CAF ta sanya ranar da za a fara gasar AFCON ta 2025
CAF ya sanyar ranar da za a fara gasar ta AFCON ta 2025.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF), ta bayyana cewar za a gudanar da Gasar Nahiyar Afirka (AFCON) a watan Disamban 2025 zuwa Janairun 2026.
Caf ta bayyana ƙasar Maroko a matsayin wadda za ta ɗauki nauyin gasar ta 2025 da za fara ranar 21 ga watan Disamban 2025 zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2026.
- Ya kashe Naira miliyan 200 don zanen tattoo a jikinsa
- Jirgin Flynas zai kwaso rukunin farko na Alhazan Nijeriya
Gasar wadda ƙasashe 24 za su fafata za ta ci karo da lokacin da ake tsaka da murza leda a gasannin a Nahiyar Turai.
Wannan ne karo na farko da za a buga gasar AFCON a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Haka kuma, CAF ta sanar da ɗage gasar ƙwallon ƙafar mata ta 2024 zuwa watan Yulin shekara mai zuwa.
Idan ba a manta ba an gudanar da gasar AFCON ta 2024 a ƙasar Ivory Coast, inda ta kai wasan ƙarshe, wanda ta samu nasarar doke Najeriya da ci 2-1.