Burina in zama muryar marasa murya – Hajiya Halima Joda Kyari
Hajiya Halima Joda Kyari, ita ce Shugabar Majalisar Zartarwar Kungiyar Mata ta Kasa (NCWS), reshen Jihar Yobe, kuma tsohuwar ma’aikaciyar gwamnati ce kwararriya a bangaren sanin harkar gandun daji a Jihar Yobe. Ta yi aiki a Ma’aikatar Harkokin Kula da Gandun Daji ta Forestry har ta yi ritaya. A zantawarta da Aminiya ta bayyana irin […]
Hajiya Halima Joda Kyari, ita ce Shugabar Majalisar Zartarwar Kungiyar Mata ta Kasa (NCWS), reshen Jihar Yobe, kuma tsohuwar ma’aikaciyar gwamnati ce kwararriya a bangaren sanin harkar gandun daji a Jihar Yobe. Ta yi aiki a Ma’aikatar Harkokin Kula da Gandun Daji ta Forestry har ta yi ritaya. A zantawarta da Aminiya ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha a rayuwa kamar haka:
Tarihin rayuwata:
Sunana Hajiya Halima Joda Kyari. An haife ni ne a garin Gadaka a Karamar Hukumar Fika a Jihar Yobe, kuma ni ’yar kabilar Ngamo ce da ke Karamar Hukumar Fika ta Jihar ta Yobe. Ni mutuniyar karkara ce, a can aka haife ni. Babana hedimasta (Headmaster) ne wato shugaban malaman firamare. A can na girma har aka sanya ni a Makarantar Firamare ta Central da ke garin Potiskum. Bayan na gama na sai ta fi Kwalejin gwamnati wato G.S.S. Nguru, na samu shaidar kammala sakandare. Daga nan sai aka yi mini aure. Daga nan sai na ta fi Kwalejin aikin gona na samu Difloma a fannin raya gandun daji Daga nan sai na tafi Jami’ar Maiduguri inda na samu digiri na farko a bangaren nazarin harsuna.
Aiki:
Na yi aiki a ma’aikatar kula da gandun daji, da ma’aikatar gona da kuma ma’aikatar tsaftace muhalli a Jihar Yobe amma na taso tun ina karama da sha’awar aikin kungiya amma ban yi ba sai da na yi ritaya don kashin kaina a 2012. Ina yin ritaya sai na ci gaba da ayyukan kungiya da taimakon kai- da- kai.
Nasarori:
Na samu nasarori sosai domin a lokacin da nake aikin gwamnati a ma’aikatun kare gandun daji da na kare muhalli da ma’aikatar aikin gona, na tsaya sosai wajen ganin ba a cutar da wani ba kuma duk inda aka samu matsalar muhalli mukan je mu warware matsalar.
Kalubale:
A lokacin da nake aikin gwamnati na saba da kalubalen saboda babban kalubale shi ne hada aikin gida da na ofis da kuma rainon yara. Aa wani lokaci kuma mazan da kuke aiki tare ba su so su ga an yaba miki ke mace saboda kwazon ki, amma ni na yi aiki da kowa lafiya, na gama lafiya. A bangaren aikin kungiya kasancewar ina shugabancin NCWS, Majalisar kungiyar mata ta kasa muna sanya ido kan yadda ake cin zarafin mata ta hanyar fyade wasu Iyayen suna boye ‘yarsu idan aka mata fyade, wanda hakan bai taimaka wa. Tsayuwar mu ne kan haka ya sa har Gwamna Ibrahim Gaidam, ya bullo da dokar daurin rai da rai kan duk wanda aka kama da laifin fyade.
Burina a rayuwa:
Burina shi ne in ci gaba da zamowa muryar marar murya don tsaya wa sosai wajen kare marasa gata musammam mata da yara kananan da ake ci wa zarafi ta hanyar yi musu fyade.
Kungiyoyi:
Kungiyoyin da nake ciki su ne: National Council for Women Society of Nigeria (NCWS) da
Kungiyar Masu Noman Shinkafa da kuma kungiyar dukkan manona ta kasa (All Farmers Association of Nigeria) sai kuma Kungiyar Sun flower Association da Kungiyar Manoman Alkama (Wheat farmers Association).
Kasashe:
Na je kasashe da dama da suka hada da Amurka da Birtaniya da Katar, da Swaziland da Kenya da sauran su.
Kwasa-kwasai:
Na je kwas a College of Agro Forestry a Maguga da ke Nairobi a Kenya da Gonar Mai Zube wato Mai Zube Farms da ke garin Minna a Jihar Neja da kuma School of Forestry Kano.
Yawan Iyali:
Alhamdulillahi ina da ‘ya’ya hudu, uku maza daya mace.
Tufafi:
A matsayina ta ’yar Arewa, na fi sha’awar daura zani da riga sannan na yafa gyale saboda cikar kamala da mutuncin ’ya mace.
Hutu:
Hutu kan kamawa yake yi amma abu ne na kashin kai wanda sai inda mutum ya zaba sannan ya je hutu.
Shawara ga iyaye:
A matsayina ta uwa, ina mai bai wa iyaye shawarar su bar ‘ya’yan su musamman mata su nemi ilimin zamani domin ba ya ga ilimin addini, kamata ya yi a ce kowace mace ta samu ilimi dai dai da namiji domin mace idan ba ta da ilimi ta zama shashasha, kuma idan ta samu ilimi takan fi taimakawa iyayen ta. Har ila yau kamar batun dora wa mata tallace-tallace ba daidai ba ne domin talla wata jami’a ce da ke lalata tarbiyya yara musamman mata.