wadda za ta zame musu abin dogaro a rayuwarsu. A da can mata suna yin sana’o’in hannu, yanzu sun yi watsi da su, wannan ya sa suke dogaro su zama nauyi a kan mazaje ko iyayensu.
Aminiya: Wane kira za ki yi ga yara, wadanda maimakon koyon sana’a sai su rika yawace-yawace da sauransu?
Maryam Bawada: Ga yara ’yan uwana, ina kira gare su, ko ba irin aikin da nake yi ba, duk aikin da suka ga mahaifinsu ko wani yana yi da ya ba su sha’awa, suke ganin zai amfane su, to su tsaya su koya domin dogaro da kansu.