Burina inganta rayuwar mata da kananan yara – Ministar Mata

Ministar Harkokin Mata, Sanata Aisha Jummai Alhassan ta bayyana cewa za ta hada kai da gwanatocin jihohi don ganin ta bunkasa rayuwar mata da yara kanana a fadin Najeriya. Ministar ta fadi haka ne a lokacin da ta kai ziyarar aiki Jahar Jigawa, ta gana da gwamnan jahar, Alhaji Badaru Abubakar a fadar gwamnati a […]

Burina inganta rayuwar mata da kananan yara – Ministar Mata

Ministar Harkokin Mata, Sanata Aisha Jummai Alhassan ta bayyana cewa za ta hada kai da gwanatocin jihohi don ganin ta bunkasa rayuwar mata da yara kanana a fadin Najeriya. Ministar ta fadi haka ne a lokacin da ta kai ziyarar aiki Jahar Jigawa, ta gana da gwamnan jahar, Alhaji Badaru Abubakar a fadar gwamnati a ranar Talatar da ta gabata.

Ta ce makasudin ziyarar tata, zagaya dukkan jihohin kasar nan ne da nufin kyautata rayuwar mata ta hanyar hada kai da kwamashinonin ma’aikatar mata dake jihohin Najeriya da nufin taimakawa matan karkara.

Hajiya Aisha Alhassan ta ce akwai bukatar ma’aikatartun mata na tarayya da jihohi su samu fashimtar juna a aikace ta hanyar samar da rance ga mata, kasancewar mata su ne shawuya a cikin harkokin rayuwar iyali ta yau da kullum.

Da yake jawabin martini, Gwamnan Jahar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar ya ce gwamnatinsa ta samar da shiri na tallafawa mata da yara kanana ta hanyar samar da sana’ar hannu kamar dinki da shirin duwatsu da kiwon kaji da sauran ayyukan inganta rayuwar mata.

Badaru ya kara da cewar gwamnatinsa a duk Najeriya ce ta fara shirin baiwa mata jarin kiwon awaki da aka fara sama da mata dubu 40 ne suka amfana da shirin na bayar da rance da gwamnatinsa ta bullo da shi da nufin inganta rayuwar mata a jahar.