Burundi: Ana gwabza fada a Bujumbura
Rikici ya varke a Bujumbura babban birnin kasar Burundi tsakanin sojojin da ke goyon bayan Shugaba Pierre Nkurunziza da wadanda ke adawa da shi, bayan wani yunkurin juyin mulki shekaranjiya Laraba. A jiya Alhamis ne wasu majiyoyin tsaro suka ce dakarun da ke biyayya ga Shugaba Nkurunziza na gwabza fada a harabar kafar Talabijin din […]
Rikici ya varke a Bujumbura babban birnin kasar Burundi tsakanin sojojin da ke goyon bayan Shugaba Pierre Nkurunziza da wadanda ke adawa da shi, bayan wani yunkurin juyin mulki shekaranjiya Laraba.
A jiya Alhamis ne wasu majiyoyin tsaro suka ce dakarun da ke biyayya ga Shugaba Nkurunziza na gwabza fada a harabar kafar Talabijin din kasar a Bujumbura tsakaninsu da sojojin da suka kaddamar juyin mulki.
Majiyoyin sun ce Sojojin Gwamnatin sun kaddamar da farmaki dauke manyan makamai a ginin Babbar kafar Talabijin na RTNB, kuma babban hafsan sojin gwamnatin kasar Rime Niyongabo da ke biyayya ga Nkurunziza ya karyata juyin mulkin ta kafar rediyo.
A shekaranjiya Laraba ne dai Tsohon Hafsan Sojin kasar Janar Godefroid Niyombare ya sanar da kwace mulki, yayin da Pierre Nkurunziza ke halartar taron sasanta rikicin Burundi a kasar Tanzaniya. Zuwa lokacin hada wannan rahoton babu tabbaci akan vangaren da ke da iko a kasar. Kodayake, Mista Nkurunziza yana Tanzaniya, bayan ya kasa komawa kasar.
Akalla masu zanga-zanga 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon arangamar da suka yi da jami’an tsaro a tsawon makonni biyu da aka shafe ana zanga-zanga. Har yanzu kuma ana ci gaba da zanga-zangar a birnin Bujumbura.