Camfi ya sa an hana mata masu jinin al’ada shan ruwa da sauran jama’a a Akwa Ibom

Camfi ya sanya al’ummar yankin hana wasu rukunin mata amfani da ruwa a yankin.

Camfi ya sa an hana mata masu jinin al’ada shan ruwa da sauran jama’a a Akwa Ibom

An hana mata masu al’ada da wadanda suka haifi ’yan biyu shan ruwa da sauran jama’a a wasu yankunan Jihar Akwa Ibom, saboda camfi.

Ko’odinetan Shirin Kula da Tsaftar Ruwa da Muhalli (WASH), na Jami’ar Uyo, Farfesa Emmanuel Akpabio ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Uyo yayin rahoton binciken da suka gudanar a Kananan Hukumomi uku na Jihar.

Farfesan ya ce an yi ta camfi tare da kalubalantar al’ummar da lamarin ya shafa saboda karancin ruwan sha da kuma fargabar cewa idan suka ci gaba da amfani da ruwan zai iya kafewa.

Ya yi nuni da cewa rashin samun damar amfani da tsaftataccen ruwa na hana mata da ‘yan mata da sauran masu karamin karfi shiga harkokin tattalin arziki da ilimi.

Ya yi kira da a sa baki wajen samar da ruwan sha ga al’ummar yankin, inda ya kuma ce hakan zai kuma magance matsalar yin bayan gida a fili.

“A Mbiabet Ikot Udo, akwai idon ruwa guda daya (Idim Affia) wanda ke gudana wanda yake gauraye da kasa.

“An hana mata masu al’ada da iyaye masu ‘ya’ya tagwaye samun ruwa, an shaida mana idan suka ci gaba da amfani da ruwan na iya kafewa.

“Mata masu al’ada ma ana hana su shiga rafi saboda gudun kada jini ya zuba a ciki, wadanda abin ya shafa su kan samu ruwa ne kadai ta hanyar tura mazajensu, ‘ya’yansu, ko kuma ta hanyar biyan kudi don a debo musu. Idan ba haka ba su kan zauna ba tare da ruwa ba na tsawon lokaci,” in ji shi.

Akpabio ya bayyana cewa, wannan al’adar tana kara rura wutar nuna wariya ga jinsi wajen samun damar yin amfani da ruwa da kuma sanya mata shiga cikin rudani da sauran nau’o’in cin zarafin mata, wanda hakan zai shafi lafiyarsu.

“Lokacin da aka hana mata da ‘yan mata ruwa saboda jinin al’ada, lokacin da za su yi tafiya mai nisa don samun ruwan da za su tsaftace jikinsu.”

Ya nuna damuwarsa kan lamarin tare da kira ga masu ruwa da tsaki da tashi tsaye don shawo kan matsalar da ke neman jefa rayuwar mutane da dama cikin tsaka mai wuya.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno