Burina in zama lauya, ba dan fim ba – Chinedu Ikedieze

Jarumi Chinedu Ikedieze (Aki) abokin tagwaitakar Osita Iheme (Popo) ne a harkar fina-finan barkwanci. Sun shafe shekaru masu yawa suna fitowa a fina-finan barkwanci. A bara ne suka fara fitowa a fina-finan Hausa. Wakilinmu ya gana da shi a ranar Asabar a Abuja lokacin da suke daukar fim din ‘Hajiya Babba’. Jarumin ya yi bayanin […]

Burina in zama lauya, ba dan fim ba – Chinedu Ikedieze
Burina in zama lauya, ba dan fim ba – Chinedu Ikedieze

Chinedu sanye makawuyaJarumi Chinedu Ikedieze (Aki) abokin tagwaitakar Osita Iheme (Popo) ne a harkar fina-finan barkwanci. Sun shafe shekaru masu yawa suna fitowa a fina-finan barkwanci. A bara ne suka fara fitowa a fina-finan Hausa. Wakilinmu ya gana da shi a ranar Asabar a Abuja lokacin da suke daukar fim din ‘Hajiya Babba’. Jarumin ya yi bayanin yadda ya fara fim, sannan ya tabo wadansu batutuwa da suka shafi rayuwarsa.

Za mu fara da takaitaccen tarihinka
Sunana Chinedu Ikedieze, an haife ni a ranar 12 ga Disamba, 1977 a kauyen Bande, Jihar Abiya. Na yi makarantar firamare da sakandare. Daga nan na karanta aikin jarida a makarantar Institute of Management Technology (IMT), daga bisani na shiga harkar fina-finai. Ina da mata mai suna Nneoma.
Yaushe ka fara fim?
Na fara fim a shekarar 2002, inda na fara da wani fim mai suna ‘Spanner’. A shekarar na yi fim kamar su ‘Ukwu na Uka’ da ‘Aka Gum’ da ‘Tom and Jerry’ da sauransu.
Tun fil’azal kana da burin zama jarumi ne?
A lokacin da nake karami burina in zama Lauya, daga baya sai kaddara ta mayar da ni jarumi. Har na kammala sakandare burin da ke raina shi ne, in zama lauya, amma sai wani dan uwana ya gamsar da ni ta hanyar zakakan bayanai cewa zan dace da aikin jarida, hakan ya na fara karatun koyon aikin jarida. A lokacin da nake tsangayar koyon aikin jarida ne na shiga kungiyar wasan kwaikwayo mai suna Communicators Art Forum, wannan shi ne silar zamana jarumi, kasancewar daga baya wata jami’a a kasar waje ta aiko mini da takardar shiga jami’ar, amma na ce na fi so in ci gaba da harkar fim.
Kai da Osita abokan juna ne tun kafin ku fara fim?
A’a, na hadu da shi ne a shekarar 2002, a lokacin na je Legas don yin gwajin zama cikakken jarumi. Ba na  mantawa a lokacin bikin yaye daliban da makarantarmu ta shirya ne ta gayyaci Nkem Owoh (Osoufia) a matsayin babban bako, inda muka yi wasan kwaikwayo, rawar da na taka yayin wasan kwaikwayon ne ta burge shi, a lokacin bai ce mini komai ba. Sai wata rana ya sanya aka nemo masa ni, bayan mun hadu ne ya ce yana so in zama jarumi, domin ya gamsu da rawar da na taka a lokacin da ya halarci bikin da makarantarmu ta shirya. Farin ciki a wurina kada ka tona, hakan ya sanya na rika zuwa gwajin zama jarumi, to a nan na hadu da Osita har ya zama babban abokina.
Kana da burin shirya fim na kanka?
kwarai kuwa, amma zan fi mayar da hankali wajen shirya fina-finai da harshen gida. Na gamsu da yadda ake sayan fina-finan Yarabawa, sun samu karbuwa har a kasashen waje. Ko lokacin da na je Landan jama’a a can sun yaba musu.
Chinedu Ikedieze da matarsa Nnoema, sai mawaka P-Sqaure da kuma Osita Iheme (na daya daga hagu)A yanzu ba ku cika fitowa tare da Osita ba, me ya faru?
Ba wai mun daina fitowa tare ba ne. Ya danganta da yanayin labarin fim ne. Idan ya hada mu za a gan mu tare, idan bai hada mu ba kuma ba za a gan mu tare ba. Kamar a wannan fim din ne na ‘Hajiya Babba’, ka ga ni kadai aka kira. Amma a fim din da muka yi a bara mai suna ‘karangiya’, ka ga labarin ya hada mu.
Jama’a sun yada jita-jitar cewa matarka don sunanka ta aure ka, me za ka ce kan hakan?
(Dariya), ba a taba raba mutane da yamididi ba, haka kawai wani zai zauna ya rika yada zancen da ba shi da tushe ballantana makama. Wannan batu ban san da shi ba.
To, ta yaya kuka hadu da ita?
Mun dade da ita, tun ma kafin in yi suna, sauran abubuwa kuma sirri ne, masu magana kuma su ci gaba da fadar abin da suka dama, wannan ya rage nasu.
Me ya fi ba ka sha’awa dangane da fim din Hausa?
Suna yin fim cikin tsari, kuma kowa na taka rawar da ta dace da shi, babu wanda yake wuce makadi da rawa. A gaskiya na yaba yadda suke gudanar da al’amuransu.
Yaya ka ji a farkon lokacin da aka ce za ka yi fim din Hausa?
Ban taba tsammanin zan iya fim din Hausa ba, ban ma taba tunanin hakan ba. Wata rana sai na ji an kira ni, ana bukatar zan yi fim din Hausa. Na dauki al’amarin kamar wasa, amma suka tabbatar mini da gaske suke. Abin ya ba ni mamaki, na rika tunanin ta yaya zan iya magana da Hausa, kasancewar ban iya yaren ba. Na tambayi kaina ta yaya zan sa labarin fim din? Daga baya suka yi mini bayanin yadda labarin fim din yake, sai na ji yana dauke da darussa, hakan ya sa na amince, amma ina dari-darin yadda aikin zai kasance. Sai dai bayan sun yi mini gamsasshen bayanin yadda aikin zai kasance sai na ga ba zan wahalar da nake tsammani ba.
Yaya ka ji bayan ka fara fim din?
Daga farko kalmomin sun yi mini tsauri, amma da na ga kowa ya saki jiki da mu, sai na samu karfin gwiwa, hakan ya taimake ni har muka kammala daukar fim din.
Wacce rawa ka taka a wannan fim din mai suna ‘Hajiya Babba’?
Na fito a matsayin shahararren mai dafa abinci ne, to akwai wanda muke kiransa Sarkin Hausawa da ke zuwa sayen abinci wurinmu, kuma yana da ubangida (Sani Garba SK), wanda shi kuma mai kudi ne, burinsa ya dadada wa mahaifiyarsa (Hafsatu Sharada), hakan ya sanya Sarkin Hausawa ya kai ni gidan ubangidansa, don in rika dafa wa mahaifiyarsa abinci, a nan muka hadu da direban ubangidansa (Rabilu Musa Ibro). Masu kallo za su yaba rawar da na taka a fim din.
Mene ne ya faru da kai na bakin ciki a harkar fim da ba za ka manta da shi ba?
Wannan ya faru ne a farko-farkon shekarun da muka fara fim, inda aka rika cewa yara a gida na kwaikwayon abubuwan da muke yi a fim, maimakon su fada ka, mun ji babu dadi, hakan ya sanya muka fada wa furodusoshi da daraktoci su rika kawo sina-sinai da ke nuna nadamarmu ko kuma wani hukunci mai tsanani a kanmu da zai zama izna. Wannan ya sanya a fim din ‘karangiya’ muka sanya aka kirkiri fitowar da ke nuna nadamarmu, wanda a labarin fim din babu shi.
Me za ka ce a kan Ibro?
kwararren jarumi ne, ina jin dadin yin fim da shi. Kana kallonsa za ka san zai iya fim din barkwanci.
Me ya sa yanzu aka yi hadaka tsakanin ’yan fim din Kudanci da kuma na Arewaci?
Daga hagu Sadik Mafiya da Chinedu Ikedieze da Sani Sk da Sarkin Hausa yayin daukar fim din ‘Hajiya Babba’A gaskiya a halin da ake ciki a Najeriya ana bukatar hadin kai, don haka za mu yi amfani da harkar fim wajen nuna wa jama’a cewa dole sai an hada kai. A yanzu jama’a sun fara fahimtar babu wani bambanci tun da jaruman fina-finan Hausa irinsu Ali Nuhu da Sani Danja sun yi fim a Nollywood. Haka ni da Osita da Nkem da John Okafor da sauransu mun yi a Kannywood.
Shawararka ga ’yan fim?
’Yan fim su gane ba sai an fitar da fim kashi-kashi kafin a samu kudi ba, za a iya fitar da fim mai inganci kashi daya ya samar da duk kudin da ake so, domin jama’a da dama ba sa son sayan fim saboda sun san ba zai kare a kashi daya ba.