Cakir ne zai hura wasan Jubentus da FC Barcelona
A ranar Talatar da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa a Nahiyar Turai (UEFA) ta bayyana alkalin wasa Cuneyt Cakir, dan asalin Turkiyya a matsayin wanda zai hura wasan karshe a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) a tsakanin kulob din Jubentus na Italiya da kuma na FC Barcelona da ke […]
A ranar Talatar da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa a Nahiyar Turai (UEFA) ta bayyana alkalin wasa Cuneyt Cakir, dan asalin Turkiyya a matsayin wanda zai hura wasan karshe a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) a tsakanin kulob din Jubentus na Italiya da kuma na FC Barcelona da ke Sifen a ranar Asabar 6 ga watan gobe.
Shi dai alkalin wasa Cakir, dan kimanin shekara 38 tun a shekarar 2006 yake yin alkalanci a wasanni daban-daban da hukumar ke shiryawa.
Shi ne alkalin wasan da ya hura wasan kwata-fainal a shekarar 2013 a tsakanin kulob din Real Madrid da na Manchester United, bayan ya ba dan kwallon United Nani katin kora da hakan ta sa Madrid ta samu galaba a kan na United a wasan.