CAN ta bukaci Gwamnati da a saki Zakzaky, Dasuki

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bukaci Gwamnatin tarayyar Najeriya da ta gaggauta sakin jagoran kungiyar Harkar Musulunci (IMN) ta mabiya Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky da tsohon mai ba shugaban kasa shawara a harkar tsaro Sambo Dasuki da aka tsare su. Shugaban CAN Rabaran Samson Olasupo Ayokunle, ne ya yi kiran a garin Ogbomosho, jihar […]

CAN ta bukaci Gwamnati da a saki Zakzaky, Dasuki

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bukaci Gwamnatin tarayyar Najeriya da ta gaggauta sakin jagoran kungiyar Harkar Musulunci (IMN) ta mabiya Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky da tsohon mai ba shugaban kasa shawara a harkar tsaro Sambo Dasuki da aka tsare su.

Shugaban CAN Rabaran Samson Olasupo Ayokunle, ne ya yi kiran a garin Ogbomosho, jihar Oyo a karshen mako wajen taron manema labarai da aka yi.

Rabaran Samson ya bukaci Shugaba Buhari, ya gaggauta magance yin garkuwa da mutane da hare-haren ‘yan bindiga da sauran kalubalen tsaro da ya addabi kasar.