Burinmu mu zama kan gaba wajen fitar da dinkakkun kaya – Ladaco Global Enterprises

Ladaco Global Enterprises da ke Kaduna, wani kamfani ne da wadansu matasa da suka kammala karatun digiri suka bude suke gudanar da shi tare da zamanantar da sana’ar dinki. A zantawarsa da Aminiya, Abdullahi Abubakar  Ladan ya bayyana yadda suke amfani da kafofin sadarwa na zamani wajen tallata hajarsu:   Ta yaya kuka fara kokarin […]

Burinmu mu zama kan gaba wajen fitar da dinkakkun kaya – Ladaco Global Enterprises

Ladaco Global Enterprises da ke Kaduna, wani kamfani ne da wadansu matasa da suka kammala karatun digiri suka bude suke gudanar da shi tare da zamanantar da sana’ar dinki. A zantawarsa da Aminiya, Abdullahi Abubakar  Ladan ya bayyana yadda suke amfani da kafofin sadarwa na zamani wajen tallata hajarsu:

 

Ta yaya kuka fara kokarin zamanantar da sana’ar dinki?

Kamfanin Ladaco, an kafa shi ne a shekarar 2015. Amma kafin nan, ya kasance yana aiki ne a bangaren abin da ya shafi dinkin kaya da zannuwan gado da jakunkuna da kuma dab’i. A shekarar 2014, kamfanin ya yi kokarin bunkasa ta hanyar saye da sayar da turamen zannuwa da labulen daki da makamantasu. Lura da yanayin rashin aikin yi a kasa musamman ga matasa da suka gama jami’a, sai muka yi tunanin amfani da iliminmu na jami’a domin ganin mun sabunta tare da zamanantar da sana’ar ta yadda za ta zama abar sha’wa kuma mu taimaka ma wadansu wajen sama musu aikin yi. Hakan ya sa muka yi rajista da Hukumar CAC da wasu hukumomi, sannan muka dauki sabon salo na amfani da yanar gizo a matsaayin hanyar tallata hajojinmu. Mukan dinka kaya na zamani sannan mu sayar wa ’yan kasuwa da daidaikun mutane.

Me ya sa kuka yi tunanin zamanantar da dinkin?

Babban dalilin shi ne mu rike kuma mu gyara sana’ar da muka gada kuma muka koya wajen iyayenmu. Mahaifiyarmu ta kasance tela ce, mahaifinmu kuma kwararren mai dabi’i ne. Sai ya kasance yanzu mukan dinka kayan sawa, kuma mu yi rubutu a kansu, sai su kasance kamar kayan da ake shigo da su daga kasar waje. Hakan ya sa muka mallaki injunan dinki na zamani da kuma na dab’i domin cimma manufarmu ta zama kan gaba a cikin masu fitar da dinkakku kaya zuwa kasashen waje daga Najeriya.

Yaya kuke yin aikinku a takaice?

Muna dinka kayayyakin sawa ne na yara da manya, kuma maza da mata. Sannan muna dinka zanen gado da labule da hulunan sawa na mata wadanda su ne suka fi karbuwa wajen abokan huldarmu. Ina da yakini a fadin Najeriya idan ba mu zo na daya ba, to ba za mu wuce na uku ba a cikin jerin masu fitar da dinkakkun hulunan mata. Sannan muna yin jakunkuna da takalma na yara da manya da sayar da kayan ado kamar abin wuya da ’yan kunne da makamantansu. Mukan dinka kaya ne, idan an gama a bincika, idan ba wata matsala sai mu mika bangaren dabi’i su yi rubutu a kai, ko kuma a kai bangaren da za su goge sannan su sanya a leda wacce ke dauke da sunan kamfani sai su manna katin kamfaninmu a jiki. Yadda kasuwancinmu yake kuma muna amfani ne da kafafen sadarwa kamar Whatsapp da Facebook da Instagram da twitter da sauransu wajen tallata kayanmu. Hakan ke sa mutane daga sassa daban daban ke taya kayan kuma su biya kudi ta banki mu tura musu. Kamar yadda na fada a baya, kashi 60 cikin 100 na abokan huldarmu ba mu taba haduwa ba. A cikin garin Kaduna muna aiki da kamfanin DTS, wanda ke kai mana sako daga kamfaninmu zuwa kofar gidan wanda ya saya. 

Ga masu nemanku a ina za su je ke nan?

Ko ina mutum yake, zai iya duba kafofin sadarwa da na ambata a baya duk bayanai game da kamfaninmu suna nan. Idan aka duba Ladaco Global Enterprises a facebook za a ganmu. Ko kuma www.Ladacoglobal.blogspot.com. Ko shafin Instagram. com/ladaco_fashion_design. Ko kuma Twitter. com/ladaconig.

Ina kuke samun kayayyakin da kuke amfani da su?

Muna samun wasu a gida Najeriya wasu kuma mukan saya daga kasashen waje kamar Dubai da Indiya da kuma China. Musamman abin da ya shafi kayan ado, muna saro su ne daga wadannan kasashen. Suna turo mana da kayan ne ba tare da mun je can ba. Sauran mukan saya a Kano da nan Kaduna da Abiya da Enugu da kuma Kwatano a Jamhuriyar Benin.

Mene ne burin da kuke so cimmawa?

Babban burinmu shi ne mu zamo kan gaba wajen fitar da dinkakku kaya daga Najeriya. Babban abin da ya sa muka samu karbuwa wajen jama’a shi ne saukin kayayyakinmu. Saboda sari muke bayarwa, shi ya sa ba mu cika kudi ba. 

Mene ne kiranka ga matasa musamman wadanda suka gama jami’a?

Kiranmu shi ne lokaci ya yi da za mu fara amfani da iliminmu wajen ciyar da kanmu da al’ummarmu da kuma kasarmu gaba. Yanzu haka a kamfaninmu muna da wadda ta karanta Biochemistry da wadda ta karanta Accounting, sai kuma ni da na karanta Industrial Chemistry. Sai muka hada iliminmu wajen assasa wannan kamfani. Kuma yanzu haka mutum kusan 35 ke aiki karkashinmu ka-tsaye, ga kuma daruruwan wadanda suke cin moriyar kamfanin a bangarori daban-daban, ga kuma wadanda muke ba kaya bashi har su samu jarinsu ya kafu. Da a ce sauran wadanda suka kammala karatunsu za su dauki wannan hanya, da adadin kayayyakin da Najeriya za ta bukata daga kasashen waje ya ragu. Sannan duk wanda ya gyara sana’arsa, zai samu ninki uku ko sama da haka na albashin da wani ke samu a aikin gwamnati.