Burinmu shi ne bunkasa karkara kafin shekarar 2050- Kungiyar NESG
Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Najeriya (NESG) ta ce a yanzu haka tana kokari tare da hada gwiwa da masu ruwa-da-tsaki wajen bullo da hanyoyin bunkasa yankunan karkara a duk fadin kasar kafin shekarar 2050. Shugaban Kungiyar NESG, Cif Laoye Jaiyeola, ne ya sanar da haka lokacin da ya jagoranci wadansu daga cikin shugabannin kungiyar suka […]
Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Najeriya (NESG) ta ce a yanzu haka tana kokari tare da hada gwiwa da masu ruwa-da-tsaki wajen bullo da hanyoyin bunkasa yankunan karkara a duk fadin kasar kafin shekarar 2050.
Shugaban Kungiyar NESG, Cif Laoye Jaiyeola, ne ya sanar da haka lokacin da ya jagoranci wadansu daga cikin shugabannin kungiyar suka kawo ziyarta hedkwatar Kamfanin Media Trust Limited mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya a Abujaa shekaranjiya Laraba.
“Wadansu daga cikin ayyukanmu sun hada da tabbatar da yankunan karkara sun samu isashshen ruwan sha da wutar lantarki da gina hanyoyi don inganta sufuri da hada gwiwa da Hukumar Kula da Kanana da Matsakaitan Masana’antu (MSME), wanda zai taimaka wajen habaka yankunan, sannan yanzu haka muna tattaunawa da shugabannin kananan hukumomi a kan muradun kungiyar,” inji Laoye.
Cif Laoye ya kara da cewa, kungiyar tana kokari wajen hada gwiwa da kungiyoyin ’yan kasuwa na jihohin kasar da kuma inganta shirin noma na gwamnati a duk yankunan karkara da ke kasar nan. “Mun hada gwiwa da hukumomin da ke kula da harkokin noma da kuma kungiyoyin ’yan kasuwa, don habaka noma.“ Sannan ya ce Kungiyar NESG tana kokarin kulla alaka da wasu kamfanoni kamar na gine-gine da tallafa wa jama’a da jari don dagaro da kai. “Idan har za mu iya kaddamar da wadannan abubuwan za mu iya cimma burinmu na shekarar 2050,” inji shi.
Shugaban ya kara da cewa kungiyar ta shirya taron shekara da za ta yi a ranakun 7 da 8 ga watan Oktoban bana mai taken ‘Kara Karfafa Ayyukan Kungiyar Kafin 2050’ wato Nigeria 2050: Sake Dabaru.” Kuma kungiyar tana da shirin da yake da alaka da taron tattalin arzikin kasa (NES) na shekara da ake yi, wanda hakan zai bunkasa tattalin arzikin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da kuma kawo sauyi a fannin ci gaban tattalin arzikin kasa na shekaru da dama.
Kungiyar NESG, kungiya ce mai zaman kanta da take da muradun bunkasa tattalin arzikin Najeriya tare da kamfanoni masu zaman kansu don kaiwa wani matakin ci gaba kamar na kasashen da tattalin arzikinsu ya bunkasa, ta hanyar amfani da abin da kasar ke da shi a yanzu.