Burina na shahara a duniya – dan wasan barkwanci
Wani matashi da ya yi fice a fannin wasan barkwanci na zamani a Jihar Legas, mai suna Abdullahi Muhammad ya ce burinsa shi ne sunansa ya karade duniya.dan wasan wanda ake yi wa lakabi da Daddy, dan kimanin shekaru 32 da haihuwa ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a ofishinsa da […]
Wani matashi da ya yi fice a fannin wasan barkwanci na zamani a Jihar Legas, mai suna Abdullahi Muhammad ya ce burinsa shi ne sunansa ya karade duniya.
dan wasan wanda ake yi wa lakabi da Daddy, dan kimanin shekaru 32 da haihuwa ya yi furucin ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a ofishinsa da ke unguwar Kwakwa-Uku a cikin karamar Hukumar Agege.
Ya ce: “Na fara kamar da wasa tun lokacin mulkin Shugaban kasa Ibrahim Babangida, lokacin akwai wani abokina da yake ba mu labarin bandariya, sai ni ma na rika kwaikwayarsa, ni ma nake bayar da labari, idan na bayar sai nawa labarin ya fi nasa bandariya. Sai wata rana wani abokina ya auri wata yarinya, sai muka je wurin walima, mutane suka fara watsewa, sai wasu daga cikin abokanenmu suka roke ni na zo na nishadantar da mutane don kada kowa ya watse daga wurin walimar. Shi ke nan sai na fara, mutane suka ji dadi; shi ke nan sai kawai idan za a yi biki mutane su gayyace ni. Gaskiya ni burina ya zama na shahara a duniya, ya zamanto na yi fice fiye da wadanda suka yi fice a yanzu a harkar barkwanci.”
Ya ci gaba da cewa: “Kuma ina da burin a ce ga ni ga shahararren mai barkwancin nan mai suna Basket Mouth muna yin barkwanci tare. Kuma ina da burin na kafa kamfanin barkwanci da jagoranci a wurin biki da taruka da sauran harkokin da suka jibinci harkar sadarwa.”
Sai dai Daddy ya bayyana cewa ya samu nasarori da yawa wadanda suka hada da samun alaka da mutane daban-daban daga ciki da wajen jihar Legas.
Duk da nasarorin da ya samu ya ce bai dogara kawai ga harkar barkwanci ba saboda yana da sana’ar dinki da yake yi.
‘Gaskiya ban dogara kawai da harkar barkwanci ba don ni kwararren tela ne wanda ya yi fice a harkar dinkunan kayan yara da manya. Ita harkar barkwanci ranaku biyu kawai nake yi.
Ranakun Asabar da Lahadi kawai nake yi saboda mafiyawan shirye-shiryen aure ko suna a ranakun Asabar da Lahadi ake yi amma sauran ranakun ina tafiya shagona na dinki ne’. In ji shi.
Tare da haka Abdullahi ya bayyana cewa zai iya barin sana’arsa ta dinki ya kama barkwanci gadan-gadan idan har ya fi samun alheri a cikinta.
Ya ce a cikin shekaru fiye da goma da ya yi yana harkar barkwanci ya rika gamuwa da kalubale iri-iri.
Inda Allah ya rika tsallakar da shi duk wata matsala da ta taso masa ba tare da wani jinkiri ba.