Burinmu mu mayar da makarantar Al-Bayan zuwa jami’a – Sheikh Suleiman
A kwanakin baya ne kungiyar Al- Muntada Al Islami da take da fitacciyar makarantar nan ta Al-Bayan da ke garin Jos, Jihar Filato, ta sake nada Daraktan Cibiyar Bunkasa Ilimi da Wayar da kan Jama’a (AWEDI) Sheikh Muhammad Suleiman Abu Suleiman a matsayin shugaban makarantar. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana kudurinsa na daukaka makarantar […]
A kwanakin baya ne kungiyar Al- Muntada Al Islami da take da fitacciyar makarantar nan ta Al-Bayan da ke garin Jos, Jihar Filato, ta sake nada Daraktan Cibiyar Bunkasa Ilimi da Wayar da kan Jama’a (AWEDI) Sheikh Muhammad Suleiman Abu Suleiman a matsayin shugaban makarantar. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana kudurinsa na daukaka makarantar zuwa jami’a:
Aminiya: Me za ka ce kan sake nada ka shugaban makarantar Al-Bayan da ke nan Jos?
Sheikh Suleiman: To, ita wannan makaranta ta Al-Bayan, makaranta ce da na fara tunanin kafa ta, tun lokacin da nake karatu a Jami’ar Musulunci ta birnin Madina a 1990. A lokacin akwai kanena Injiniya Sani Saleh wanda yanzu darakta ne a hukumar tashoshin jiragen ruwa ta kasa. A lokacin yana karatu a kasar Italiya, sai na aika masa cewa ya zana mini wata makaranta da za ta kunshi ajujuwa da gidajen kwanan dalibai da ofishohin gudanarwa. Nan take ya zana ya aiko mini. Bayan haka sai Allah Ya sa muka hadu da marigayi Alhaji Hussaini Magaji wanda ya zo Umara, sai ya ce min akwai wani fili a Dutse-Uku a garin Jos, in ya koma Najeriya zai saya mana don mu gina
wannan makaranta. Da ya dawo gida ya saya mana filin ya rubuta takarda ya aika mana da ita. A lokacin da na gama karatu da nake yi a Madina, na dawo gida Najeriya a 1994, sai kuma muka samu Alhaji Rabo Salihu Musa wanda ya gina wata makaranta a Rock Heaben da ke nan Jos, ya dauke ni a matsayin shugaban makarantar.
Kafin nan kungiyar Al- Muntada Al-Islami ta shigo Najeriya a wannan shekara. Sai aka ce na je mu gana da shugabanninsu. Da na je muka gana da su, suka ce suna son su yi ayyuka na taimaka wa al’umma, kamar gina makarantu da masallatai da haka rijiyoyi da sauransu.
Sai na ce musu akwai wata makaranta da wani bawan Allah ya gina sabuwa a Jos da aka ba ni shugabancinta, su je su roke shi ko zai ba su ita. Saboda haka muka zo muka same shi muka yi masa magana ya amince ya bayar da makarantar. Wannan makaranta ita ce ainihin bude makarantar Al-Bayan. Bayan haka, sakamakon rikicin Jos da aka yi a shekara ta 2001, sai muka taso daga wannan makaranta ta Rock Heaben, muka dawo Unguwar Dutse Uku muka gina makarantar Al-Bayan a wannan fili da marigayi Alhaji Hussaini Magaji ya saya mana. Na yi shekara tara ina rike da makarantar a matsayin shugaba. Daga nan na zama ko-odinatan shirin yi wa masu cutar makanta magani na kungiyar Al- Muntada Al-Islami a nan Najeriya. Na yi shekara biyu ina gudanar da wannan shiri. Sai ofishin kungiyar da ke Kano ya bukaci in na yarda, na koma Kano na zama daraktan bangaren jin dadin al’umma na kungiya a babban ofishinsu da ke Kano. Sai na ce wa kungiyar wa zan bar wa makarantar, sai suka ce za su turo wani daga kasar Sudan ya zama shugabanta. Sai na ce musu lalacewarmu ba ta kai sai an dauko mana wani daga waje ba. Don haka na ce zan bar wa Malam Muhammad Nazifi ya rike a matsayin shugaba, sai Malam Isma’ila a matsayin mataimaki. Haka aka yi na ba su makarantar, don su rike na tafi wancan aiki da aka ba ni da manufar idan na dawo za mu ci gaba da aiki.
Da na tafi Kano na kama wannan aiki har na tsawon shekara uku, sai na ajiye aikin na dawo nan Jos na kafa Cibiyar Bunkasa Ilimi da Wayar da Kan Jama’a (AWEDI) a shekara ta 2006. To, a yanzu wannan kungiya ta Al- Muntada Al-Islami sun mayar da hankalinsu zuwa ga kasashen Turai. Don haka suka nemi wadanda suka kafa irin wadannan makarantu na Al-Bayan suka mika musu. Sakamakon wannan mataki da suka dauka a wani taron kara wa juna sani da muka yi da su a kasar Malesiya, suka ce sun dawo mini da wannan makaranta ta Al-Bayan. Kuma sun aiko min da takarda kuma zan ci gaba da gudanar makaranta kamar yadda aka kafa ta.
Aminiya: To, yaya ka ga yadda makarantar ta kasance bayan da ka bar ta zuwa wannan lokaci da ka dawo?
Sheikh Sulaiman: To, a gaskiya daga lokacin da na bar makaranta zuwa yanzu da na dawo ta bunkasa. Amma kuma an saba ainihin yadda muka fara gudanar da ita. Saboda a lokacin da muke rike da makarantar, yara ’yan kadan ne a makarantar, saboda muna samun tallafi. Amma da muka daina samun tallafi sai aka sanya yara da dama a makarantar don a rika samun kudin da za a rika biyan malamai. Wannan ya jawo ilimin makarantar ya yi kasa, tarbiyyar makarantar ta yi kasa, saboda haka jama’a ba sa farin ciki da wadannan abubuwa da suka faru a makarantar. Amma yanzu za mu duba mu ga yadda za mu warware wannan matsala, domin ba neman kudi ne manufar kafa makarantar ba. Saboda haka dawo da wannan makaranta da aka yi zuwa gare ni a yanzu, da ma mu ne muka yi aikin ginata, za mu daukaka ta tashi daga inda take ta koma jami’a wannan shi ne babban burinmu.
Aminiya: Ganin sunan da makarantar ta yi, a takaice wadanne irin nasarori ne kake ganin ta cimma?
Sheikh Suleiman: A gaskiya wannan makaranta ta samu nasarori masu yawa, domin daliban da makarantar ta yaye, wasu sun zama manyan daraktoci a Nijar, wasu suna koyarwa a jami’o’i a kasashen Ghana da Benin da Togo da Sudan da Malesiya, wasu sun shiga ayyukan ’yan sanda da soja, wasu sun zama lauyoyi wasu sun zama limamai a Najeriya da sauran kasashen da muke makwabtaka da su. Don haka muna kira ga irin wadannan tsofaffin dalibai da makarantar ta yaye, su zo su ba da gudunmawarsu wajen dada ciyar da makarantar gaba.
Aminiya: To, a takaice wadanne muhimman abubuwa za ku sanya a gaba a makarantar?
Sheikh Suleiman: Babban abin da za mu sanya a gaba a makarantar shi ne dawo da tarbiyyarta ta asali kamar yadda na fada a baya. Yara su rika girmama na gaba da su. Kuma za mu tsaya muga cewar ana horar da malaman makarantar ta hanyar tura su zuwa karo ilimi. Kuma muna son kafin mu zama jami’a mu bude wani reshe na samun takardar shaidar ilimi ta kasa (NCE) a makarantar, ta yadda za mu rika horar da kwararrun malamai da za su rika koyarwa. Wadannan su ne muhimman abubuwan da za mu sanya a gaba, domin dawo da martabar wannan makaranta.
Aminiya: To, wane sako ko kira kake da shi ga al’umma dangane da wannan makaranta?
Sheikh Suleiman: To, ina kira ga al’ummar Musulmi da sauran wadanda suka taimaka aka kafa makarantar, su ci gaba da taimakawa don ganin makarantar ta dawo yadda take a baya.