Cafke sojan da ya harbe matashi a Zariya abun a yaba ne — Atiku

Na sha ba wa jami’an tsaro shawara kan su daina ba da umarni far wa masu zanga-zanga.

Cafke sojan da ya harbe matashi a Zariya abun a yaba ne — Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa; Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya yabi rundunar sojin kasar da ta bayyana kama sojan da ake zargi da harbe wani matashi mai shekaru 16 a Zaria da ke Jihar Kaduna.

Atiku wanda ya yi wannan yabo cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, ya kuma bayyana alhininsa kan yadda matashin ya rasa ransa.

Wazirin Adamawa ya ce akwai bukatar a gudanar da bincike kan sauran zargin abubuwan da a jami’an tsaron suka yi a sassan kasar a lokacin zanga-zangar.

“Ina kuma kira da a gudanar da cikakken bincike a kan sauran ayyukan da sojoji, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka yi a lokacin zanga-zangar.”

“Matakin tsare wannan soja kan wannan abin takaici abin a yaba ne kuma zai bude babin tabbatar da adalci da bin doka.” Atiku ya kara da cewa.

Atiku ya kara da cewa “na sha ba shugabannin soji da kwamandoji shawara kan su daina ba da umarni kai hari kan masu zanga-zanga.”

Bayanai sun ce a ranar 6 ga watan Agusta, wani soja ya harbe wani matashi mai suna Ismail Muhammad a yankin Samaru da ke Zaria a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa.

Rundunar sojin kasar ta ce sojan ya je yin harbin gargadi ne a lokacin da harsashin ya samu matashin.

Wasu rahotanni da dama sun ruwaito cewa mutanen da abin ya faru a gabansu sun musanta hakan.

A ranar Talata, rundunar sojin ta ce an kama sojan ana kuma gudanar da bincike kan lamarin.