Burina matan karkara su samu ilimin zamani – Hassana Arkila

Honorabul Hassana Arkila ita ce tsohuwar shugabar karamar Hukumar bogoro da ke Jihar Bauchi a lokacin mulkin Malam Isa Yuguda.   Cikin tattaunawarta da wakilinmu, ta yi tsokaci game da muhimmancin karatun ’ya’ya mata sannan ta bayyana wasu daga cikin kalubalen da ta fuskanta a rayuwa. Ga yadda tattaunawar ta kasance kamar haka? Za mu so […]

Burina matan karkara su samu ilimin zamani – Hassana Arkila
Burina matan karkara su samu ilimin zamani – Hassana Arkila

Honorabul Hassana Arkila ita ce tsohuwar shugabar karamar Hukumar bogoro da ke Jihar Bauchi a lokacin mulkin Malam Isa Yuguda.   Cikin tattaunawarta da wakilinmu, ta yi tsokaci game da muhimmancin karatun ’ya’ya mata sannan ta bayyana wasu daga cikin kalubalen da ta fuskanta a rayuwa. Ga yadda tattaunawar ta kasance kamar haka?

Za mu so ki  gabatar da kanki?
Na yi matukar farin ciki bisa wannan dama da na samu.   Sunana Honarabul Hassana Arkila.   Ni ce tsohuwar shugabar karamar hukumar bogoro da ke Jihar Bauchi.   Na yi wata 10 ina rike da wannan mukami kafin na sauka.
An haife ni a shekara ta 1973.   Na fara makarantar firamare a garin Dashen- Yalwa daga sai na tafi makarantar Sakandare na GSS Tafawa balewa na kammala a shekara ta 1992 sai kuma na zarce zuwa makarantar Bakas da ke cikin garin Bauchi.
Daga nan sai na sake shiga makarantar Kwalejin Kimiyya da Fasaha (Federal Polytechnic)  inda na karanta sashin kudi, na kammala a shekara ta 1977.   A shekara ta 2003 na samu babbar dipiloma(HND) sannan kuma sai muka koma Jihar Gombe tare da maigidana da ma yana aiki ne a can.
A shekara ta 2012 na sake zuwa jJhar Borno inda na samu takardar dipiloma.
Tun ina karama nake kasuwanci domin na tashi na ga mahaifiyata tana soya kosai ni ma daga nan sai na shiga cikin harkokin sayar da gwanjo domin ba na kaunar zaman kashe wando a tsakanin al’umma.
Na taba tsaya wa takarar shugaban karamar hukumar bogoro amma cikin ikon Allah a shekara ta 2014 lokacin da aka zo nada shugabannin riko na kananan hukumomin Jihar Bauchi sai aka rubuta sunayen mutane uku ga Gwamnan Bauchi lokacin da ya samu sunayenmu sai ya dauki sunana ya b ani shugabar karamar hukumar bogoro.

Kina da ’ya’ya nawa a duniya?
Ina da ya’ya’ya bakwai, maza hudu mata uku.   Ina da shekara 41 a duniya bayan haka muna tare da mijina dan karamar hukumar bogoro ne. Kuma har yanzu ina cigaba da neman ilimi a sassa daban-daban na ciki da wajen Jihar Bauchi.

Idan kika ga mata suna zaune ba sa karatu, ba sa aiki, yaya kike ji a zuciyarki?
Gaskiya tsakani da Allah duk macen da take bukatar zama lafiya da mijinta, ya zamo wajibi ta nemi ilimin zamani domin sama da kashi 85 cikin 100 na maza ba sa kaunar zama da mace jahila domin duniyar yau ana alfahari da ilimi ne.
Saboda haka duk lokacin da na halarci taron mata babban abinda nake fada musu shi ne kada mace ta raina sana’a domin da rarrafe yaro kan tashi dole mace ta yi hakuri da matsalolin da za ta fuskanta a rayuwa.

Wadanne gudunmawa kika ba mata lokacin da kike shugabar karamar Hukumar bogoro?
Na yi abubuwa da dama ga mata lokacin da nake shugaban karamar hukuma saboda haka sai dai na takaita domin abubuwan suna da dimbin yawa.   Akwai mata da muka tallafa musu da jari tare da goya musu hanyoyin kiwon kifi a.  Sannan na tallafawa mata da zannuwa akalla dubu 5 a lokacin da nake shugabar karamar hukuma.
Akwai ‘yan banga sama da mutum 400 da muka kara musu alawus-alawus sannan kuma na gyara hedkwatar karamar hukumar bogoro tare da zuba sabbin kayayyaki irin na zamani, sannan na gyara hanyoyi masu dimbin yawa. Muna da ward goma sha uku a karamar hukumar kuma dukkansu mun yi musu aiki daidai gwargwado a lokacin mulkina.

Har yanzu kina jam’iyyar PDP?
Kamar yadda kowa ya sani ne ina daya daga cikin magoya bayan Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi kuma har yanzu ina PDP kuma ba zan sauya sheka ba, ni da PDP mutu-ka-raba, takalmin kaza.

Bashin nawa kika bari a karamar hukumar bogoro?
Na bar karamar hukumar bogoro ba a bi nta bashin ko sisin kwabo.  A lokacin da na shiga karamar hukumar na samu ana bin ta dimbin basussuka amma cikin ikon Allah duk na biya miliyoyin da ake bi bashi.

Yaya aka yi kike jin yaren Fulatanci?
Mahaifiya ta Bafulatana ce  sannan zaman da muka yi a Gombe shi ma ya kara min jin fulatanci, sannan yara kuma sun fi jin yaren uwa fiye da na uba.
Ina da alaka mai kyau tsakanina da masu unguwanni da sarakunan gargajiya da ke yankin karamar hukumar bogoro da sauran wadanda suke zaune a cikin garin Bauchi baki daya.
‘Yan sanda a jihar Bauchi idan suka ganni kamar za su dagani sama suke ji saboda yadda muke zaune lafiya da hukumomin tsaro.

Menene sakonki ga ‘yan mata masu tasowa?
Babban sakona ga ‘yan mata shi ne su yi hakuri da kalubalen rayuwa sannan kuma a dage sosai game da neman ilimin zamani.   Babu wata al’umma da za ta samu cigaba sai tana da ilimi domin shi ne sinadarin da ke jawo cigaba cikin hanzari.
Don Allah matasa a guji dabi’ar zama a bakin hanya ana sai ka yi, duk kasar da ta samu cigaba sai da matasanta suka bada kulawa ta musamman watau a bangaren yin karatu da kuma na sana’a.

Kina ganin PDP za ta sake farfadowa a Najeriya?
Kamar yadda aka sani jam’iyyar PDP ta fadi a zaben shekara ta 2015 amma ina

tabbatar maka da cewa za ta sake farfadowa domin har yanzu talakawa suna kaunar PDP. Allah Ya kai mu zaben 2019, adawa a siyasa tana da amfani amma ba kowa ne ya san haka ba.

Wasdanne abubuwa kike ganin ya kamata gwamnoni su yi wa matan karkara?
Babban abinda nake so gwamnonin Najeriya su yi wa matan karkara shi ne a taimaka musu da jari.   Bayan haka gwamnati ta bada kulawa ta musamman wajen gina makarantu a karkara domin har yanzu akwai dimbin mata wadda ba su iya karatu da rubutu ba.
Bayan haka ina fatar alheri ga gwamnan Jihar Bauchi Barista Mohammed Abubakar kuma ya sani mata da dama sun bada gagarumar gudunmawa a lokacin zaben 2015, saboda haka suna bukatar tallafi.
Akwai matasa masu yi wa kasa hidima NYSC na ba su tallafi lokacin ina ofis da sauran kungiyoyi da ke yankin karamar hukumar bogoro.   Muna fatan alheri ga kowa da kowa.

Wadanne matsaloli matan Jihar Bauchi suke fuskanta a halin yanzu?
Babbar matsalar da matan Jihar Bauchi suke fuskanta a halin yanzu shi ne da yawa daga cikinsu suna fama da matsanaicin talauci da rashin aikin yi. Bayan haka muna da mata da dama wadanda mazajenzu suka rasu wasu daga cikinsu an bar musu ‘ya’ya marayu masu tarin yawa kuma da kyar suke cin abinci sau biyu a rana. Matan karkara suna fama da bakin talauci a Najeriya ba ma Jihar Bauchi kadai ba saboda haka muna fata gwamnati za ta kawo musu daukin gaggawa.
Na shiga siyasa ce domin na bada gudunmawa ta ga ‘yan uwana mata domin na san fiye da kashi 85 cikin 100 na matsalolin matan karkara saboda ni ma daga karkarar na fito.
Duk abinda na samu a rayuwa babban burina shi ne na kyautatawa mata domin na san halin da suke ciki.

Daga karshe menene sakonki?
 Sakon shi ne na yi matukar farin ciki bi sa wannan dama da na samu a wannan jarida ta Aminiya, kuma na gode da damar da kuka ba ni har na fadi ra’ayoyina a game da mata musamman a kan matsalolin da ke ci musu tuwo a kwarya.  Na gode.