Cajin Naira 65 na cire kudi a na’urar ATM ya haifar da cece-kuce

A ranar Litinin tsarin da Babban Bankin Najeriya ya kawo na cire wa mutum Naira 65 idan ya cire kudi a na’urar ATM din da ba ta bankinsa ba ya fara aiki.Sabon tsarin ya ce idan mutum ya cire kudi sau uku da katin ATM dinsa a na’urar ATM din da ba ta bankinsa ba […]

Cajin Naira 65 na cire kudi a na’urar ATM ya haifar da cece-kuce

A ranar Litinin tsarin da Babban Bankin Najeriya ya kawo na cire wa mutum Naira 65 idan ya cire kudi a na’urar ATM din da ba ta bankinsa ba ya fara aiki.
Sabon tsarin ya ce idan mutum ya cire kudi sau uku da katin ATM dinsa a na’urar ATM din da ba ta bankinsa ba sau uku, to za a cire masa Naira 65. Daga nan duk kudin da zai cire za a ci gaba da cire masa Naira 65.
A yanzu wannan sabon tsarin ya haifar da cece-kuce, inda jama’a suke tofa albarkacin bakinsu, wadansu sun ce hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa, yayin da wadansu suka ce tsarin ba zai haifar wa masu ajiya a bankuna da mai ido ba.
Babban Bankin Najeriya ya ce, a shekarar 2012 akwai na’aurar ATM 10,727 a kasar nan, amma a watan Yuni 2014 yawan ATM ya kai dubu 15, inda kudin da bankin yake kashewa a kan ayyukan da suka shafi ATM ya tashi daga Naira tiriliyan 1.3 a shekarar 2012 zuwa Naira tiriliyan 1.7 a karshen Yuni, 2014. Wannan kuwa ba karamin kudi ba ne.
Barista Shehu Usman ya ce batun an dawo da wannan caji don kada bankuna su durkushe ba gaskiya ba ne, ko a bara bankuna sun ce sun samu ribar Naira biliyan 500 duk da cajin Naira 100 da aka cire idan an cire kudi na’aurar ATM.
Hashim Ibrahim ya ce “a kwanakin baya bankin CBN ya ce idan katin ATM dinka ya makale kafin a ba ka sai an huhhuda shi, wanda hakan yake nufin sai dai ka sake karbar wani a kan Naira dubu, yanzu ga batun cire Naira 65, kashe mu ake so a yi?”
Daraktan Babban Bankin Najeriya, Mista Dipo Fatokun ya ce bankin CBN na matukar kashe kudi wajen biyan ayyukan na’urorin ATM a kasar nan, wanda hakan ya zama kamar kura da shan bugu gardi da kwashe kudi ne.