Burinmu mu farfado da martabar masarautun Hausa da fim din Juyin Sarauta – Furodusa Balaraba Ramat Yakubu

A tattaunawarmu da marubuciya kuma furodusar fina-finai, Hajiya Balaraba Ramat Yakubu ta yi bayanin irin kalubalen da ta sha wajen shirya fim din Juyin Sarauta, wanda ya danganci sarauta, inda ta hasko yanayin masarautar Hausa shekara 100 da ta gabata. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Game da wannan fim naki na Juyin Sarauta, ko za […]

Burinmu mu farfado da martabar masarautun Hausa da fim din Juyin Sarauta – Furodusa Balaraba Ramat Yakubu
Burinmu mu farfado da martabar masarautun Hausa da fim din Juyin Sarauta – Furodusa Balaraba Ramat Yakubu

A tattaunawarmu da marubuciya kuma furodusar fina-finai, Hajiya Balaraba Ramat Yakubu ta yi bayanin irin kalubalen da ta sha wajen shirya fim din Juyin Sarauta, wanda ya danganci sarauta, inda ta hasko yanayin masarautar Hausa shekara 100 da ta gabata. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Game da wannan fim naki na Juyin Sarauta, ko za ki yi mana bayani takaitacce game da shi, wa ya rubuta labarinsa kuma me ya ba ki kwarin gwiwa kika tsara shi?
Shi dai fim din Juyin Sarauta, labarina ne, ma’ana ni na rubuta shi kuma ni na tsara shi yadda zai kasance a fim. Labari ne na wata masarauta a kasar Hausa, shekara 100 da ta wuce. Dalilin da ya sanya aka kirkire shi, saboda muna son maida hankali ga yin fina-finai na tarihi, wadanda suka kunshi al’adunmu na Hausa, maimakon irin wadanda ake yi na soyayya da sauransu. Wannan shi ne dalilin da ya sanya aka shirya fim din Juyin Sarauta.
Mun samu labarin cewa shi wannan fim ya bambanta da tsarin sauran fina-finan Hausa, wajen shiryawa da sauransu, ko kimanin nawa aka kashe wajen shirya shi kuma wadanne bambance-bambance ya kunsa tsakaninsa da sauran fina-finan Hausa?
Gaskiya lokacin da muka gama tsara daftarin fim din, muna neman ina za mu dauki shirin, sai da muka zagaya jihohi kimanin guda bakwai. Mun je Jigawa da Jos da Daura da Katsina, Kano nan ma mun duba amma ba mu samu ba. Sarkin Dutse har fadarsa ya ba mu, muka duba amma ba mu samu gamsuwa ba. Abin da dama muka ci karo da shi, shi ne, duk fadojin sarakunan da muka duba, an riga an shafe su da siminti da kuma fenti, don haka ba za su dace da fadar sarkin da ya yi zamani shekaru dari baya ba, domin a lokacin babu siminti kuma babu fenti irin na zaanin nan. Don haka muka hakura, muka zo muka karya lissafinmu, muka gina gidan sarautar da ya dace da fim din, mun gina gidan sarkin a wani kauye da ake kira Iyatawa, danhassan, karamar Hukumar Rano, Jihar Kano, kuma gidan nan da muka gina yana nan har yanzu. Kuma fadar sarkin danhassan din, ya yarda kuma ya ba mu dama muka sassakke simintin da fentin, muka maida ta ta kasa. A yanzu haka mutane na nan masu aiki, suna mayar wa fadar tasa siminti da fentin kamar yadda muka same ta.
Ta ina kuke ganin za ku dawo da dinbin kudaden da kuka kashe a wannan fim, ganin irin kalubalen da ke fuskantar fina-finan Hausa a wannan lokaci?
Gaskiya kam wannan abin tunani ne, to amma yadda muke kiran fim din da sabon salo, saboda ya zama shi ne sabon salo a harkar fina-finan Hausa, to muna ganin abubuwan da muke so mu saka a ciki, idan ya fito, da inda muke son mu nunnuna shi, muna rokon Allah Ya sa abin da muka kashe ya dawo har mu ci riba.
Wani al’amari da ya dauki hankali shi ne, yadda kika dauki tsofaffin ’yan wasan da ba a cika jinsu a wannan zamani ba, kin hada har da marubuta da sauransu. Ko wace hikima ce ta sanya kika yi haka?
Saboda labarin fim din namu ba irin na yanzu ba ne, ba labari ne na rawa da waka ba kuma mun yi kokari mun saka mutane da suka dace. Kowane mutum da ka ga mun sanya a fim din nan, mun tabbatar cewa ya cancanta ne, babu son rai babu son zuciya, babu kuma cewa wane nawa ne, wane ba nawa ba. Wannan shi ne dalilin da ya sanya muka zabi wadannan ’yan wasa kamar yadda kuka gani.
Baya ga niyyar fayyace martabar sarauta a kasart Hausa, ko akwai wasu darussa da fim din ke dauke da su?
Ai Juyin Sarauta labari ne game da mata da bayi da kwara-kawarai da ’ya’yan sarki, yadda suke tafiyar da al’amuransu a cikin gida, ba wai fim ne na sarautar ita kawai a fada ba. Wannan shi ne bambancin, ba kamar yadda mutane suka dauka ba, idan an ce sarauta, an dauka duk a cikin fada ake yin komai a gama. A’a, mun ba da hankali ne ga rayuwar al’amuran sarautar gaba daya, misali, shi sarkin idan ya fito fada daga gida, suwa ke juya shi ko kuma suwaye ke juya sarautar da yake zaune nan? To mu sai muka shiga gidan, muka dauko labarin matan da ’ya’yan da kwara-kwaransa, nan muka bai wa karfi, ba wai cikin fadarsa ba. Amma kuma mun shiga fadar ma mun yi abubuwa, sai dai wancan shi ne jigon labarin.
Kasancewarki marubuciyar labaran kirkira, shin kin tsara labarin fim din nan zai fito a littafi bayan fim din ko kuwa?
A’a, ban yi tunanin tsara shi zuwa littafi ba, duk kuwa da cewa mutane suna cewa ya kamata a mayar da shi littafi, domin mutane za su so karantawa, kasancewar akwai bambanci tsakanin fim da littafi.
Kin yi wasu fina-finan a baya kafin shi wannan Juyin Sarauta, shin ko guda nawa ne kika yi a baya?
Farko dai kamfanin FILAPS sun dauki littafina a nan, Alhaki Kwikwiyo, sun maida shi fim, sai kuma ni da kaina na yi wani fim din mai suna Wata Shari’ar Sai A Lahira, amma shi ba littafi ba ne, labari ne kawai na yi na fim din. Sannan na fassara littafina daya, Ina Sonsa Haka, shi ma na yi fim dinsa. To sai kuma yanzu da na yi Juyin Sarauta.
Idan kika kwatanta wadancan fina-finan naki na baya da shi wannan na yanzu, wadanne canje-canje ko kalubale kika fuskanta?
E, to gaskiya, lokacin da na yi fim dina na farko, Wata Shari’ar Sai A Lahira, na sha wuya, na sha kalubale saboda shi ne fim dina na farko. Na sha ‘kan ta waye’ domin sai da na je banki ma na ciwo bashi, na zo aka karasa shi. To a wannan ina ganin gaskiya na sha kalubale. Shi kuma fim din Ina Sonsa Haka, ban sha wata wahala ba sosai, ganin cewa na goge saboda wancan fim dina na baya. Amma a wannan fim na Juyi Sarauta, ka ga mun samu tallafin kudi daga Ma’aikatar Kudi ta Gwamnatin Tarayya, a wani shiri nasu na bayar da tallafi ta wannan bangare, sannan mun tafi bankin Tallafa wa Masana’antu mun ranto kudi kuma duk wannan fim din ya lakume su, har yanzu kuma lissafi muke yi, domin mu tantance mu gano nawa muka kashe. Muna cikin lissafi sai wani kuma ya zo da takarda, ya ce ga shi an kashe kaza ko za a yi kaza, da sauransu. Don haka har yanzu muna nan muna tattara bayanan nawa ne wannan fim ya lakume, idan mun kammala za mu shaida maku.
Idan muka yi la’akari da cewa ke Bakanuwa ce, lokacin da kike rubuta labarin fim din nan, ko kin saka wata masarauta a zuciya, ma’ana ko za mu ce masarautar Kano kika kalla a shekara 100 da suka gabata?
A’a, wallahi ba masarautar Kano ba ce saboda idan ka kalli labarin ma ba irin na masarautar ba ne. Bincike ne na yi yadda masarautar Hausa take shekaru dari, na yi la’akari da masarautu daban-daban, na jawo labarunsu na harhada na tayar da labari guda daya da ya wakilci dukkan masarautun kasar Hausa.
Bayan kin kammala rubuta labarin, ko kin mika wa malaman tarihi ko masana sun dan kwankwashe shi kafin a mayar da shi fim?
E, gaskiya sun dan kwankwashe shi sosai saboda kafin ma mu kai ga zuwa wurin masana, mu da kanmu mun fara kwankwasarsa. Ka ga na farko sai da labarin ya yi wajen shekara biyu a hannun Sadik balewa, ganin cewa bai yi komai a kai ba, na kuma kiran Nazir da Babinlata da Bashir Mudi Yakasai da Ado Ahmad da Tijjani Ahmad da sauransu, wajen mutum takwas, muka zo muka kuma rusa shi, aka kuma tantance shi. Daga nan kuma aka sake kiran wasu daga cikinsu, muka hadu da Nasiru Wada Khalil, wanda shi ma masani ne na al’adun masarautu. Tare da shi aka tantance, aka kara gyara labarin. Sannan kuma mun shiga intanet, muka binciko irin kayan da ake sanyawa da irin abincin da ake ci da sauransu, shekaru dari da suka gabata. Wannan ya ba mu wahala da yawa, domin shi kansa labarin fim din sai da ya shekara uku ana ba-ni-in-ba-ka da shi, kafin daga bisani Allah Ya taimake mu aka samu guda daya tatacce. Da farko mun yi shawarar mu yi shi kashi-kashi, sai mu ka ga kudin da zai ci da yawa, shi ne muka bar shi a guda daya. Alhamdu lillahi, mun samu labari, mun samu wuraren daukar fim din.
Daga fara tunanin rubuta labarin fim din nan zuwa yanzu da aka kammala daukar shi, shekara nawa ke nan?
Shekara uku ke nan muna yinsa.
A matsayinki na furodusar fim din nan, wane sako ke gare ki ga al’umma dangane da abin da za su tsimaya ga fim din Juyin Sarauta?
Sakona ga al’umma shi ne, fim din Juyin Sarauta ya zo da sabon salo a tsarin fina-finan Hausa kuma alal hakika mun kashe kudi sosai wajen shirya shi. Rokona da nake ga masu shirya fina-finan Hausa irina shi ne, don Allah mu maida kai mu rika shirya fina-finai da za su farfado mana da al’adunmu da addininmu, koda a wace kasa za a kalle shi, a fahimta da cewa al’adunmu ne kuma addininmu ne ake kallo. Haka kuma mu rika gudanar da binbcike kafin mu shirya fim, ba kawai mutum ya tashi da ka ya shirya fim na tarihi ba tare da bincike ba. Akwai wani fim namu da aka kai kasashen waje, muna takamar cewa shi ne fitacce, amma Turawa suka ce ba za su kalla ba saboda ba al’adunmu ba ne a ciki. Ga sauran mutane kuma da suke jiran fim din, ina yi masu albishir da cewa za su ga sabon salo da canji mai kayatarwa, wanda zai gamsar da su. Kuma daga nan mun ci gaba ke nan da shirya fina-finai na tarihi da al’ada. Ina rokon masu kallo da su sanya kudi su saya, yadda za mu maida kudinmu kuma mu ci riba, domin mu samu kwarin gwiwar ci gaba da shirya wasu nan gaba.