Cancanta muka duba wajen zaɓo ministoci — Tinubu
’Yan Najeriya na sa ran za ku yi aiki mai inganci.
Shugaban Bola Ahmed Tinubu ya ce cancanta ce ta yi tasiri wajen zaɓo ministocinsa da aka rantsar a yau domin su taimaka wajen tafiyar da lamurran ƙasar.
Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da ya yi jawabi bayan rantsar da sabbin ministoci a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
- ’Yan ta’adda sama da 100 sun mutu a gumurzu tsakanin Boko Haram da ISWAP
- Tinubu ya rantsar da sabbin Ministocinsa
“Ƴan Najeriya na sa ran za ku yi aiki mai inganci kuma za ku sauke nauyin da aka ɗora muku,” in ji Tinubu.
Ya ƙara da cewa “Dole ne ku yi aikin da zai sanya ƴan Najeriya su sake amincewa da gwamnati.”
Ya bayyana cewa akwai babban nauyi a kan sabbin ministoci ganin irin manyan alƙawurran da gwamnatinsa ta ɗauka.
Shugaban ya kuma buƙaci sabbin ministocin da su yi aiki ba tare da nuna banbanci ba, inda ya ce: ”An ba ku wannan matsayi ne ba domin ɓangaren da kuka fito ku jihonhinku ba, sai dai domin ƙasa baki ɗaya.”