CAN ta wanke Etsu Nupe kan batun musuluntar A’isha Uzoechina

Babban Sakataren kungiyar Kiristoci ta kasa Najeriya, Rabaran Musa Asake ya wanke Mai martaba Estu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar kan zarginsa da hannu wajen musuluntar da A’isha Uzoechina ’yar Fasto Raymond Uzoechina, inda ya ce ba a fadi gaskiya kan matsayin Sarkin a kan al’amarin ba. Fasto Uzoechina ya rika zargin Etsu Nupe da garkuwa da […]

CAN ta wanke Etsu Nupe kan batun musuluntar A’isha Uzoechina

Mai martaba Etsu Nupe Alhaji Yahaya AbubakarBabban Sakataren kungiyar Kiristoci ta kasa Najeriya, Rabaran Musa Asake ya wanke Mai martaba Estu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar kan zarginsa da hannu wajen musuluntar da A’isha Uzoechina ’yar Fasto Raymond Uzoechina, inda ya ce ba a fadi gaskiya kan matsayin Sarkin a kan al’amarin ba.
 Fasto Uzoechina ya rika zargin Etsu Nupe da garkuwa da ’yarsa tare da sanya tat a musulunta ba tare da son tab a.
Rabaran Asake ya wanke sarkin ne bayan ganawar sirri da gwamnatin Jihar Neja ta shirya domin warware matsalar cikin lumana.
Ya ce, “Mun warware matsalar, yanzu an samu kyakkyawar fahimta, musamman game da abin da ya shafi mutum mai martaba kamar Etsu Nupe wanda jaridu suka rika bayanan karya a kansa.”
Mataimakin Gwamnan Jihar Neja Ahmed Musa Ibeto wanda ya shugabanci ganawar ya shaida wa manema labarai cewa, bangarorin biyu sun amince cewa za a janye umarnin da Kotun Shari’a ta Bidda ta bayar na ba da rikon A’isha saboda tsoron mahaifinta zai iya cutar da ita.
Ya ce batun mayar da budurwar ga iyalanta ne ya ja hankali a wurin ganawar ba batun musluntar ta ba, tare da ba ta tabbacin cewa mahaifin nata ba zai cutar da ita ba.
Y ace, A’isha wadda a baya ake kira Charity mai shekara 25 tana da ’yancin yin addinin da ta zaba, ya ce sai an janye umarnin kotun ne za a iya daukar mataki na gaba, “Sai an janye umarnin kotun ne za ta iya yanke shawara a kashin kanta,” inji shi.