Burna Boy ya fusata masoyansa a Legas
Idan ma ba ku so ni ba, to ba ku kaunar Allah.
Fitaccen mawakin Najeriya Damini Ogulu da aka fi sani da Burna Boy, ya shiga shekarar 2023 da kafar hagu, dalilin caccaka da yake sha sakamakon wasu kalamai da kuma harbin masoyinsa da kafa lokacin da yake wasa a Legas.
Bidiyon mawakin dai ya karade kafafen sada zumunta, bayan ya furta maganganu marasa dadi, da kuma harbin wani masoyinsa da ya halarci wasan da ya gudanar a Legas.
- ’Yan Najeriya sun koka da karancin sababbin takardun kudi a bankuna
- Dubai ta soke harajin barasa domin zawarcin masu yawon bude ido
Caccakar dai ta biyo bayan fara wasan karfe 3:30 na dare, madadin karfe 9:00 da aka tsara.
Baya ga haka, wadanda suka halarci wasan, sun bayyana yadda mawakin ya ki bayar da hakurin wannan bata lokaci da ya yi, sai ma ya biyo da kalamai marasa dadi.
Bacin ran kin bayar da hakurin ya sanya wasu suka fara yi masa ihun ba ma so, wanda ya harzuka mawakin take.
“Babu laifina a bata muku lokacin da a ka yi, wadanda suka shirya ne ba su tsara komai yadda ya kamata ba.
“Ku gode wa Allah ma na zo wasan gaba daya. Kuma ina sane da jita-jitar da wasunku suka dade suna yada wa a kaina.
“Har cewa aka taba yi na harbe wani har lahira a gidan rawa a Legas, wasu kuma suka dinga cewa mahaifyata ’yar rawa ce zamanin mawaki Fela. Amma wannan duk bai hana ni zuwa wasan yau ba.
“Idan ma ba ku so ni ba, to ba ku kaunar Allah, Allah wadaranku”, in ji Burna Boy.
Baya ga bidiyon wadannan kalamai nasa kuma, akwai na harbin wani masoyinsa da ya yi yunkurin taba shi a wurin bikin.
Sai dai daga baya masoyan nasa da ke filin wasan, sun sakko, bayan ya fara gudanar da wasan, inda bidiyon ya nuna masu fushin na murna suna bin wakokin da ya yi a wurin.
Kalli bidiyon: