Burina kara daga martabar Najeriya a Jamus – Ambasada Yusuf Tuggar

A farkon Makon nan ne Al’ummar Jihar Bauchi suka karrama sabon jakadan Najeriya a kasar Jamus, Tsohon dan Majalisar Tarayya sannan dan takarar gwamna a karkashin APC a 2015, Ambasada Yusuf Tuggar don yi masa bankwana. Kafin tafiyar tasa, ya zanta da manema labarai ciki har da Aminiya. Ga kadan daga cikin abin da sabon […]

Burina kara daga martabar Najeriya a Jamus – Ambasada Yusuf Tuggar

A farkon Makon nan ne Al’ummar Jihar Bauchi suka karrama sabon jakadan Najeriya a kasar Jamus, Tsohon dan Majalisar Tarayya sannan dan takarar gwamna a karkashin APC a 2015, Ambasada Yusuf Tuggar don yi masa bankwana. Kafin tafiyar tasa, ya zanta da manema labarai ciki har da Aminiya. Ga kadan daga cikin abin da sabon Ambasadan ya bayyana kamar haka:

 

 

Aminiya: Idan ka tafi kasar Jamus, ko wane abu ne zaka fi maida hankali akai?

Ambasada Tuggar: Idan Allah Ya sa na isa kasar Jamus na fara aiki zan yi kokari kwarai wajen yin ayyukan da za su kara kawo wa Najeriya martaba da daraja da daukaka ta yadda za a sami bunkasar tattalin arziki da kyakykawar dangantaka, haka kuma zan yi kokari a wanan gefe wajen jawo masu zuba hannun jari daga kasar Jamus a Najeriya, zan yi kokarin neman taimako ga Najeriya daga kasar, ta yadda zamu tabbatar da cewa an samu cikakkiyar zaman lafiya a Arewa maso Gabashin Najeriya, da yankin da ake hako albarkatun man fetur na Neja-Delta da makeken tekun nan mai arziki da ake kira da (Gulf of Guinea), zan kuma yi kokari domin ganin ana fitar da kayayyakin da ake nomawa ko sarrafawa a Najeriya ana fitar da su a na kai su kasuwannin kasar Jamus, haka kuma zan yi kokari wajen kara dankon zumunci tsakanin kasarmu Najeriya da Jamus.

 

Aminiya: Matsalasr ‘yan gudun hijira daga Najeriya a kasar Jamus babbar matsala ce da a yanzu ke damun kasashen biyu, ta ya ya zaka fuskanci wannan matsala?

Ambasada Tuggar: Eh to. A bisa gaskiya wannan matsala za a iya maganceta ne idan mutanenmu suka samu ayyukan yi, shi ya sa ma dazu nake magana kan bayar da horo don koyon sana’o’i  (bocational Training ) suna da sha’awa kan haka, kuma a yanzu haka ma akwai kamfanonin kasar Jamus wadanda suke cikin Najeriya kuma su na da sha’awa kan kafa wuraren da za a koyawa matasa sana’a. Ba wai dole kowa duk wanda ya yi karatu dole sai ya je jami’a ba , mu ma da haka muke anan Najeriya, don da na san muna da ire-iren makarantun koyar da sana’o’in hannu, kamar a Gombe muna da makarantar koyon ire-iren wadannan sana’o’i na hannu da ake kira (Craft School), akwai kuma na kere-kere (Technical School), duk cikin wadannan makarantu ana koyon sana’o’i, kuma hakan yana nuna cewa ba wai in ba ka je jami’a ba ba zaka yi arziki ba, ko ba zaka sake koyon wani abu na rufin asiri ba ne, zaka samu komai na rufin asiri da gata da sana’arka, domin sana’arka ita ce mutuncinka, dole ne mu dawo da ire-iren wadannan makarantu, kuma kasar Jamus za ta iya taimaka mana mu dawo da irinsu.

 

Aminiya: Wata matsala dake addabar jama’a a yau ita ce matsalar nan ta sauyin yanayi? Ko me zaka ce kan haka?

Ambasada Tuggar: Wannan matsala na sauyin yanayi matsala ce da muke gani tana da nasaba da misali rashin zama lafiya a Arewa maso Gashin Najeriya, domin ba zaka shawo kan matsalar ba tilas sai ana noma ana shuka ana yin sana’o’i kafin ake iya rage matsalar, saboda haka ne na ce zamu yi kokari domin samun zaman lafiya mai dorewa a Najeriya, kamar wannan matsala na Boko Haram duk da cewa an ci karfinta, ai ka ga an sauya salo, da farko ba a yarda cewa hamada na daga cikin wannan matsala kuma warware wannan matsala tilas sai mun hada kai da makwabtanmu kamar kasashen Nijar, Chadi da Kamaru da sauran kasashen duniya, ka ga ai canjin salon Shugaba Muhammadu Buhari yana kama ragamar mulki in baka mance ba ko sati bai yi ba sai da ya ziyarci wadannan kasashe da muke makwabtaka da su na Nijar, Kamaru da Chadi, kuma insha Allahu zamu yi kokari domin ganin an samu zama lafiyan farko.

 

Aminiya: Ga lokacin zabe na shekara 2019 yana kara kunno kai, ko ya ya batun takara?

Ambasada Tuggar: To wannan dai da sauran lokaci, muna nan dai mun zuba ido tukuna sai mun ga abinda jama’a suka ce suna so mu yi.

 

Aminiya: Magoya bayanka dake Jihar Bauchi ne suka shirya maka wannan liyafa, ko wace irin fata Tugga ke da shi ga jihar?

Ambasada Tuggar: Fatana shi ne in ga Jihar Bauchi ta ci gaba, in ga Najeriya ta ci gaba, kuma in ga an samu zaman lafiya a Najeriya baki daya, kuma kun ga a makon jiya Shugaban kasarmu, Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya wanda duka muka cika da farin ciki, hakan kuma ya sa na sake tuna abin da ya faru a bara, inda nake so in yi mana nasiha, dukkanmu da muke rike da mukami a kujerar shugabanci na gwamnati da kuma sauran shugabanninmu, wato a irin wannan rana ne a shekarar da ta wuce wadansun da ba a san ko jami’ai ne ko ba jami’ai ba ne suka tafi daga nan Bauchi suka je Abuja suka dauko daya daga cikin wadanda suka shirya wannan taron karramawa, mai suna Musa Azare aka sace shi kamar yadda za a sace Naira a cikin aljihu, suka tafi da shi Bauchi, me aka shirya za a masa Wallahu A’alamu.

Wadda a lokacin mun yi iyakacin kokarinmu kuma mutane da dama sun bada gudummawa domin a sake shi. Alhamdu lilahi kuma aka yi nasara aka sake shi. Nasihar da zan yi anan ita ce misali da wasikar da Sayyidina Ali ya rubuta wa gwamnansa na kasar Misra wanda wasikar ta na nuna muhimmancin da ke dashi ga shugabanni su yi adalci ga talakawansu, ba kawai su maida hankali akan wadanda suke da wani hali ba ko attajirai, musamman talakawa, domin Alllah Madaukakin Sarki ya na nuna fishinSa akan shugabannin da suka tursasawa talakawa bayan kuma wannan nasiha ina mana ne baki daya har da ni kaina, da fatan Allah zai sa mu yi aiki da ita.

 

Aminiya: A karshe me za ka ce game da wannan matsayi da Allah Ya baka?

Ambasada Tuggar: Kamar yadda muka ji an yi jawabai da dama game da ita wannan kasa ta Jamus da muhimmancinta a tsakanin kasashen duniya, ita dai kasar Jamus babbar kasa ce a cikin kasashen turai, ita ce take kan gaba cikin kasashen turai, kuma tana da jihohi duk da cewa jihohinsu ba su kai namu yawa ba, jihohinsu guda 16 ne kawai, kuma manya manyan jihohi ne, kuma sun dade suna samun ci gaba, ta fannin ilimin kimiyya da kere-kere, kuma sai ya kasance muna da tsohuwar dangantaka tsakaninmu da su, zan yi kokari in ga yadda zamu amfana da su mu ci moriyarsu ta yadda zamu sami ci gaba a fannin raya ilmi, kiwon lafiya, aladu, bunkasa harkokin cinikayya da sana’o’i.