Burundi za ta ba tsofaffin shugabanni gidan alfarma da Naira miliyan 200 a matsayin fansho
Gidan alfarma da Dala dubu 500 (kimanin Naira miliyan 200) kasar Burundi za ta fara ba tsofaffin shugabannin kasar bayan barin mulki, kamar yadda wata sabuwar dokar da majalisar kasar ta sahale. Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaba Pierre Nkurunziza ya ce ba zai tsaya takara ba watanni kalilan kafin zaben da […]
Gidan alfarma da Dala dubu 500 (kimanin Naira miliyan 200) kasar Burundi za ta fara ba tsofaffin shugabannin kasar bayan barin mulki, kamar yadda wata sabuwar dokar da majalisar kasar ta sahale.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaba Pierre Nkurunziza ya ce ba zai tsaya takara ba watanni kalilan kafin zaben da za a yi a watan Mayu.
A shekarar 2015, yunkurinsa na neman wa’adi na uku ya jefa kasar cikin rikici, inda ya haifar da rudanin siyasar da har yanzu bai kare ba.
Sabuwar dokar ta tanadi cewa a karshen wa’adin mulkin shugabannin, kowane shugaba za a ‘gina masa gida na kasaita a wurin da yake so cikin shekara biyar – daga baitul malin kasar tare da kudin sallama na biliyan daya na kudin kasar (kimanin Dala dubu 530)’.
Wannan makudan kudi ne a kasar Burundi, inda fiye da kashi 65 na ’yan kasar ke rayuwa cikin fatara, yayin da kashi 50 kuma ke fama da karancin cimaka, kamar yadda alkaluman Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya, WFP, suka nuna.
Dokar da ta samu sahalewar kuri’a 98 yayin da biyu suka hau kujerar na ki, ta bambanta damar da tsofaffin shugabannin za su samu – tsakanin wadanda aka zaba – wanda a halin yanzu Nkurunzizan ne kawai zai ci moriyarta – da wadanda suka haye iko ta hanyar juyin mulki ko yarjejeniyar zaman lafiya.
Sai dai dokar ba ta yi wani karin haske game da girma da kudin da ginin gidan zai ci ba.
Shugaba Nkurunziza wanda yake mulki tun shekarar 2005, ya shammaci masu lura da al’amura lokacin da ya yi shelar cewa ba ya da niyyar tsayawa takarar wani sabon wa’adi a zaben da za a yi ranar 20 ga watan Mayu – duk da damar hakan da sabon kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi.