Cacar dubu 20 ta yi sanadin mutuwar matashi a cikin tekun Legas

Toheeb Jimoh dan kimanin shekaru 25 a duniya bai san cewa zai bar duniya ba a karshen makon da ya gabata har sai da musu ya kaure  a tsakaninsa da abokansa yayin da suka kalubalence shi ba zai iya yin iyo a cikin tekun Legas ba.Binciken Aminiya ya gano cewa Jimoh ya nemi abokansa biyu […]

Cacar dubu 20 ta yi sanadin mutuwar matashi a cikin tekun Legas
Cacar dubu 20 ta yi sanadin mutuwar matashi a cikin tekun Legas

Toheeb Jimoh dan kimanin shekaru 25 a duniya bai san cewa zai bar duniya ba a karshen makon da ya gabata har sai da musu ya kaure  a tsakaninsa da abokansa yayin da suka kalubalence shi ba zai iya yin iyo a cikin tekun Legas ba.
Binciken Aminiya ya gano cewa Jimoh ya nemi abokansa biyu su ajiye dubu goma-goma dubu 20 kenan in har suna ganin ba zai iya yin iyo a wuri mai zurfi na tekun ba inda daga bisani suka amince da yin cacar.
kaninsa Tiamiyu Jimoh wanda bai yarda a dauki  hotonsa ko maganarsa a na’ura ba ya bayyana abinda ya auku ga Jimoh a matsayin tsautsayi.
  ‘Na dauki abinda ya sami Toheeb a matsayin tsautsayi ne domin ya sha yin musu da abokanensa ya na yin nasara. Yakan shiga wurin da ya fi kowanne zurfi ya fito lafiya. A ranar da abin ya faru bayan sun yi musu sai ya nemi su sanya naira dubu ishirin. Da suka amince sai  ya shiga karamin kwale-kwale zuwa wurin, nan take ya cire rigarsa ya fada ba tare da wata fargaba ba. Tun da ya fada ba mu sake jin duriyarsa ba. Mun yi tsammanin nutso ya yi, amma har wasu mintuna ba mu ga motsin sa ba. Da lokaci ya kara ja sai muka yanke shawarar neman taimako don a tsamo shi, amma ba a ga gawarsa ba sai bayan sa’o’i aka gano gawar a wuri mai nisan gaske. Ina zaton ajali ne ya ja shi, domin gawarsa babu rauni balantana a yi tunanin wani abu ne ya yi masa rauni’. In ji shi.
Ya ci gaba da cewa ‘Da muka kai shi asibiti sai likitoci suka tabbatar mana cewa ya mutu. Sai muka dawo da shi muka yi masa jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada. Har yanzu muna jimamin mutuwarsa’.
Toheeb wanda dalibi ne a jami’ar Jihar Abeokuta ba shi da aure, kuma yana zaune ne tare da dangin mahaifinsa a unguwar Bariga da ke jihar Legas .
Makwabtansu sun bayyan shi a matsayin mutumin kirki  wanda ba ya hayaniya kuma mai bin addinin musulunci sau da kafa.
Jami’in da ke kula da ofishin ’yan sanda na unguwar Bariga wanda ya ki bayyana sunansa ya bukaci wakilinmu ya tuntunbi ofishin mai magana da yawun ’yan sandan jihar Legas domin ba shi da hurumin yin magana da manema labarai.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin mai magana da yawun ’ yan sandan jihar Legas ya ci tura domin wayarta ba ta shiga amma wata majiya  a ofishinta sun bayyana cewa tana halartar wani babban taro a ofishin kwamishinana ’yan sandan jihar.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan