Burina tallafa wa al’ummar Lere – Injiniya Ahmed
Dan takarar kujerar Majalisar Wakilai daga mazabar Lere da ke Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar APC, Injiniya Ahmed Munir ya ce babban burinsa, shi ne tallafa wa al’ummar mazabar. Injiniya Ahmed Munir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida, a garin Saminaka, inda ya ce a kan wannan kuduri nasa […]
Injiniya Ahmed Munir
Dan takarar kujerar Majalisar Wakilai daga mazabar Lere da ke Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar APC, Injiniya Ahmed Munir ya ce babban burinsa, shi ne tallafa wa al’ummar mazabar.
Injiniya Ahmed Munir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida, a garin Saminaka, inda ya ce a kan wannan kuduri nasa ne ya sa, tun daga lokacin da ya fara yakin neman zaben wannan kujera ya yi rijiyoyin burtsatse a dukan mazabun Karamar Hukuma Lere 11.
Kuma ya ce ya tallafa wa marasa lafiya da suke fama da cututtukan zazzabin sauro da taifod da hawan jini sama da mutum dubu 5, tare da ba su magunguna kyauta.
Ya ce wannan tallafi da yake bayarwa yana bayarwa ne ga al’umma ba tare da bambancin jam’iyya ba. Don haka al’ummar mazabar suke ba shi goyon baya, ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba.
Injiniya Munir ya ce ya fara yakin neman zabe a cikin kwanciyar hankali ba tare da wani rikici ba. “Wannan yakin neman zabe da muke yi shi ne na farko a wannan mazaba, da ake yi ba tare da wani tashin hankali ba. Ba ma amfani da ’yan banga don cutar da matasa da sauran al’umma. Domin manufofinmu masu kyau ne’,” inji shi.
Ya nuna godiyarsa ga al’ummar karamar hukumar kan irin goyon bayan da suke nuna masa. Ya ce babu abin da zai ce wa al’ummar mazabar, kan goyon bayan da suke nuna masa, sai godiya.
Kuma ya tabbatar wa al’ummar mazabar, cewa zan rike amanar da suka damka masa.Daga nan sai ya yi kira ga dukan magoya bayansa su ci gaba hakuri da nuna juriya, kan abubuwan da ake yi musu. Ya ce mai nasara ba ya fada, don haka su ci gaba da hukuri da nuna juriya domin suna tare da nasara.