Cajin waya
Wata rana wani Bakatsine ya je bakunta Hadeja, yana shiga garin, kawai sai ya ga mutane sai gudu suke yi. To abinka da bako, bai san me yake faruwa ba, kawai shi ma sai ya shiga sahun masu gudu. Ana cikin gudu to sai ya ga kowa da ya zo kofar gidansa sai ya ga […]
Wata rana wani Bakatsine ya je bakunta Hadeja, yana shiga garin, kawai sai ya ga mutane sai gudu suke yi. To abinka da bako, bai san me yake faruwa ba, kawai shi ma sai ya shiga sahun masu gudu. Ana cikin gudu to sai ya ga kowa da ya zo kofar gidansa sai ya ga kawai ya shiga, kuma ba tare da ya rufe kofa ba. Ya duba ya ga yadda kowa ya fita daga hayyacinsa, ana ta gudu. Kawai sai ya yanke shawarar, ya rike daya ya tambaye shi. Yana juyawa sai ya rike na gefensa, ya ce masa: “Wai gudun me ake yi ne? Sai mutumin nan ya ce: “Ai wutar NEPA aka kawo, shi ne kowa yake gudu ya je ya saka cajin waya.”
Daga Kabir Sakaina Malumfashi