Burina na yi suna a harkar fim – Maryam Ali

Aminiya ta sami tattaunawa da wata matashiyar jaruma mai suna Maryam Ali wacce take sha’awar ta yi fice kamar yadda ’yan fim mata suka yi suna a harkar fina-finan Hausa. Domin ta cimma burinta ne ya sa ta shiga kungiyar masu shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakabi da ‘AYA Production’ da ke Legas.Takaitaccen […]

Burina na yi suna a harkar fim – Maryam Ali

Aminiya ta sami tattaunawa da wata matashiyar jaruma mai suna Maryam Ali wacce take sha’awar ta yi fice kamar yadda ’yan fim mata suka yi suna a harkar fina-finan Hausa. Domin ta cimma burinta ne ya sa ta shiga kungiyar masu shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakabi da ‘AYA Production’ da ke Legas.
Takaitaccen tarihinta:
An haife ni a unguwar Yanafaja da ke cikin karamar Hukumar Alimosho da ke Jihar Legas. Na yi makarantar firamare a Yanafaja daga nan na shiga sakandire ta Agege. Shekarata 18 a duniya. Ni memba ce a kungiyar fim ta ‘AYA Production.’ Ina jin yarukan Hausa da Yarabanci da kuma Turanci sosai. Ina da burin na ci gaba da karatu mai zurfi zuwa jami’a.
Dalilinta na shiga kungiya:
Na shiga kungiyar AYA Production ne saboda idan za su yi fim su rika sanya ni ina fitowa a ciki. Kuma na shiga wannan harka ne saboda sha’awar da nake da ita na yin suna da fadakar da jama’a da kuma ilimantar da su dangane da harkokin rayuwa.
Matsayin da ta fi so a fim:
Ka san kowa da burin da yake so ya cimmawa. Ni dai na fi so na fito jaruma. Ina so na rika yin abu kamar fitacciyar jaruma Nafisa Abdullahi da Fati Ladan. Domin Nafisa tana da basira kuma idan ka lura da yadda take taka rawa a fim, babu shakka zai burge ka kwarai da gaske. Ita kuwa Fati Ladan Allah ya ba ta hazaka da kwarewa ta musamman. Ita ma idan ka duba yadda take abubuwa a fim za ka ga cewa tana yin abin da ake bukata. Shi ya sa na dauke su tamkar wadanda nake kwaikwayo a harkar fim.
Ra’ayinta game ’yan fim:
Ka san a duniyar nan babu abin da za ka yi ka burge kowa da kowa. Dole ka sami wadanda za su kushe ka. Koda a cikin ’yan uwanka ne sai ka sami wanda zai rika kushe ka. In dai zuciyarka a tsarkake take, to ni duk abin da mutane za su ce a kaina ba zai yi tasiri ba kuma ban damu ba saboda na san abin da nake yi. Kuma don mutane suna ganin ’yan fim mata na fitowa tare da maza a cikin fim, ai wannan ba zai sa a ce su lalatattu ba ne.
Yada za ta fuskanci kalubale:
Ka san an ce yadda ka gabatar da kanka a wurin jama’a haka za su dauke ka. Idan a matsayinki na mace kika gabatar da kanki a matsayin ’yar iska ko kika yi shiga ta rashin mutunci, to haka za a dauke ki. Amma idan kika yi shigar mutunci, to babu shakka za a dauke ki mai mutunci. Wani lokaci su matan ne suke janyo wa kansu matsala saboda surutun da suke yi. Idan abu ya faru sai a rika yayata shi. Idan bai faru ba ma sai a rika kirkiro shi ana fada wa kawaye. To ka ga dole a rika kara wa abin gishiri.
Dangartakata da iyaye:
Gaskiya  iyayena sun ba ni goyon baya dari bisa. Dalili shi ne, ni iyayena masu fahimta ne saboda duk abin da na kawo musu sukan yi nazari a kansa. Idan suka ga ba matsala, sai su kyale ni na yi. Musamman mahaifina ba shi da matsala a kan haka domin ya san yadda nake shi ya sa yake ba ni goyon baya. Mahaifina malami ne to ka ga idan da a ce akwai illa a ciki ba zai kyale ni ba. Mahaifiyata da yayyena duk sun yarda kuma sun ba ni goyon baya dari bisa dari. Saboda haka da yardar su na shiga.
Burinta a fim:
kodayake ba wanda zai ce ba ya son kudi amma ni na fi son na yi suna, a rika kwatance da ni ta yadda mutane za su rika yabawa da ni suna yin koyi da ni kamar yadda ake koyi da wasu fitattaun ’yan fim a kasa da duniya baki daya.
Yadda za a gyara fim:
Gaskiya akwai gyare-gyare da dama. Amma abin da ya fi damuna shi ne yadda daraktoci suke shirya fim. Da farko zai ba da ma’ana amma daga karshe sai ya zama bai ba da wata ma’ana mai muhimmanci ba. Ya kamata fim farkonsa da karshen ya kare da ma’ana guda daya. Domin tsayawa a kan jigo daya yana da muhimmanci a harkar fim saboda ta haka ne mutane za su fahimci sakon da ake so a isar musu.