Buzu da bako
Wani Buzu ne ya sawo garin rogo, ya hada kwadon garin tsaf. Ya sa cokali zai ci, sai ga wani abokinsa, suka gaisa ya yi masa tayin garin. Abokin ya ce ‘madallah.’ Buzu ya kawo masa cokali, ya ce a’a, shi hannu zai sanya. Mutumin sai ya tattara gari mai yawa ya dunkule ya kai […]
Wani Buzu ne ya sawo garin rogo, ya hada kwadon garin tsaf. Ya sa cokali zai ci, sai ga wani abokinsa, suka gaisa ya yi masa tayin garin. Abokin ya ce ‘madallah.’ Buzu ya kawo masa cokali, ya ce a’a, shi hannu zai sanya. Mutumin sai ya tattara gari mai yawa ya dunkule ya kai baki. Kan haka garin ya kare Buzu bai ci abin kirki ba. Mutumin ya yi gyatsa ya ce: “Na gode aboki, zan tafi.” Buzu ya ce, a fusace: “Kai namiji dakata, zan ba ka shawara don nan gaba. Idan za ka ci gari, kada ka sa hannu, domin gari ba ya son dunkula.”
Daga Shehu Lawali Tsafe, 08091573703